Illar bin abokan banza
Assalamu alaikum Manyan gobe yaya sabuwar shekara? Tare da fatan za a dage da mayar da hankali a karatu. A yau na kawo muku labarin “illar bin abokan banza”. A sha karatu lafiya. Bala yaro ne mara jin magana. Gashi kuama yana da matukar ilimi sosai wanda a ajinsu ko bai yi rubutu ba […]
Assalamu alaikum Manyan gobe yaya sabuwar shekara? Tare da fatan za a dage da mayar da hankali a karatu. A yau na kawo muku labarin “illar bin abokan banza”. A sha karatu lafiya.
Bala yaro ne mara jin magana. Gashi kuama yana da matukar ilimi sosai wanda a ajinsu ko bai yi rubutu ba idan an ba su gwaji yana samun nasara sosai. Yana da yayye da kanne amma an fifita shi akan sauran ’yan uwansa domin iliminsa.
Duk da yake ba shi ne babba ba, hakan ta sa yake ganin duk abin da ya yi daidai ne, koda kuwa abin ba shi da kyau.
Ran nan ya fada hannu mara kyau. Ya gamu da wasu ’yan ajinsu wadanda ba su da wani aikin yi da ya wuce shaye-shaye. Gadararsa ita ce tun da yana da kokari, ko ya yi karatu ko bai yi ba, zai ci jarrabawa, don haka ya yanke shawarar shiga harkar shaye-shaye da duk wadansu dabi’u marasa kyau.
Yau da gobe abin ya fara canza masa tunani da kalamansa da dabi’unsa da kuma mu’amalarsa da mutane. Hakan ya sa iyayensa suka gane amma a kurarran lokaci. Suka shiga nema masa magani amma abin sai gaba yake. Sai ya rika yin wayo da zarar ya fahimci za a kai shi asibiti sai ya yi sauri ya yi wa kansa wata allurar da za ta sa ya boye halin mayen da yake ciki.
Rannan sai wani yayansa yyi masa nasiha, kuma da taimakon Allah ya daina yin shaye-shayen, ya zama yaron kwarai. Amma duk da haka da yawa daga cikin iyayensa da kuma dangi ba su yarda ya daina halayyar shaye-shaye ba, suka rika yin kaffa-kaffa da shi. Hakan ta sa ransa ya baci inda ya yanke shawarar komawa gidan jiya.
Tare da fatan Manyan gobe za su san irin abokan da za su rika yin mu’amala da su.