Illar koyi da kafirai (2)

Daga Sheikh Su’ud bin Ibrahim AsshuraimMasallacin Harami, Makka Raunana da jahilan Musulmi da suke kokarin sake zamanantar da al’ummarmu ta hanyar kwaikwayo kamata ya yi su sani cewa, duk da cewa irin wadannan bakin dabi’u kan iya bata kyawawan namu, ba fa za su tabbata ba, kuma su ba za su zamo kamar wadanda suke […]

Illar koyi da kafirai (2)

Sheikh Abu Ibrahim Sa’ud Ibn Ibrahim Ibn Muhammad ash-ShuraimDaga Sheikh Su’ud bin Ibrahim Asshuraim
Masallacin Harami, Makka

Raunana da jahilan Musulmi da suke kokarin sake zamanantar da al’ummarmu ta hanyar kwaikwayo kamata ya yi su sani cewa, duk da cewa irin wadannan bakin dabi’u kan iya bata kyawawan namu, ba fa za su tabbata ba, kuma su ba za su zamo kamar wadanda suke kwaikwaya ba. Idan kuma wasu mutane suna ganin wajibi ne al’ummarmu ta canja yadda take tafiyya domin samun ci gaba, to, su sani komawarmu ga Littafin Allah da Sunnar AnnabinSa Muhammad (SAW) ne ta fi dacewa domin samun canji. Allah Ya ce: “Lallai Allah ba Ya canja abin da ke ga mutane sai sun canja abin da yake ga zukatansu. Kuma idan Allah Ya yi nufin wata azaba game da mutane, to, babu mai mayar da ita, kuma ba su da wani majibinci baicin Shi.” (k:13:11).
Idan muka rungumi cewa za mu zamo masu karfi ne ta yin riko tam da ka’idoji kamar azama da cijewa da karfin hali da bin koyarwar Musulunci da riko ga kyawawan dabi’unmu da suke nuna mu masu addini ne kuma muna da ka’idoji, to me zai cutar da mu daga hakan? Shin wadannan ba su ne hakikanin dabi’un Musulunci ba? Shin akwai wasu ginshikai na ci gaba da suka fi wadannan ne? Allah Madaukaki Ya ce: “(Ka ce, namu shi ne) Rinin Allah (addinin Allah)! Kuma wane ne mafi kyau ga rini (tsara dokokin rauwa) daga Allah? Kuma mu, a gare Shi masu bautawa ne.” (k:2:138).  Kuma Ya sake cewa: “Shin fa, wanin Allah nake nema ya zama mai hukunci, alhali kuwa Shi ne Wanda Ya
 Saukar muku da Littafi abin rabewa daki-daki (Alkur’ani)” (k:6:114).
Amma a ce sai mun dauki al’adun Turawa da dabi’unsu da suka saba wa Musulunci kafin mu samu ci gaba, wannan ne ba zai yiwu ba. Ya kamata mu fahimci Musulunci, Musulunci ne, shirka, shirka ce, kafirci, kafirci ne, hanyar jirgi daban ta mota daban. Mu ne jagorori a kan gaba a duniya kafin mu rungumi al’adun Turawa da suke ruguza al’ummar Musulmi – mazansu musamman mata wadanda saboda rashin sani suke haba-haba su kwaikwaye su. Kayayyakin kawarsu da ci gaban masana’antunsu suna burge su, ta kai fitsararrun mata suna yi musu makauniyar biyayya ta yadda suturarsu ta zamo daidai da ta ’yan mata ’yan kwalisar Turawan. Duk lokacin da ka ga mace Musulma ta sanya suturar da ba ta cika rufe mata tsaraici ba, to tana kwaikwayar suturarsu ce.
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ban ga wadanda suke da karancin hankali da addini kuma (a lokaci guda) suke kwace hikimar mazaje masu hikima irin ku (mata) ba.” Buhari da Muslim.
Wannan ne ya sa Allah Madaukaki Ya ce: “Sai Muka karba masa (addu’ar Zakariyya) kuma muka kyautata masa matarsa…” (k:21:90). Wannan aya tana nuna irin rahamar da aka yi wa Annabi Zakariyya ta samun mace tagari.
Kuma Allah Ya sake cewa: “Salihan mata masu da’a, masu tsarewa ga gaibi, saboda abin da Allah Ya tsare…” (k:4:34).
Don haka ya ku Musulmi! Dokokin da addininmu ya sanya ga dan Adam ba ya yi ba ne domin musgunawa ko hana shi jin dadin rayuwa. Maimakon haka, manufarsu ita ce ta bambanta shi da dabi’a irin ta dabba domin ya zama cikakken muttum. Don haka Musulmi zai iya magance matsalolinsa ya dogara da kansa, imaninsa da muru’arsa su hana shi bin muguwar sha’awa irin ta dabbobi.
A lokacin da al’umma ta yi watsi da wadannan dokoki ko ta yi sakaci da su, za ta bude kofofin manyan matsaloli ga kanta, kuma ta tura kanta ga mahalaka kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma wanda ya ketare iyakokin Allah, to wadannan su ne azzalumai.” (k:2:229). Kuma Allah Ya sake cewa: “Kuma wane ne mafi bata daga wanda ya bi son zuciyarsa, ba tare da wata shiriya daga Allah ba? Lallai ne, Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai.” (k:28:50).

Huduba ta Biyu:   
Manzon Allah (SAW) ya hana duk wani abu da zai zamo koyi ne da kafirai, ta kai har wani Bayahude ya ce: “Wannan mutum (Annabi SAW) ba ya da niyyar kyale wani abu daga harkokinmu face ya aikata sabaninsa.” Muslim ya ruwaito.
Kuma an ruwaito cewa Annabi (SAW) ya hana Musulmi yin Sallar Nafila bayan Sallar Asuba har sai rana ta fito da kuma bayan Sallar La’asar har sai rana ta fadi. Ya nuna cewa rana tana fitowa da faduwa ne a tsakanin kahonnin Shaidan, kuma a wannan lokaci kafirai suna yi mata sujuda. Sanannen abu ne cewa mumini ba ya sujuda ga kowa sai Allah; mutane da dama ba su cika hankalta cewa rana ttana fitowa da faduwa ne a tsakanin kahonnin Shaidan kuma mushirikai suna yi mata sujuda, don haka ne Annabi (SAW) ya umarci Musulmi kada su yi Sallah a wannan lokaci domin kada su yi koyi da kafirai ta kowace fuska.
Koyi da Mutanen Littafi da sauran mushirikai zai kai mutum ya rika sha’awarsu. Kan haka ne aka hana koyi da su, domin a toshe kafar da irin wannan soyayya za ta gudana kuma a yi rigakafin yi musu mubayi’a; wannan baya ga wasu hujjoji da suka hana irin wannan koyi ne.
A fili yake wasu mutane da suke kwaikwayar kafirai ta sutura da al’adu da dabi’u ko suke fifita harshensu, suna nuna musu soyayya da girmama su. Ta irin wannan hanya ce kafiran suka samu nasarar cusa musu akidar duniyanci da kyamar addini da kiyayya ga Musulmi, kuma suna yin haka ne domin lalata dabi’un Musulmi da haibarsu. Duk lokacin da mutum ya ki irin wannan sabuwar koyarwa tasu, sai a rika jifarsa da mai tsaurin ra’ayi ko bagidaje ko ma wawa da bai san inda duniya ta sanya gaba ba.   
Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma Yahudu ba za su yarda da komai daga gare ka ba, kuma Nasara ba za su yarda da, sai ka bi irin akidarsu. Ka ce: “Lallai ne shiriyar Allah ita ce shiriya.” Kuma lallai ne idan ka bi son zuciyoyinsu a bayan abin da ya zo maka na ilimi, ba ka da, daga Allah wani majibinci, kuma babu wani mataimaki.” (k:2:120). Kuma Ya sake cewa: “Suna gurin ku kafirta kamar yadda suka kafirta, domin ku kasance daidai.” (k:4:89).