Illar tallace-tallacen ‘yan dugwi-dugwi
’Yan dugwi-dugwi muna ganin cewa tallar da suke yi talalar talauci ne ai ta talau-talau ce yake kawo shi saboda neman yadda za a tsira da rayuwa. Wasu daga cikinsu ko makarkata ba sa samun damar zuwa sai sun yi ta karkarwa saboda yanayin da suke ciki tare da iyayensu.Wasu ’yan dugwi-dugwin kuma suna zuwa […]
’Yan dugwi-dugwi muna ganin cewa tallar da suke yi talalar talauci ne ai ta talau-talau ce yake kawo shi saboda neman yadda za a tsira da rayuwa. Wasu daga cikinsu ko makarkata ba sa samun damar zuwa sai sun yi ta karkarwa saboda yanayin da suke ciki tare da iyayensu.
Wasu ’yan dugwi-dugwin kuma suna zuwa koyon watsatstsakene amma da zarar sun dawo za su kauki kayan talla don samo yadda za su biya kukin makaranta da kukin zuwa Islamiyya da sauransu. Kakan daga cikin illolin tallace- tallacen ’yan dugwi-dugwi su ne;
’Yan dugwi-dugwi sukan yi mu’amala da jama’a wajen yin tallace-tallacensu ciki har da lalatattu da abokai na banza su koya musu shaye-shaye da romo irin na kayan bokan Turai da kara wa duniya hazo da yawon ta zubar, saboda ganin iyaye sun kasa kula ko kaukar nauyinsu a yau da kullum.
Kuma ta nan ne ake cusa wa ’yan dugwi- dugwi wasu kabi’u marasa kyau kamar bizi ko siriyal na bayye, shaye-shaye da romon jaba, neman mata, harkar neman maza da ire-irensu.
’Yan dugwi-dugwi mata kuma suna fuskantar matsala babba wajen kaukar na masara ba na gaban fatiha ba da kuma fakawa ga kaurayen karuwanci, shaye-shaye, makigo, a gidajensu kuma iyayensu sun sa musu na mujiya wai don suna kawo musu na koko, kaico ’yan dugwi-dugwi suna kawo musu na makancewa, kai iyaye ko ba ku sani ba ne ehe!
Wayyo-wayyo! Abin da nake son kara faskare a nan shi ne, mace za ta kauko tallar kayan da ba su fi sili da zagaye da zagaye da zagaye ba, amma wani zai ba ta Naira karamin lauje da zagaye da zagaye da zagaye, ya ce ta raba wa yara abin da take sayarwar. Haka gobe ma zai neme ta , ya biya bukatarsa a kan kukin da zai ba ta, ta koma gida ko ta je ta sayi kayan sawa, sannan ta ci abin da ranta yake so na more rayuwa, wanda iyayenta ba za su iya saya mata ba, kuma ba tare da bincike ba. Da haka da haka ita ma za ta zama mai zaman kanta don ta san maza da yadda za ta samu damin Hauro, suna hauro mata ba kakkautawa. Wasu ma har da shorido a hannun duk wani namiji da take so ta karbi kuki a hannunsa.
Hakan kuma yakan sa matan su jawo sauran kawayensu wajen koya musu yadda za su samu damin Hauro . Wasu masu tallar kuma yara ne kanana, wakanda masu gadi ke jan hankalinsu su yi lalata da su har ta kai ga sun lalata musu rayuwa. Idan aka ce kai ne ko ke ce idan da ’yan dugwi-dugwi kin yaya za ka yi? Daga nan shi ke nan sai su shiga neman maza a unguwanni, har su ma suke jan makwabtansu