Ilimin ’yan Najeriya na neman abinci ne kawai – Farfesa dahiru Yahaya

Fitaccen masanin tarihi, Farfesa dahiru Yahaya, ya soki lamirin karatun boko da ’yan Najeriya suke yi a yanzu, wanda da zarar sun kammala burinsu shi ne su samu aikin yi kawai.Farfesa wanda malami ne a Tsangayar Tarihi ta Jami’ar Bayero Kano, ya yi furcin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya.Ya ce, mutane a yanzu […]

Ilimin ’yan Najeriya na neman abinci ne kawai – Farfesa dahiru Yahaya
Ilimin ’yan Najeriya na neman abinci ne kawai – Farfesa dahiru Yahaya

Fitaccen masanin tarihi, Farfesa dahiru Yahaya, ya soki lamirin karatun boko da ’yan Najeriya suke yi a yanzu, wanda da zarar sun kammala burinsu shi ne su samu aikin yi kawai.
Farfesa wanda malami ne a Tsangayar Tarihi ta Jami’ar Bayero Kano, ya yi furcin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya.
Ya ce, mutane a yanzu sun daina tunanin su nemi ilimi don su bunkasa kansu su zama mutane sosai.
“Karatun da mutane suke yi a yanzu ya zama na neman abinci, ina zai samu harawa ya ci shi ke nan. Wato shi yana ganin an ba shi ilimi ne kawai ya je ya yi aiki a kamfani ko kuma aikin gwamnati. Ya zama bawan kamfani ko bawan Gwamnati. Ba zai taba tunanin cewa wadanda suka gina kasar nan suka koya masa sanya riga, ba haka suka yi ba.” Inji shi.
Ya dage a kan cewa irin wannan tunani na rashin daraja kai ne kuma tunani ne na ‘dabbobi’ wadanda ba su tunanin komai sai dai su ci abinci.
Ya zargi ’yan Nijeriya da zama ‘dabbobi’ saboda yadda wadansu suke tara dukiya ta hanyar cin hanci da rashawa.
“Yanzu ’yan Najeriya da yawa ai dabobi ne mu. Mutum ya je ya samu aiki ya saci kudin da bai san amfaninsu ba. Me ye amfanin wannan? Ka ga ka cuci jama’a.” Inji shi.
Ya dage a kan cewa ilimi na sanin kai ba na neman abinci ba shi ne ilimin hakika mai tattare da gaskiya da rikon amana.
Daga nan sai ya dora alhakin daina koyar da ilimin tarihi a kan wadanda suke da ruwa da tsaki a harkar ilimi da a cewarsa ba su san abin da suke yi ba. Saboda a ganinsa manya-manyan kasashen duniya da suka ci gaba, sun sanya doka a kasashensu cewa lallai a koyar da ilimin tarihi.
Ya ce: “Duk kasa mai alfahari da kanta kamar su Faransa da Ingila da Jamus da sauransu, duk sun sanya doka a rika koyar da tarihi saboda ’ya’yansu su san tarihinsu. Amma mu a nan Najeriya ba haka lamarin yake ba. Wannan kuma babban bala’i ne.”
Saboda haka sai ya bayar da shawara cewa dole sai an koma an gyara inda aka yi kuskure, an dawo da koyar da tarihi sannan darajar ilimi za ta dawo.