NAJERIYA A YAU: Illar Shiga Jerin Sunayen Masu Ɗaukar Nauyin Ta’addanci

Gwamnati ta bayyana Tukur Mamu da wasu mutum 14 cikin jerin sunayen.

NAJERIYA A YAU: Illar Shiga Jerin Sunayen Masu Ɗaukar Nauyin Ta’addanci

‘Yan kasa sun jima suna kalubalantar gwamnatin tarayya ta ayyana sunayen masu daukar nauyin ta’addanci.

Watakila gwamnatin ta duba wannan batu domin kamar yadda wasu suka ji a labari, ta bayyana sunan Tukur Mamu na jihar Kaduna da wasu mutum 14 waɗanda ɓaro-ɓaro ba za a iya cewa ta ambaci suna ba.

Shirin Najeriya a Yau ya duba matakan doka kan ayyana sunan wanda aka samu da daukar nauyin ta’addanci.

Domin sauke shirin, latsa nan

Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani

Yau Majalisar za ta ci gaba da aiki kan Dokar Haraji

Kotu ta tsige Ohinoyi na Ƙasar Ebira

Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano