Illar sauya ra’ayi a siyasar Arewa

’Yan siyasar Arewa na da hanyoyi da dama da suke amfani da su wajen yaudarar jama’a, ta yadda mutane kan yi tunanin karesu suke yi, ku sun dauke su a matsayin ‘yan uwa. Musamman domin dan Arewa ya fi so a nemo a ba shi! A dalilin haka ne wasu talakawa kan yi kokarin samun […]

Illar sauya ra’ayi a siyasar Arewa
Illar sauya ra’ayi a siyasar Arewa

’Yan siyasar Arewa na da hanyoyi da dama da suke amfani da su wajen yaudarar jama’a, ta yadda mutane kan yi tunanin karesu suke yi, ku sun dauke su a matsayin ‘yan uwa. Musamman domin dan Arewa ya fi so a nemo a ba shi! A dalilin haka ne wasu talakawa kan yi kokarin samun duk da abin da zai shigo a lokacin zabe kafin dan takarar ya yi musu nisa!. Su kansu ‘yan siyasar kan yi tunanin mabiyansu a matsayin wadanda kan nemi abin da za su samu a lokacin kamfen shikenan. A nan sai a yi kasafi mai zai kashe, kai me zaka samu, domin idan ku ka kuskura aka yi zabe baku sami wani abu ba, ya gama da ku!
A yayin da zaben 2015 ke matsowa, sun fara nuna muhimmancin addini da yi kamar kai a hade yake, duk da duhun da yankin ya fada saboda yake-yake da bakin talauci don su sami kuri’u. Wani abin bakin ciki da takaici shi ne har wasa suke da tsaron kasar, wai su suna tare da mu, don su tsaya takara bayan duk abin da aka yi da su aka yi!. Abin har ya kai wasu gwamnoni na nuna shugaba Jonathan ya jawo talaucin da ya addabe jihohinsu, ko rashin tsaron da ake fuskanta a jihohin da shi ne sababi, wannan abin takaici ne, mutane su bar nuna laifin wani bayan su suka jefa Arewa halin da ta fada, su ‘yan siyasar Arewa nan da wasu malaman addini suka goyi bayan Jonathan a zaben shekarar 2011, inda suka ba shi 20% da yake bukata ya zama shugaban kasa daga kowace jiha, har ana cewa sai mai fitsarin tsaye.
A wannan lokacin ne wasu suka sauya Goodluck Jonathan zuwa Mai nasara. Da gangan ake barin mutane cikin jahilci, inda ko malaman addini ba a iya tambaya game da hukunce-hukuncen da suke dauka, musamman domin kar ku yi rashin ladabi! Duk da halin da Arewa ta fada wasu manya mutane wai su dattijai na goyon bayan Jonathan a zabe mai zuwa!
Idan mutane ba su manta ba da yadda Gwamna Murtala Nyako ya goyi bayan Goodluck, har yake masa kirari da Mai nasara, ne mafi alherin da ya taba faruwa a Najeriya. Kuma ya tsaya masa a kan Atiku da Buhari a zaben da aka yi a 2011, abin tambaya shi ne shin me ke kawo sauyin ra’ayi cikin kankanen lokaci? Ko wai duk tsawon lokacin nan tsohon Gwamnan Jihar Kano Ibrahim Shekarau bai gane PDP ce mafitar Najeirya ba sai yanzu! Ku ji yadda gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu ke wa Jonathan kamfen a Arewa!
Hakan ya zama wata dabi’a ga ‘yan siyasar Arewa, da zaran iskan siyasa ya kada sai su wa ‘yan hamayya sharri, domin magoya bayansu su amince da su. Tabbas duk mai gani da madubin zahiri ya san wadanan mutane ba don Arewa suke magana ko neman tsaya takara ba!. Maimakon a baje hujoji da ayyukan da aka wa talakawa ko yadda yaka nuna kulawa ga ‘yan uwa ko abokan arziki a baya, A’a daga sama za a nuna matsayi a bisa nawa aka kashe a kasa!
Lokaci ya yi da mutane zasu gane cewa ‘yan siyasar Arewa ba abin da suke yi sai tara abin da za su gina kansu da abin da za su bar wa iyalensu. Sun sauka daga tsari irin na ‘yan siyasar farko irinsu Malam
Aminu Kano da Alhaji Abubakar Tafawa balewa da Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato wadanda kan dauki mutanen mazabu da muhimanci. Su kan yi amfani da mu don arzuta kansu, su nemi suna, amma ba wai don ci gaban Arewa ba. Babban abin takaicin shi ne ba ta yadda za su iya yin hakan sai sun nuna suna tare da mu, bayan suna tare da mai malfa.
Abin ya kai ga har ana amfani da addini, ko darika don samun mabiya, sai ka iske ‘yan adawa na tare da ‘yan Izala, ko ‘yan darika na tare da gwamnati ko ‘yan Shi’a na goyon bayan wannan dan takarar ko wancan don neman jama’a. A nan ma gwamna zai iya shirya zaman da za su rika yi don tattauna bambance da ke tsakani don fahimtar juna, amma shi biyayya da yawan jama’a ya ke nema. Wanda ba ruwansa da ku ya fara muku magana ko salla a masallatai mabambanta don a ce yana da jama’a! Duk wannan a sunan siyasa.
‘Yan Kudu ba haka suke siyasa ba, da farko ba wanda zai tsaya takara sai ya tabuka wani abu kafin lokacin zabe! Wannan ya kara nuna mana da yadda ake siyasa a kauyuka inda ba maganar ra’ayi ake ba, ana maganar nawa za a samu kafin a yi gaba a bar mutane da hayakin mota, kanananan hukumomin da dan sanda daya ya isa ya tarwatsa ko ba bindiga, balle an ganshi da barkonon tsohuwa!
Shi yasa su kansu talakawan Arewa kan taka rawar gani wajen wannan sauya ra’ayin na ‘yan siyasar yankin, inda da mutum ya watsa tsaba sai ka iske mutane a gaban gidansa, sai abin da ya fada! Abin da a
kwananan har tsakar dare akan iske mabarata a kofofin ‘yan siyasa suna zaune, wasu garurruwan ma tare wa ake irin wadannan gidajen!
Yanzu wasu sun  fara komawa kauyuka tare da yawan kai ziyara da zuwa daurin aure da gaisuwa duk don an kusa kada gangar siyasa, inda za su kwashi ribar jarin da suka zuba a kasa! Yaushe rabon da ku ga keyarsu a kauyuka ko a kasar? Mutanen da suka san mutunci na nan birjik a Arewa, da su muke zama da tashi, tabbas akwai mutanen kirki a Arewa.

Za a iya tuntubar Daure a shafin sadarwarsa na [email protected]

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya