Illar shafe-shafen man kara girman mama ga mata
Masana kiwon lafiya sun yi gargadi kan illar amfani da mayukan kara girman mama.
Ganin yadda zamani ya zo da wani salo inda wadansu mata ke shafe-shafen mayukan kara girman nono da zummar jan hankalin maza, masana harkar kiwon lafiya na gargadin cewa hakan na jawo sankarar nono na mata.
Maryam Abubakar, wata kwararriyar ma’aikaciyar jinya ce da ke aiki a Babban Asibitin garin Dutse na Jihar Jigawa, a wata hira da Aminiya ta ce ko shakka babu shafe-shafen mayukan na daya daga cikin hanyoyin da ke haddasa kansar mama.
Ta ce matan na amfani da magunguna da mayukan da suke shafawa ba tare da suna la’akari da illolin da ke tattare da su ba.
Kamar yadda ta shaida wa Aminiya, galibin asibitocin a jihar na bai wa mata da masu zuwa awo wata jaka mai dauke da kayayyakin gwajin cutar sankarar da man da ake shafawa domin maganin cutar.
Alamomin sankarar
Maryam Abubakar, ta ce idan mace ta matsa nononta ta ji akwai wani kullutu ko ta matsa bakin nonon ta ga wani ruwa mai launin rawaya na fita to akwai alamar sankarar.
Ta bayar da shawarar da zarar mace ta ga wadannan alamomin, ya kamata ta je asibiti ta ga likita domin a ba ta magani.
Ta ce jakar da ake bai wa matan a asibitocin jihar, na kunshe ne da mai mai santsi wanda idan mace ta ji wannan kullutu za ta rika shafawa a matsayin kandagrki kafin ta je asibiti domin fara magance sankarar.
Jami’ar jinyar, ta yi kira ga Malaman Addini da Sarakunan gargajiya da su rika bai wa maza shawarwari kan suna barin matansu na zuwa awon ciki domin samun kariya daga yawan zubar ciki da samun hanyar kariya daga kamuwa daga cutar sankarar maman.
Jami’ar kiwon lafiyan ta hori mata masu juna biyu a musamman a Jihar Jigawa da su tabbatar suna ziyartar asibiti domin samun gidajen sauro kyauta domin kare lafiyar jikinsu daga zazzabin cizon sauro da ma jariran da suke dauke su.
Ta ce a asibiti ne kadai mace mai juna biyu za ta samu kulawar da ta dace.