Illolin koyarwa da harshen Ingilishi maimakon harshen Hausa

  Wannan takarda, an gabatar da ita ne a yayin taron kara wa juna sani na kasa-da-kasa da aka gudanar a Sashen Koyar Da Harsunan Afirka Da Al’adu na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, daga 1 zuwa 3 ga Agusta, 2017. (Wannan ne kashi na biyu kuma na karshen takardar):   Ba tare da dogon bayani […]

Illolin koyarwa da harshen Ingilishi maimakon harshen Hausa

 

Wannan takarda, an gabatar da ita ne a yayin taron kara wa juna sani na kasa-da-kasa da aka gudanar a Sashen Koyar Da Harsunan Afirka Da Al’adu na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, daga 1 zuwa 3 ga Agusta, 2017. (Wannan ne kashi na biyu kuma na karshen takardar):

 

Ba tare da dogon bayani ba za a fahimci cewa kamar inda tsarin harshe na kasa da kuma tsarin ilimi na kasa sun yi rawar gani wajen bayar da dama a koyar da yaro a matakin ilimi a shekarar farko da harshen uwa, domin saukin ganewa.

 

Ingilishi da Harshen Uwa a Gidajenmu:

Nnaji (2001) a bayaninsa, cewa ya yi abubuwan da ke faruwa a makarantu game da wannan matsalar na koyar da yara a makarantun firamare da Ingilishi fiye da na harshen uwa ya zama ruwan dare ba a Arewacin Najeriya ba ne, kawai duk a kasar ne baki daya, sauran harsunan ma su ma haka suke, domin idan aka duba, ya ma wuce inda ake zato. Duk wadannan abubuwa na faruwa a gidajenmu, mu ’yan Najeriya baki daya saboda akasari iyaye su da kansu Ingilishi suke yi a gidajen nasu, sai su ki yin harshen da suka gada, wai su ’ya’yansu dole su rika magana da Ingilishi, yin haka shi ne burgewa da nuna ci gaba a rayuwa. Bugu da kari har ya kai cewa ’yan aikin gidansu su ma komai kauyancinsu su ma sai dai da Ingilishi za su yi magana a gidan, ba sa so sam-sam a yi magana da harshen uwa.

Wannan hali na haifar da koma baya ga bunkasa harshen uwa da kuma hana yara su san asalinsu, wanda ya sa su kansu ’ya’yan ba sa ganin martabar harsunan.

 

Kishin Kai Ko Kishin kasa?

Bargery (1993) ya ba da ma’anar kishin kai da cewa mutum ya tsare ko ya kula da kansa ko kuma kulawa da abin da yake kauna. A kamusun Hausa (2006) kuwa, an ba da ma’anar kishin kasa ne da tsayawa da nuna kwazo kan harshe ko kasar mutum. Akilu Aliyu (1976) a Fasaha Akiliya, cikin wakarsa mai suna ‘Hausa Mai Ban Haushi’ a wasu baitoci da yawa ya ja kunnen jama’a da nuna cewa mutane su yi kishin harshensu, shi ne nasu, kamar haka:

 

Tsuntsu kamata yai da shi ya yi kuka,

Ya irin na kaka nasa can mai nisa.

 

Ku san Bature ba shi kin Turanci,

In ya game da kininsa ko a makasa.

 

Faufau, ba ka ga, ba ka ji mai yare ba,

Ya nuna ki ga kininsa, sai mu Hausa.

 

In har akwai biyu masu jin Turanci,

Kuma ga na ukku cikarsu duk ’yan Hausa.

In kai na ukkun ba ka jin Turanci,

Biyu din na tare da kai sukan kiya Hausa.

 

Tafiya fa tai tafiya, mu lura mu juyo,

An kada mu, mui kokarin shan fansa. 

 

A halin da ake ciki a yau a manyan makarantunmu, za ka samu da dama daga cikin dalibai masu nazarin Hausa, ba sa ma son abokansu su san cewa Hausa suke karantawa. Haka nan a garuruwansu, ba duka iyaye da ’yan uwa ke farin ciki ba, idan aka ce ga wani nasu na karatun Hausa. 

 

Ingilishi da Harshen Uwa a makaranta:

Mba (2010:44) ya ce, da gaske ne kwarai kuma a bayyane yake, mafi yawan makarantunmu a Najeriya, musamman makarantu masu zaman kansu, mawuyacin abu ne ka ga sun amince ko kuma ka ga suna magana da harshen uwa wajen koyar da yara, koda kuwa yara ’yan ajin reno ne. wannan na faruwa ne saboda irin muhimmanci da aka ba harshen Ingilishi a kasar. Don haka sai ka ga cewa shugaba mai makarantar na bayar da umurni ga malaman da su rika amfani da harshen Ingilishi kawai wurin koyar da yaran, wai domin su nuna cewa sun fi sauran makarantu kwarewa da kwazo. Sai ka ga cewa suna nuna wa iyayen yaran cewa ai sun iya koyarwa, domin ga shi nan sun sa yaransu iya harshen Ingilishi, musamman a lokutan bukin yaye dalibai da bikin cikar shekara. A wannan lokaci wakoki da wasanni da labarai da gasa tsakanin dalibai duk da Ingilishi za a yi su, wai shi ne burgewa.

Ajujuwan kuwa doka ne ga duk dalibin da ya yi magana da wani harshe da ba na Ingilishi ba, za a hukunta shi.

 

Ingilishi da Harshen Uwa Tsakanin Manya Masu Ilimi:

Hakika haka zancen yake, a cewar Rizbi (2009), idan aka duba da kyau za a ga kamar yadda yake faruwa a makarantu ko a waje cikin garuruwa da unguwanni ma harshen Ingilishi ya mamaye harshen uwa a tsakanin manya, iyaye masu ilimin zamani. Akwai alamun cewa harshen Ingilishi ya samu wannan tagomashi sosai ga ’yan Najeriya, a duk tarurruka da za ka ga an shirya, walau Hausawa ne ko Inyamurai ko Yarabawa, sai ka ga ana saka Ingilishi cikin bayanan ana gamade ko kuma ana rabi da rabi, wato a yi magana da harshen uwa can kuma sai a koma a sako Ingilishi. Abin nufi a nan shi ne, wai yin haka zai sa a ce mutum ya burge, kar a yi masa kallon bai waye ba ko kar a dauke shi bai san komi ba. Amma kuma irin wannan hali, mafi yawa yana faruwa ne ga wadanda ba su girma a cikin gida ba ne, sai kasashen waje da kuma irin wadanda iyayensu ba sa koya masu harshen nasu saboda ba kishin harshen uwa.

 

Illar Fifita Harshen Ingilishi:

Wannan abu na nuni da rashin tsaro ga harshen uwa, idan ba a kiyaye ba; haka kuma idan ba a amfani da harshen uwa a gidajen sosai ga yara, masu harshen ba su dama su rika yi a wuraren tarukansu ba. Haka dai kuma idan mutane ba su alfahari da harsunan uwa, zai zamo hatsari da ban tsoro nan gaba, wanda zai sa fargaba da koma baya ga harshen uwa. In dai aka bari haka na faruwa, to lallai ba shakka wadannan harsunan uwa na Najeriya za su rasa matsayinsu da al’adunsu na gado. Har wa yau, a haka da muke ciki, wadansu Hausawan ko Inyamuran ko Yarabawan, ba sa iya karatu da rubutu da harshensu na uwa, sai kame-kame (Okafor, 2010:501).

 

Shawarwari:

Don tabbatar da kula da kiyaye wannan harshen uwa da muke da su, dole ne mu mike da yunkurin da ya dace wajen kare muradun harsunan kamar haka: 1-Dole ne masu ruwa da tsaki da kuma masu makarantu masu zaman kansu a kasa da su maida hankali kan tsarin ilimi na kasa. 2-Gwamnatin Tarayya ta rika kula da irin wadannan dokoki da take kafawa, ta hanyar bibiya da kafa kwamitocin da za su rika tsawatar wa makarantu don cin ma wannan buri. 3-Ya kamata a mike da dagewa wajen yin kamfe a wurare kamar su ofisoshin ma’aikatun gwamnati da kasuwanni da makarantu, domin jawo hankalin mutane kan amfani da harsunan, cewa a kodayaushe cikin al’amuransu na yau da kullum. 4-Iyaye kuma ya zama wajibi a gare su da su rika amfani da harshen uwa a gidajensu, suna koyar da ’ya’yansu don su taso da harshen asalinsu, su san tarihinsu cikakke.

 

Kammalawa:

Ganin cewa irin fifikon da aka ba harshen Ingilishi fiye da harsunan Najeriya wanda su ’yan Najeriya suka bayar da wannan dama da kansu, kuskure ne sosai, domin ba wani harshe da ya fi wani.

Wannan tunatarwa ce ga dukkan mai kishin Hausa da ya tuna a baya can, Turawa su suka jagoranci yin rubuce-rubuce cikin harshen Hausa da har gobe ana alfahari da su kuma wadannan rubuce-rubuce sun jawo wa Turawan suna da daukaka. Amma yanzu ga shi Hausawan sun yi sake kuma a wannan zamanin idan har ba ka ‘busa kahonka ba, to babu mai busa maka.’

Musa Abdullahi, malami ne a sashen koyar da Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau, Jihar Zamfara.