Illar koyi da kafirai (1)

Daga Sheikh Su’ud bin Ibrahim AsshuraimMasallacin Harami, Makka Hamdala da salati: Bayan haka, ina yi muku wasiyya da ni kaina da tsoron Allah a cikin wadata da sanani a fili da boye: “Ya ku mutane! Ku bauta wa Ubangijinku, Wanda Ya halicce ku, ku da wadanda suke daga gabaninku, tsammaninku, ku kare kanku.” (k:2:21).Ya ku […]

Illar koyi da kafirai (1)

Sheikh Abu Ibrahim Sa’ud Ibn Ibrahim Ibn Muhammad ash-ShuraimDaga Sheikh Su’ud bin Ibrahim Asshuraim
Masallacin Harami, Makka

Hamdala da salati:

Bayan haka, ina yi muku wasiyya da ni kaina da tsoron Allah a cikin wadata da sanani a fili da boye: “Ya ku mutane! Ku bauta wa Ubangijinku, Wanda Ya halicce ku, ku da wadanda suke daga gabaninku, tsammaninku, ku kare kanku.” (k:2:21).
Ya ku mutane! Idan mutum ya leka tarihin kasashe da mutanen da suka gabata, zai ga abubuwan mamaki game da juyin juya-hali da sauye-sauye da suka hadu da su. Misali akwai watab fitacciyar kasa (kasar Musulmi) wadda a jagoranci duniya na karnoni da dama, amma sai ta fadi ta rasa wannan jagoranci nata; ta fadi ne saboda mummunan koyi da bin hanyoyin wasu kasashe ta wajen dabi’u da akida da imani. Lokacin da ta kai kololuwa wajen bunkasa da karfi, sai ta yiwo kasa tana makaskanciya. Ta mutu bayan ta kasance rayayyiya, ta lalace bayan ta kasance abar sha’awa, ta ruguje bayan ta bunkasa. Ita ce kasar da ta gano tushen ilimi da bunkasa wayewar Musulunci da kimiyyarsa, wadanda daga baya kasashen Turai suka samu a bagas ba tare da wahala ba, suka dora a kai. Sai ga shi kamar an kulle kofofin ci gaba ga Musulmi, inda suka koma jujin jibge kayayyakin ci gaba na Turai. Har ma sun koma suna kwakwayar wasu abubuwa, wadanda nasu ne tun asali da aka sace daga gare su.
Ya ku Musulmi! Lokacin da wani Musulmi ya rika makauniyar biyayya ga Yammacin Turai, ya zama kamar rakumi da akala wajen biyayya ga akidu da al’adunsu; zai zamo kamar wanda yake kokarin gyara wani abu ne amma ya bata shi ba tare da ya sani ba. Shi kamar yankwanannen fure ne, kamar jaririn da yake cizon nonon mahaifiyarsa ne a lokacin da aka sanya masa a baki. Wannan mutum ba zai san makauniyar biyayya ga Turawan Yamma ya hada da boyayyun abubuwan da za su jawo abin da zai ruguza mutunci da martaba da ’yancinmu ba, ta wajen irin wannan koyi.
Ya ku Musulmi! Manzon Allah (SAW) ya ce: “Da sannu za ku rika bin hanyoyin al’ummomin da suka gabace ku, taku bisa taku, ta yadda da za su shiga ramin damo, kuma za ku shiga.” Sai sahabbansa (RA) suka ce: “(Kana nufin) Yahudu da Nasara ne ya Manzon Allah?” Sai (SAW) ya ce: “Su wane ne in ba su ba?” Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Alkiyama ba za ta tashi ba, sai al’ummata ta kwaikwayi al’ummomin da suke gabaninta.” Sai aka tambaye shi: “Kamar mutanen Farisa da Romawa, ya Manzon Allah?” Ya ce: “Wadanne al’ummomi ne (nake nufi) in ba su ba?” Buhari ya ruwaito.
Manzon Allah (SAW) ya nuna cewa wasu daga cikin al’ummarsa za su yi koyi da Mutanen Littafi wato Yahudu da Nasara (Kiristoci) da sauran kafirai, kamar Farisawa da Romawa. Allah Madaukaki Ya ce: “Kamar wadanda suke a gabaninku, sun kasance mafi tsananin karfi daga gare ku, kuma mafia wan dukiyoyi da ’ya’ya. Sai suka ji dadi da rabonsu, sai kuka ji dadi da rabonku kamar yadda wadanda suke a gabaninku suka ji dadi da rabonsu, kuma kuka kutsa kamar kutsawarsu. Wadancan (masu yin haka) sun baci a duniya da Lahira, kuma wadannan su ne masu hasara.” (k:9:69).
Ibnu Abbas (RA) yya fassara wannan aa da cewa: “Wadancan mutane su ne Bani Isra’ila wadada za mu kwaikwaya.” Ibnu Mas’ud (RA) ya ce: “Kun yi kusan kama da Bani Isra’ila a siffa ta zahiri da dabi’u, amma ban sani ba, ko za ku bauta wa dan maraki (kamar yadda suka yi) ko a’a.”
Ya ku bayin Allah! Manzon Allah (SAW) ya haramta koyi da sauran al’ummomi. Kuma ya dace a tuna wadannan Hadisai ba suna nufin daukacin al’ummar Musulmi ne za su aikaa wannan zunubi ba, domin Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wata kungiya daga al’ummarsa za ta ci gaba da kasancewa a kan Tafarki Madaidaici har zuwa Ranar Sakamako.”
Musulmi sun kasance mafi shiriya da kyawawan dabi’u a tsakanin al’ummomin duniya da aka taba fitarwa; don haka ne a Ranar Hisabi Allah zai sanya su zama shaidu a kan sauran al’ummomi kamar yadda SWT Ya ce: “Kuma kamar wancan, Muka sanya ku al’umma matsakaiciya domin ku kasance masu bayar da shaida a kan mutane. Kuma Manzon (Annabi Muhammad) ya kasance mai shaida a kanku…” (k:2:143).
Hakika wannan matsayi ne mai girma. To yaya kuma Musulmi za su dawo suna koyi da wasu a al’adu da dabi’u da bukukuwansu? Manzon Allah (SAW) ya ma hana neman bayani kan al’amuran addini daga Mutanen Littafi, domin akwai lokacin da Umar Ibnu Khaddabi (RA) ya karanta wasu ayoyi daga littafin Mutanen Littafi ga Annabi (SAW), sai (SAW) ya fusata ya ce: “Na kawo muku addini ingantacce. Don haka kada ku tambaye su, (Mutanen Littafi) a kan komai, domin suna iya gaya muku gaskiya, ku gaskata su, kuma suna iya gaya muku karya ku iya gaskata su. Na rantse da wanda raina ke hannunSa da (Annabi) Musa yana raye ba abin da zai isar masa face bi na.” Ahmad da Ibnu Abu Shaiba suka ruwaito.    
Allah Ya sanya dan Adam da sauran halittu su zamo masu cudanya da junansu. Kuma a lokacin da kama ta karu wannan cudanya sai ta koma koyi, sai dabi’u da halaye su koma kusan iri daya, ta yadda zai yi wuya a iya bambance su.
Don haka mutane na samun tasiri ta wajen cudanya da zama wuri daya da kwaikwayar juna. Kuma sannane ne cewa idan mutum a zauna a cikin wasu nau’o’in dabbobi zai kwaikwayi wasu dabi’unsu; wannan ya sa wadanda suke kiwon rakuma suka yi suna wajen alfahari da girman kai, masu kiwon tumaki suka yi suna wajen tawali’u da sanyin hali, yayin da wadanda suke kiwon rakuma da tumakin suke dabi’antuwa da wasu miyagun halayensu.
To haka dabbobin gida sukan dabi’antu da halayen dan Adam, kamar dabi’ar yadda za su zauna da wasu.
Shi ya sa idan mutum ya sanya tufafin da malamai suka fi sanyawa, zai rika jin kamar shi ma malami ne, saboda kamanci da koyi da su ta wajen shigar tufafi yana jagorancinsa zuwa ga kamanci ta wajen dabi’u da halaye kamar yadda muke gani a zahiri, kuma ilimi da hankali sun tabbatar da haka. Masu iya magana sun ce ‘Zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai.’ Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk wanda ya kamantu da mutane, to, yana cikinsu.” Ahmad da Abu Daud suka ruwaito.
Sheihul Islam Ibnu Taimiyya (RH) ya ce: Mukan ga yadda shirka a tsakanin Yahudu da Nasaran da suke zaune tare da Musulmi kan ragu, yayin da imanin Musulmin da ke zaune cikin Yahudu da Nasara kan yi kasa da na Musulmin kirki.”
Ya ku bayin Allah! Koyi ko kamanci da mushirikai da kafirai ta waje tufafi da al’adu da dokoki da siyasa da tattalin arziki ya watsu a tsakanin Musulmi da dama fiye da kima, ta yadda ya kai a makance mutane ke kwaikwayar Turawa suna neman mayar da kansu Turawan dole, kai abin ya kai talakawa fitik da matasa da masu dukiya da kwararru suna sha’awar irin wannan mutum. Kaito da irin wannan koyi da bi-ta-zaizai. Wane irin saki na dafe ne haka? Wane irin rashin tunani ne haka? Wane irin bakin jahilci ne haka? Babu hasarar da ta fi mutum ya bi su!
Eh, bone ga koyi da kamanci da mutanen Yammacin Turai! Sun ja wasu matasan Musulmi zuwa ga duhu, sun sanya su a kurkukun dimuwa da bi-ta-zaizai, sun hana su tunani balle su gane gaskiya su kai ga nasara. Sun kange su daga samun jin dadi na hakika a zukatansu.
Bone ga kwaikwayo da bi-ta-zaizai ga dabi’un Turawa. Sunkange kwakwalensu, sun hana su komawa cikin hayyacinsu.
Al’ummar Musulmi ne ya kamata su wuce gaba, ba su rika bi ba, kamata ya yi saura mutane su dogara da mu, ba sabanin haka ba. Bai kamata al’ummarmu ta rudu da kayan alatun duniya da mutane masu hadama suka mallaka ba, domin Allah Ya ce: “Kuma kada ka mikar da idanunka zuwa ga abin da Muka jiyar da su dadi da shi nau’i-nau’i, daga gare su, kamar furen rayuwar duniya yake, domin Mu fitine su a cikinsa, alhali kuwa arzikin Ubangijinka ne mafi alheri kuma mafi wanzuwa.” (k:20:131).