Illolin da ke tattare rashin bin ka’idojin rubutu

Ashe rashin bin ka’idojin rubutu mugun abu ne? Ba ma mugu ba, mummunan abu ne mara kyawun gani da rashin dadin azanci. Rashin bin ka’idojin rubutu bala’i ne mai karya tattalin arzikin rubutu da marubuta. Bari ku ji dalilina:Ina kwance ina ta faman juyin rashin lafiya amma wayata na hannuna. Da zarar na ji zazzabi […]

Illolin da ke tattare rashin bin ka’idojin rubutu

Misalin littafin da ya samu ingancin dab’i da bin ka’idojin rubutuAshe rashin bin ka’idojin rubutu mugun abu ne? Ba ma mugu ba, mummunan abu ne mara kyawun gani da rashin dadin azanci. Rashin bin ka’idojin rubutu bala’i ne mai karya tattalin arzikin rubutu da marubuta. Bari ku ji dalilina:
Ina kwance ina ta faman juyin rashin lafiya amma wayata na hannuna. Da zarar na ji zazzabi ya sauka sai na leka Fesibuk ko wata tashar daban a intanet. A irin wannan lokutan ne ma na samu na sanar da halin da nake ciki.
Na bude wani gida ina karanta rubuce-rubuce da labarun ciki, a nan na yi karo da wani dogon labari. A zatona dogon labarin zai yi ma’ana kuma zai kayatar. Da na soma karantawa sai na ji kaina na juyawa, zuciyata na tashi, tsigar jikina na motsawa ‘yarrr!’
Wato rubutun ne gaba daya a cakude, ga shi nan cike da baragada, ga rashin karbabbiyar Hausa, ga bankaura, ga shirme, ga shashanci. Kawai misalin rubutun shi ne, ka dauko danyen kashi ka jefa a farar shinkafa, sannan ka cakuda ka soma kai wa baki.
Kafin na kai rabin rubutun, tuni zuciyata ta gaza, sai ga amai da karfinsa. Na yi ta kwarara amai ina murkususu. Nan da nan zazzabi ya dawo, wanda ya fi na baya karfi. Aka ce wai ina ta surutai ina cewa: ‘….Allah wadan wane mai rubutun labari kaza…’ Daga nan dai ban sake samun kaina ba sai washegari da yamma.
Don haka ya ku marubuta, ku taimaka ku ceci rai, ku rika rubutu mai kunshe da mafi yawan ka’idojin rubutu. Wanda bai sani ba ya tambayi wanda ya sani. Abin murna kuma ga malamai kullum a shirye suke su koyar da wadannan ka’idoji. Wanda ba marubuci ba kuwa, ya daina kankanbar rubutu matukar bai iya kiyaye ka’idojin nan. Idan ba haka ba wata rana za ku yi kisan kai alhali ba ku sani ba.
Ni dai kam daga yau ba zan kara yarda na ci kwadon kashi da shinkafa ba.

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano

Ɗan Gwamnan Jigawa ya rasu kwana guda bayan rasuwar mahaifiyarsa

Mutum 38 ne suka mutu a haɗarin jirgin sama a Kazakhstan