Illar kwafar aikin wani
Akwai wasu ’ya’yan Sarki biyu masu suna Hajara da Delu, Hajara ita ce ’yarsa ta farko kuma ta fi hankali da ilimi ga kuma natsuwa. Ita ko Delu a kullum tana son ganin gazawar ’yar’uwarta Hajara. Tana son ganin ta wuce ta a aji saboda a fi sonta a gida kamar yadda ake son Hajara.Ranar […]
Akwai wasu ’ya’yan Sarki biyu masu suna Hajara da Delu, Hajara ita ce ’yarsa ta farko kuma ta fi hankali da ilimi ga kuma natsuwa. Ita ko Delu a kullum tana son ganin gazawar ’yar’uwarta Hajara. Tana son ganin ta wuce ta a aji saboda a fi sonta a gida kamar yadda ake son Hajara.
Ranar nan malamarsu ta ba su aikin gida (Home work) a kan kowa ya dinka wa kansa riga mai fuffuke yadda rigar za ta yi kama da tsuntsu. Idan kuma daliban ba za su iya yin haka ba, to su yi kowace irin riga amma wacce za ta burge.
Da aka koma gida kowa ya samu allura da zare sai kokarin dinki yake. Hajara dai ta kamanta kuma kayanta ya yi kyau. Sai ta kai dakin Delu don nuna mata irin kayan da ta dinka. Delu na ganin kayan sai ranta ya baci. Sai yar’uwarta ta ba ta allura da zare kan cewa idan tana son wani taimako ta yi mata magana.
Delu ba ta son nuna cewa ba ta iya komai ba sai ta nufi gidan wani mai tsafi, ta ce da shi ya ba ta rigar tsuntsu yadda za ta fi kowa kyau. Sai ya ba ta wani dutsi yac e ta matsa idan ta isa makaranta.
Washegari Delu ta je makaranta ta matsa dutse kawai sai rigar tsuntsu ya fito a jikinta fiye da na ‘yar’uwarta. Tana shiga aji aka bata namber daya har da kyauta daga malaman.
Sai ta kasa cire kayan da ta isa gida ashe mayar da ita tsuntsun gaske akayi. Sai ta gaya wa yar’uwarta suka fadawa malamansu da kyar ta dawo mutum. Sannan aka yi mata bulala goma saboda abin da ta yi.