Illar auren dole (2)

Assalamu Aalaikum warahmatullahi wabarakatuhu.  A  yau zan kawo wani tsokaci da wata baiwar Allah ta aiko a kan halin da take ciki sakamakon auren dole da aka yi mata kamar haka: Daga Sanusi Hashim A nan ina kira ga iyaye su yi nazari a game da illar yin auren dole da abubuwan da yake janyowa.  […]

Illar auren dole (2)

Assalamu Aalaikum warahmatullahi wabarakatuhu.  A  yau zan kawo wani tsokaci da wata baiwar Allah ta aiko a kan halin da take ciki sakamakon auren dole da aka yi mata kamar haka:

Daga Sanusi Hashim

A nan ina kira ga iyaye su yi nazari a game da illar yin auren dole da abubuwan da yake janyowa.  Wasu ta dalilin haka a kan samu kisan kai, ko tafiya yin karuwanci da sauran abubuwa marasa kyau.

Shi aure an gina shi ne domin;

– So da kauna,

– Raya sunnar Manzo (Saw),

– Haihuwa

Da sauran su.

Duk da Allah Madaukakin Sarki Ya ambaci namiji a matsayin shugaba amma akwai inda aka ambaci mace a matsayin abokiya. Kenan ya za ka yi abota da wanda ba ka so?

Annabi (Saw) yana cewa “ku auri wadda kuke so kuma mai haihuwa domin ya yi alfahari da yawan ku a ranar tashin kiyama.”

Auren dole in muka duba yana cin karo da hikimomin da ke cikin aure kamar haka;

– Samun natsuwa: Ba yadda za a yi mutum ya samu natsuwa da macen  da ba ta son sa.

– Soyayya: da ma a auren dole babu batun soyayya, kenan masu aiwatar da shi suna cin karo da ayar da ke cewa “an sanya soyayya a tsakanin ma’aurata.”

– Tausayi: wanda ba ya son ka ta ina tausayi zai shigo a tsakani?.

Kira ga masu ruwa da tsaki:

-Iyaye

-Ma’aurata

-Malamai

-Al’umma

-Hukuma

Da sauran su.

Mu sani aure ibada ce kuma sunnah ce ta kowane Annabi da Allah Ya aiko bisa doron kasa.

Iyaye: su ji tsoron Allah su tuna ’ya’yansu kiwo ne aka ba su kuma za a tambayesu a kan kiwon da aka ba su. Saboda haka su bar kallon dalilin da suke da shi na aurar da’ya’yansu a kan dole, su kalli

dalilin da aka ce a yi aure, su aurar da ’ya’yansu ga wanda suke so.

Ma’aurata: Namiji ya duba damar da aka ba shi ta neman aure da wadda ma yakamata ya aura amma ginshikin auren shi ne so.

Malamai: Su ci gaba da fadakarwa a masallatai da majalisai da makarantu,

Kuma akwai litattafan aure  da babin da suka yi magana a kan yadda ake zabar wadda za a  aura. Yakamata malamai su kara yin kaimi a kan wannan dabi’a domin a kullum tana kara zama ruwan dare.

Hukuma: Uwa ce ga al’umma kuma yakamata a ce shugabanni musamman sarakuna da hukuma har da ’yan majalisu su sanya baki kuma su kawo mafita a kan wannan danyen aiki da ke yaduwa.

A karshe ba a bin da ke cikin auren dole sai musgunawa da tsangwama da rashin zaman lafiya,

Don haka yakamata mu hankalta mu kauce wa kwadayi domin yana daga cikin dalilin da ke kawo

auren dole.

Zan dakata a nan sai kuma mun hadu a wani darasin in Allah Ya yarda.

 Sanusi Hashim Abban Sultana daga Jihar Katsina  08065507271

    Sanusihashim3@gmail .com