Ilimin zamantakewa zai magance yawan mace-macen aure —Sheikh Daurawa
Mutum 4.6m sun bibiyi sabuwar manhajar neman aure da harshe Hausa..
An yi kira ga gwamnati ta sanya darasin ilimin aure a cikin manhajar karatun sakandare da nufin rage yawan mace-macen aure a cikin al’umma.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya yi wannan kira a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Kano.
- Auren ‘Wuf’ ba shi da wata illa a Musulunci —Sheik Daurawaj
- Namijin da mata suka fi so tsakanin miskili da mai surutu
“Idan matasa suka san hakkokin ma’aurata zai taimaka musu wajen hana su shiga harkar aure da ka.
“Idan maganar sakin ma ta taso za su san yadda za su bullo mata bisa ka’ida.
“Idan kin dubi kasashen Larabawa za ki ga suna da irin wadannan cibiyoyi don ma’aurata su san hakkokinsu.”
Sheikh Daurawa ya ce wannan ya sa ya kirkiro sabuwar manhaja domin inganta rayuwar ma’aurata.
“Ita wannan manhajar idan mutum ya shiga zai samu abubuwa uku a ciki.
“Ma’ana ajin farko ga masu neman aure na biyu kuma ga masu neman shawarwarin akan aure. Sai na uku ga masu matsalolin aure.”
A cewarsa zuwa yanzu manhajar na samun tagomashi daga wajen jama’a, domin a kasa da wata biyu da sakin manhajar wadanda suka bibiye sun kai miliyan 4.9 yayin da yawan wadanda suka sauke ta a wayoyinsu ko kwamfutucinsu sun kai mutum dubu goma.
Sheikh Daurawa ya kuma bayyana cewa ita wanna manhaja ita ce irinta ta farko da aka yi ta da Hausa a duniya kuma ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnati ta sanya hannu kan dokokin aure.
“Idan har gwamnati ba ta yi da gaske ta samar mana da namu dokokin na Musulunci ba to za mu zo wata rana mu yi amfani da na Turawa,” inji shi.