Illolin da ke tattare da hassada da sakamako ga mai yin ta 1

Masu karatu, ina yi muku sallama, Assalamu alaikum. A yayin da za mu fara bayani game da hassada, ya kamata mu binciki karin maganar nan ta Malam Bahaushe, inda ya ce hassada ga mai rabo taki ce. Idan muka tsaya ga wannan magana ma kadai, ta isa ta fassara mana maudu’inmu na yau, domin kuwa […]

Illolin da ke tattare da hassada da sakamako ga mai yin ta 1
Illolin da ke tattare da hassada da sakamako ga mai yin ta 1

Masu karatu, ina yi muku sallama, Assalamu alaikum.
A yayin da za mu fara bayani game da hassada, ya kamata mu binciki karin maganar nan ta Malam Bahaushe, inda ya ce hassada ga mai rabo taki ce. Idan muka tsaya ga wannan magana ma kadai, ta isa ta fassara mana maudu’inmu na yau, domin kuwa kamar tana nuni da cewa lallai hassada na taimakon mutum a rayuwa, watau ba cutar da shi take ba. Idan muka yi nazari sosai, za mu ga yadda taki ke taimakon tsiro. A duk lokacin da manoni ya samu takinsa, na gargajiya ko na zamani, ya barbada a gindin tsiron shukarsa, to kuwa za ka ga tsiron nan ya yi kore shar, yabanya ta tashi cikin koshin lafiya da kaurin gaba. Idan amfanin ya nuna kuwa, za ka same shi da nagarta da inganci. Taki ya yi amfani ke nan, kamar kuma yadda aka ce hassada taki ce, to haka take yi wa mutum, ta maida shi managarci mai samun nasarar al’amuransa. Yadda haka ke kasancewa kuwa, shi ne darasinmu na yau.
Abin da za mu fara ganewa da hassada shi ne, a duk lokacin da mahassadi ya yunkuro da hassadarsa, to ya kulla babban yaki ne da Allah Ubangiji, Buwayi gagara misali, Mai kowa, Mai komai. Ya kulla yaki ne da kudurar Allah, kasancewar Shi ne ke wanzar ko gudanar da dukkan wani abu da Ya ga dama, kuma a duk lokacin da Ya ga dama. Shi kuwa mai hassada, idan ya ga wannan iko na Allah Yana gudana ga wani bawanSa, sai ya shiga nukura da makarkashiya, da nufin dakile faruwa ko ci gaban wanda yake wa hassadar. Inda Gizo ke sakar shi ne, wannan mutum da Allah Ya nufa da samun wani ci gaba ko karuwa, ba shi ya ba kansa nasara ko karuwar ba; Allah ne Ya bude masa kofa kuma Ya ba shi karfi da hikima da basirar yin abin da yake yi. Don haka, Allah ne zai jagorance shi kuma Ya kare masa duk wata fitina ko kandagarki da zai hana shi cimma burinsa. Ke nan Allah zai yi fada da yaki ga duk wani mahassadi da zai nemi cutarwa ko hana wannan mutum cimma kudurinsa. Idan Allah na fada da mahassadi kuwa, wane ne zai cece shi?
Ke nan, a lokacin da mahassadi ke wa wani nukura da hassada, Shi kuma Allah Yana nan Yana kare shi, Yana kara masa hikima da basira da karfin gwiwar tunkarar aikinsa ko sana’arsa ko kuma duk wani abu na rayuwa da ya sanya gabansa, wanda cikin ikon Allah zai samu nasara, domin kuwa mahassadin nan ba zai yi wani tasiri a rayuwar wannan mutum ba da Allah Ya nufa da samun ci gaba.
Wani dalili na biyu da ke sanyawa hassada ta taimaki wanda ake wa hassadar shi ne, a lokacin da mahassadi ke hassada, aikinsa da al’amuransa duk za su tsaya ga hassadar nan kawai. Zai maida hankalinsa da karfinsa domin ganin ya cimma mummunar manufarsa ga mutumin da ya sanya wa kahon zuka. Ke nan shi mahassadin zai tattara ayyukansa ya jefar a gefe guda, watau ya tsayar da lamurransa ke nan domin ganin ya cimma mummunar manufarsa. A daidai lokacin da yake bata lokacinsa da karfin jikinsa wajen wannan bakin buri, shi kuma mutumin da ake wa hassadar yana can yana ta aiki tukuru, yana kokari da himmar aiwatar da ayyukansa. Haka kuma mutumin na tare da ikon Allah da kariyarSa, wanda haka zai sanya ya samu nasarar dukkan abin da ya sanya a gabansa. Idan haka ta faru, hassadar da aka nuna masa ta zama taki ke nan a gare shi.
Wani dalili na uku da zai sanya hassada ta zama taki ga mutumin da ake nuna wa ita shi ne, a duk lokacin da mutum ya ankara da wani da ke masa makarkashiya ko kutungwila, shi kuwa zai jajirce, ya kara himma domin ganin cewa ya kauce wa illar da wannan mahassadi ka iya yi masa. Tare da ikon Allah da kariyarSa, sai ka ga ya kauce daga irin wannan makirci da mahassadi ke shirya masa. Sannu a hankali sai ka ga yana ta kara samun daukaka da nasara a lamurransa, ya Allah kasuwanci ne, aiki ne ko ma dai mene ne yake yi a rayuwa.
Haka kuma, a lokacin da mahassadi ke hassadarsa, wanda ake wa hassadar kuma yana ganin budi da nasara, to ciwo biyu ko asara biyu za su baibaye wannan mahassadi. Asara ta farko ita ce, ya sanya kansa cikin halaka, domin duk mutumin da ke fada da ikon Allah, tabbas ya sanya kansa cikin mummunar halaka ke nan. Na biyu kuma, ya sanya kansa cikin hasara da bakin ciki. Zai yi asara ne saboda lokacinsa da zai bata a yayin da yake hassada. Zai kasance cikin bakin ciki ne a duk lokacin da mutumin da yake wa hassadar ya samu nasara da ci gaba. Ke nan hassada mummunan hali ne, marar kyau kuma marar tasiri ga rayuwar al’umma.
Babban darasin da maudu’inmu na yau ke nunawa shi ne, mu kaurace wa duk wani nau’i na hassada. Mu fuskanci ayyukanmu ko sana’o’inmu cikin nasiha da neman albarka wurin Allah. Mu sani cewa duk abin da muka samu Allah ne Ya kadarta kuma Ya huwace mana. Abin da ba mu samu ba kuwa, mu dauka haka shi ne mafi alheri da Allah Ya nufa gare mu.
Muddin dai  muna son ci gaba, muna son farin ciki da ci gaba a rayuwarmu, to mu kaurace wa hassada da ayyukan hassada, domin kuwa ita taki ce ga dukkan mai rabo, ko kuma ga dukkan wanda Allah Ya nufa da samun rabo ko nasara. Sai kuma mako na gaba, za mu kawo muku wani maudu’in.