Illolin koyarwa da harshen Ingilishi maimakon harshen Hausa

Wannan takarda, an gabatar da ita ne a yayin taron kara wa juna sani na kasa-da-kasa da aka gudanar a Sashen Koyar Da Harsunan Afirka Da Al’adu na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, daga 1 zuwa 3 ga Agusta, 2017. Tsakure: Harshen mama (uwa), shi ne harshen iyayen yara, kamar yadda masana suka fada, shi ne […]

Illolin koyarwa da harshen Ingilishi maimakon harshen Hausa

Wannan takarda, an gabatar da ita ne a yayin taron kara wa juna sani na kasa-da-kasa da aka gudanar a Sashen Koyar Da Harsunan Afirka Da Al’adu na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, daga 1 zuwa 3 ga Agusta, 2017.

Tsakure: Harshen mama (uwa), shi ne harshen iyayen yara, kamar yadda masana suka fada, shi ne tushen koyon ilimi, musamman a matakin ilimi na farko, wanda yake a halin yanzu ya koma baya bisa ga harshen Ingilishi. Haka kuma a yanzu, a bayyane yake, makarantun renon yara da firamare, mawuyaci ne ka ga sun yi amfani da harsunan mama wajen harkokin koyarwa. Bugu da kari, a wasu makarantun akan ladabtar da yara idan suka yi magana da harshen mama, wanda ya hada da duka da tozartarwa ko kuma biyan tara na kudi. Su ma iyaye ba a bar su a baya ba wajen fifita bakon harshe, wanda ke hana yara maida hankali wajen koyon harshensu. Don haka wannan sakaci ne da Gwamnatin Tarayya ke nunawa wajen rashin ba da karfi ga harshen mama, kamar yadda ya fito cikin tsarin ilimin kasa, ya yarda da amfani da harshen mama. Wannan takarda za ta mai da hankali ne ga yin tsokaci a kan fifita harshen Ingilishi da ake yi bisa ga harshen mama da malamai ke nunawa. Bugu da kari, za a binciko adadin illolin da harshen mama ke fuskanta a hannun masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.

Gabatarwa: Ba wanda ke kokwanton amfanin harshen Ingilishi a Najeriya a matsayin harshen sadarwa ta mu’amala a tsakanin mutane da ba da umurni da kasuwanci da dai sauran harkoki tsakanin mutane a kasar. Duk da haka dai, masu gudanar da harkar mulki ta bangaren ilimi da iyaye sun nuna shakuwarsu da karfafa wannan harshe na Ingilishi wajen amfani da shi. Amma kuma an assasa cewa a kundin tsarin ilimi na kasa (2004) ta yi la’akari da alfanun da ke tattare da harsunan Najeriya, domin haka aka wajabta wa kowane yaro a makarantun firamare da na gaba da firamare da ya yi kokarin koyon daya daga cikin wadannan manyan harsuna guda uku da gwamnati ta amince da su, wato Hausa da Ibo da Yarabanci. Wannan abu da gwamnati ta yi bai sa iyayen yara da malamai da su kansu yaran karbar wannan tsari hannu biyu ba, wato abin nufi a nan, sun yi watsi da dokar da gwamnatin kasa ta kafa na daraja harshen mama. Harshen Hausa na daga cikin manyan harsunan iyalan Chadi. Yana daga cikin manyan harsunan da Afirka ke bugun gaba da su ga kowane misali na martabar harshe, ya yi wa sauran harsuna babakere a Afirka ta yamma. Ya kuma yi wa sauran takwarorinsa fintinkau a cikin gida Najeriya, (Bunza, 2013:3). Dadin dadawa (Amfani, 2012) ya yi bayanin cewa, a kididdigar masana, akwai mutane kimanin miliyan hamsin Hausawa da wadanda suke jin Hausa. Kuma Hausawan nan sun kai Hausar wurare daban-daban irin su kasashen Ghana da Togo da Benin da Kamaru da Chadi da Sudan da Mali da sauransu. Ya kuma ci gaba da bayanin cewa, mahankalta na ganin cewa a da Hausawa sun yi rayuwa mai ma’ana. Harshen Hausa kuma yana cike da azanci da hikima. Amma kuma yau wannan harshe na fuskantar barazana da kalubale, sakamakon sauyin zamani, wanda ka iya jawo wa harshen koma-baya ko ma ya rasa shi. Sakamakon haka ne a yau ake da bukatar kara matsa kaimi wajen ganin ana amfani da Hausa sosai da sosai, a kuma duk inda ya dace a yi amfani da ita, ya zama tilas Hausawa su yi kishin Hausa in har suna so ta kara tsawon rai, ta kuma tsira daga sauyin zamani.

A dalilin haka ne wannan takarda za ta yi tsokaci kan amfanin harshen mama (uwa), Ingilishi da harshen uwa a makarantu, Ingilishi da harshen uwa a gida, kishin kai ko kishin kasa, Ingilishi da harshen uwa a tsakanin magidanta masu ilimi, illar fifita harshen Ingilishi, shawarwari da kuma kammalawa.

Amfanin Harshen Mama (Uwa): Amfanin harshen uwa ba zai misaltu ba ta kowane bangare a rayuwar dan Adam, sai kawai a fadi iya abin da aka dan sani. Alal misali, ta fagen harkar ilimi da rayuwar yau da kullum na cinikayya da kasuwanci da kuma nuna al’adun dan Adam. Sanin kowa ne cewa harshen uwa na taskace al’adu da dabi’u ga al’ummar wannan harshen; yaro ba ya sakewa ko jin dadin walwala idan ba irin al’adun yake ciki ba, ta inda zai amfani da harshen uwa wanda ya taso da shi tun farkon rayuwarsa. Olugbeko da Adepoju (2010) a cewarsu, sun yarda dari bisa dari game da wannan ra’ayi, domin duk yaron da ya taso da al’adun dabi’un harshen uwa za ka ga yana da kiyayewa da kokarin jajircewa wajen kare al’adun da kuma yada su, duk yin haka bai yiwuwa sai da harshen uwa. Haka kuma sun ce yaro ya fi samun tunani da natsuwa sosai da kuma fahimtar duka darussan da za a koyar da shi. “Idan har harshen da za a koyar da karatun a firamare da harshen uwa ne.”

Chumbow (2004:61) cewa ya yi da wannan bayani da masana suka ce a yi amfani da harshen uwa wajen koyar da karatu daga firamare har zuwa aji uku na karamar sakandare, inda ya ce kamar haka:

“Inda ake ganin cewa tunani da wayewa na al’adu da basira suna da muhimmanci wajen harshe ga dan Adam, wanda yake nuni da cewa irin haka ana samun shi ne kawai a harshen uwa, wanda yake shi ne harshen farko da yaro ya koya ya kuma taso a ciki. Wannan kan ba yaro damar bayyana fahimtarsa da basirar da yake dauke da ita, da kuma bayanin sanin da yake da shi a cikin duniya. Haka kan sanya yaro kwarewa kuma tunaninsa ya zamo yana dacewa da al’adunsa.”

Ya kara da cewa amfani da harshen uwa a shekarun farko a makaranta na kara kaifin bunkasar kwarewar yaro. Masana sun yarda cewa koyar da yaro a hankali da harshen uwa zuwa wani harshe na biyu, misali, harshen Ingilishi ya fi saurin a ce tashi daya a juye a fara da Ingilishi nan take daga shiga makaranta.

(Za a kammala makon gobe in sha Allah).

Musa Abdullahi, malami ne a sashen koyar da Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau, Jihar Zamfara.