Illar auren dole

Assalamu Aalaikum warahmatullahi wabarakatuhu.  A  yau zan kawo wani tsokaci da wata baiwar Allah ta aiko a kan halin da take ciki sakamakon auren dole da aka yi mata kamar haka:   Ta fara da tambayata a kan hukuncin macen da ta nemi saki wajen mijinta, sai na ba ta amsa a cikin hikima cewa: […]

Illar auren dole

Assalamu Aalaikum warahmatullahi wabarakatuhu.  A  yau zan kawo wani tsokaci da wata baiwar Allah ta aiko a kan halin da take ciki sakamakon auren dole da aka yi mata kamar haka:

 

Ta fara da tambayata a kan hukuncin macen da ta nemi saki wajen mijinta, sai na ba ta amsa a cikin hikima cewa: “In har babu dalili da shari’a ta kalla a matsayin tauye mata hakki daga cikin manyan hakkokinta ko kuma zuwa da wata alfasha amma in ba wannan tabbas laifi ne babba.” Daga nan sai ta fada mini cewa an yi mata auren dole ne amma ita a gaskiya tana jin tsoro ba ta iya yi masa biyayya kada Allah Ya kamata a kan haka, ga shi sun yi  shekaru kuma har da ’ya’ya.

Wannan ya tuna min da labarin wadansu ma’aurata. Matar ba ta son mijin sun kwashe shekaru da dama sun hayayyafa har da jikoki, ran nan suna cikin lambu suna shakatawa sai mijin ya tuno mata cewa: “Wance da fa ba ki sona muka yi aure.” Sai matar ta ce masa ai har yanzu ba na sonka, ina dai zama ne da kai bisa kaddara.  Nan take hankalin mijin ya tashi, ya gane illar yin auren dole, ganin duk shekarun da suka kwashe da mata har sun samu jikoki amma ba ta kaunarsa.  Hakan ya sa ya yi nadama kuma ya yi alkawarin ba zai aurar da ’yarsa wa wani a bisa auren dole ba.

Mu kwana nan

Za a iya samun Sanusi Hashim a 08065507271