Illar rashin yi wa miji biyayya
Wata mata ce da Allah Ya albarkace ta da ‘ya’ya hudu da mijin mai biya mata bukatunta daidai gwargwado amma kash ita dai duk abin da ya yi mata ba ta gode wa hasalima gani take dole ne ya yi mata abin da take bukata ko yana so, ko ba ya so. Wata rana da […]
Wata mata ce da Allah Ya albarkace ta da ‘ya’ya hudu da mijin mai biya mata bukatunta daidai gwargwado amma kash ita dai duk abin da ya yi mata ba ta gode wa hasalima gani take dole ne ya yi mata abin da take bukata ko yana so, ko ba ya so.
Wata rana da sallah ta gabato sai ya sayi mata kayan sallah da ita da ‘ya’yanta. Yana shigowa gida sai ya kira ‘ya’yan nata a yayin da take kicin tana girki. Jin hayaniyar da ’ya’yan keyi a falo ya sa ta bar kicin ta je don ta ga abin da ka faruwa. Sai ta tarar ashe babansu ne ya sayo masu sababbin kaya kuma suna ta shewa don murna. Da ta isa falon ne sai ta yi kerere babu ko sannu da dawowa maigida. Maigidan ko kula ta bai yi ba ya cigaba da gwadawa yaransa musamman dan karamin cikinsu rigar da ya sayo masa. Can kuwa sai ta ce ‘haba Baban Abba ka rasa irin kayan da za ka saya musu sai irin wannan?
Ya ce mata sai da ya tambaya kuma aka ce masa masu kyau ne. Sannan ya dauko nata ya ajiye a gabanta. Ta kalli kayan ta ce masa ita da ma kudin ya ba ta don ta saya da kanta da ya fi.
Maigida ya ce gara a cuce shi da ya bar matarsa ta shiga kasuwa wajen cunkoson jama’a. Nan take ta yi masa tsaki ta koma kicin tana guna-guni.
Ta yi ta sake-saken yadda za ta bullo wa wannan al’amari. Sai washegari da mijinta ya tafi aiki sai ta aiki danta na biyu ya tafi gidan mai adashi ya karbo mata kudin adashinta. Can yaro ya kawo mata kudi sai ta saba danta karami a baya ta fada wa sauran yaran cewa tana zuwa ba za ta dade ba. Tana sauri ta je ta sayo wa yaranta kayan da take ganin sun fi na mijin kyau ko irin wanda za su tserewa tsara. Ta shiga a daidaita sahu sai ga hadari ya murtuke kamar ta koma gida amma wata zuciya ta ce ta tafi kawai. Ba ta kai kasuwa ba ruwa ya tsinke kamar da bakin kwarya. Da suka isa kasuwa, tana ta tunanin yadda za ta shiga ruwa sai ta ga wasu mata ‘yanuwanta suna kai wa suna komowa sai ita ma ta fita ta rintuma cikin kasuwa. Ruwa na ta dukanta tare da danta. Ya yi ta kuka amma ta rasa inda za ta tsaya don ta ba shi nono saboda yawan mutanen da ke karakaina a kasuwar. . Da kyar ta samu wani shago ta fake. Ta rika nuna irin kayan da take son ta saya ana miko mata kaya ana miko mata hankali a tashe ba ta san zaben da ta ke yi ba. Yaro tun yana kuka ya yi shiru abinsa. A yi lissafi ta ja jaka za ta ba da kudi, kudi ya ce dauko ni inda kika ajiye. Ta zazzage jaka babu ko sisi, daga nan ta san ‘yan sane sun cika aiki. Mai shago ya yi mata tsawa da ta fita masa daga shago. Ta fita rai a bace kuma ga shi ana ruwa. Can sai wani ya ce mata da dai ta dubi goyonta don kamar ba shi da rai. Jiki na rawa ta sauke yaro sai ta sa ihu aka taru, aka yi ta ba ta magana. Ta goya shi tana sauri ta koma gida kafin maigida ya dawo. Ta kai unguwarsu ke nan sai ta ji ana yi mata jaje. Tana shiga shiga gida sai ta tarar da daya daga cikin ’yarta kuma gidan a hargitse da alamar an yi gobara, kuma ya shafi falo da kicin. ‘Yarta ce ta ba ta labarin yadda mahaifinsu ya shiga kichin wai yana jin yunwa sai ya yi kokarin kunna murhun gas don ya yi abinci saboda yana jin yunwa daga nan ne wuta ta tashi, inda ta kama wani sashe na gidan kuma ta kone kayan da ke ciki kurmus.
Daga nan ne ta wuce sannan ta shinfida gawar danta na goye da ya rasu tana tunanin abin da za ta yi ,can sai ga maigidanta ya shigo inda take. A nan ne ta fada masa cewa dansa na goye ya rasu tun a kasuwa. Daga nan ya kalle ta, hawaye na zuba. Ya fita ya nemo makwabta inda aka yi wa dansa sutura aka kai makabarta kuma aka binne. Bayan an dawo daga makabarta ne ya rubuta mata takardar saki, kuma ya ba ta, ya nemi ta fice masa daga gida.
To wannan darasi ne ga mata musamman wadanda ka takura wa mazaje a kan abin da bai zama dole ba. Mata, ga sallah ta gabato ya kamata mu yi wa kanmu karatun ta natsu musamman a wannan lokaci na mayuwancin hali na rashin kudi. Dole ne mace ta gode wa Allah da irin ni’imar da Ya yi mata. Rashin godiya ne da butulci ga Ubangiji mace ta tilasta wa maigida ya yi mata kayan sallah ko yana da shi ko babu.
A cewar shahararriyar malamar nan Rabi’autu Sufiyanu Ahmad a yayin da take tattaunawa da Aminiya ta ce, duk macen da Allah Ya yi mata kyauta ba ta gode maSa ba, lallai tana cikin bala’i duniya da lahira.
“Duk matar da take ganin dole sai mijinta ya yi mata kayan sallah to duk ladan da ta samu a watan Azumi zai tafi a banza saboda zunubin da za ta kwasa. Saboda haka duk wace ta dora wa mijinta abinda ya fi karfinsa, Allah Shi ma zai dora mata azabar da ba za ta iya ba kuma dole ta dauke ta. Saboda haka mu yi hattara mata.”
Malamar ta ci gaba da kira ga iyaye mata da su yi wa yaransu nasiha ta gaskiya, tare ba ba su hakuri da irin halin rayuwar da ake ciki.
“Allah Mai girma da daukaka a Suratul asr Yana cewa mutane na cikin asara face wadanda suka yi imani sannan suka yi aiki na kwarai sannan suka yi wa junansu nasiha ta gaskiya.” Saboda haka dole ne mata mu kasance masu yi wa ‘ya’yanmu nasiha ta kwarai.”
Allah Ya sa mu dace