Illar tsananin kishi
Labarin ya yi nuni ne ga irin masifar da mutum yake shiga idan ya kasance mai tsananin kishi.
Assalamu alaikum manyan gobe, tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labari a kan ‘Tsananin kishi.’
Labarin ya yi nuni ne ga irin masifar da mutum yake shiga idan ya kasance mai tsananin kishi.
- Gwamnati na kashe $10m wajen ciyar da dalibai miliyan 10 —Ngige
- Jerin ’yan kwallo 10 da suka samu kudi mai tsoka a 2022
A sha karatu lafiya:
Hamida da Kausar gimbiyoyi ne a Masarautar Kaho inda mahaifinsu ne Sarki a garin. Hamida ita ce babba a kan Kausar.
Baki dayansu sun isa aure amma Sarki ya ce ya fi son aurar da babbar ’yarsa kafin karamar.
Akwai wani Yarima wanda kauyensu ke makwabtaka da garin Kaho, ya yanke shawarar aurar daya daga cikin wadannan ’ya’yan Sarki.
Labari ya iso garin Kaho duk an shirya da su kide-kidensu da sauransu a lokacin da Yarima ya isa. Ita ko Hamida ta yi ado amma hankalin Yarima yana kan Kausar.
Sai ya ce da Sarki shi Kausar yake so ba Hamida ba. Wannan ya bakanta wa Hamida rai sosai wanda hakan ya sa ta kashe kanwarta ta tura ta a cikin wani kogi.
Can aka gano gawar Kausar a wani kauye inda wani makadi da ya yi ta kallon lokacin da aka ciro ta daga ruwa. Aka binne ta.
Da Yarima ya rasa Kausar sai ya yanke shawarar auren Hamida kuma ana cikin biki sai makadi ya zo da gangarsa, ganga ta fara fadin cewa Hamida ce ta kashe ta, har aka gano gaskiyar magana.
Hamida don razana sai ta samu tabin hankali. Haka ta kasance kuma ba ta auri Yarimar ba.