Illolin koyarwa da Ingilishi maimakon Hausa
Wannan takarda, an gabatar da ita ce a yayin taron kara wa juna sani na kasa-da-kasa da aka gudanar a Sashen Koyar da Harsunan Afirka da Al’adu na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, daga 1 zuwa 3 ga Agusta, 2017. Tsakure: Harshen uwa, shi ne harshen iyayen yara, kamar yadda masana suka fada, shi ne […]
Wannan takarda, an gabatar da ita ce a yayin taron kara wa juna sani na kasa-da-kasa da aka gudanar a Sashen Koyar da Harsunan Afirka da Al’adu na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, daga 1 zuwa 3 ga Agusta, 2017.
Tsakure: Harshen uwa, shi ne harshen iyayen yara, kamar yadda masana suka fada, shi ne tushen koyon ilimi, musamman a matakin ilimi na farko, wanda yake a halin yanzu ya koma baya bisa (dogaro) ga harshen Ingilishi. Haka kuma a bayyane yake, makarantun rainon yara da firamare, mawuyaci ne ka ga sun yi amfani da harsunan mama wajen harkokin koyarwa. Bugu da kari, a wasu makarantun akan ladabtar da yara idan suka yi magana da harshen uwa, wanda ya hada da duka da tozartarwa ko kuma biyan tara na kudi. Su ma iyaye ba a bar su a baya ba wajen fifita bakon harshe, wanda ke hana yara mai da hankali wajen koyon harshensu. Don haka wannan sakaci ne da Gwamnatin Tarayya ke nunawa wajen rashin ba da karfi ga harshen uwa, kamar yadda ya fito cikin tsarin ilimi na kasa, wanda ya yarda da amfani da harshen uwa. Wannan takarda za ta mai da hankali ne ga yin tsokaci a kan fifita harshen Ingilishi da ake yi a kan harshen uwa da malamai ke nunawa. Bugu da kari, za a binciko adadin illolin da harshen uwa ke fuskanta a hannun masu ruwa- da-tsaki a harkar ilimi.
Gabatarwa: Ba wanda ke kokwanton amfanin harshen Ingilishi a Najeriya a matsayin harshen sadarwa na mu’amala a tsakanin mutane da ba da umarni da kasuwanci da sauran harkoki tsakanin mutane a kasar nan. Duk da haka dai, masu gudanar da harkar mulki a bangaren ilimi da iyaye sun nuna shakuwarsu da karfafa wannan harshe na Ingilishi wajen amfani da shi. Amma kuma an assasa cewa a kundin tsarin ilimi na kasa (2004) ya yi la’akari da alfanun da ke tattare da harsunan Najeriya, domin haka aka wajabta wa kowane yaro a makarantun firamare da na gaba da firamare ya yi kokarin koyon daya daga cikin wadannan manyan harsuna guda uku da gwamnati ta amince da su, wato Hausa da Ibo da Yarabanci. Wannan abu da gwamnati ta yi bai sa iyayen yara da malamai da su kansu yaran karbar wannan tsari hannu biyu ba, wato abin nufi a nan, sun yi watsi da dokar da gwamnatin kasa ta kafa na daraja harshen uwa. Harshen Hausa na daga cikin manyan harsunan iyalan Chadi. Yana daga cikin manyan harsunan da Afirka ke bugun gaba da su ga kowane misali na martabar harshe, ya yi wa sauran harsuna babakere a Afirka ta Yamma. Ya kuma yi wa sauran takwarorinsa fintinkau a cikin gida Najeriya. (Bunza, 2013:3). Dadin dadawa (Amfani, 2012) ya yi bayanin cewa, a kididdigar masana, akwai mutane kimanin miliyan 50 Hausawa da wadanda suke jin Hausa. Kuma Hausawan nan sun kai Hausar wurare daban-daban irin su kasashen Ghana da Togo da Benin da Kamaru da Chadi da Sudan da Mali da sauransu. Ya kuma ci gaba da bayanin cewa, mahankalta na ganin cewa a da Hausawa sun yi rayuwa mai ma’ana. Harshen Hausa kuma yana cike da azanci da hikima. Amma kuma yau wannan harshe na fuskantar barazana da kalubale, sakamakon sauyin zamani, wanda ka iya jawo wa harshen koma-baya ko ma ya rasa shi. Sakamakon haka ne a yau ake da bukatar kara matsa kaimi wajen ganin ana amfani da Hausa sosai da sosai a kuma duk inda ya dace a yi amfani da ita. Ya zama tilas Hausawa su yi kishin Hausa in har suna so ta kara tsawon rai, ta kuma tsira daga sauyin zamani.
A dalilin haka ne wannan takarda za ta yi tsokaci kan amfanin harshen uwa, Ingilishi da harshen uwa a makarantu, Ingilishi da harshen uwa a gida, kishin kai ko kishin kasa, Ingilishi da harshen uwa a tsakanin magidanta masu ilimi, illar fifita harshen Ingilishi, shawarwari da kuma kammalawa.
Amfanin Harshen Uwa: Amfanin harshen uwa ba zai misaltu ba ta kowane bangare a rayuwar dan Adam, sai kawai a fadi iya abin da aka dan sani. Alal misali, ta fagen harkar ilimi da rayuwar yau da kullum na cinikayya da kasuwanci da kuma nuna al’adun dan Adam, sanin kowa ne cewa harshen uwa na taskace al’adu da dabi’u ga al’ummar wannan harshe; yaro ba ya sakewa ko jin dadin walwala idan ba irin al’adun yake ciki ba, ta inda zai yi amfani da harshen uwa wanda ya taso da shi tun farkon rayuwarsa. Olugbeko da Adepoju (2010) a cewarsu, sun yarda dari bisa dari game da wannan ra’ayi, domin duk yaron da ya taso da al’adun dabi’un harshen uwa za ka ga yana da kiyayewa da kokarin jajircewa wajen kare al’adun da kuma yada su, duk yin haka bai yiwuwa sai da harshen uwa. Haka kuma sun ce yaro ya fi samun tunani da natsuwa sosai da kuma fahimtar dukan darussan da za a koyar da shi. “Idan har harshen da za a koyar da karatun a firamare da harshen uwa ne.”
Chumbow (2004:61) cewa ya yi da wannan bayani da masana suka ce a yi amfani da harshen uwa wajen koyar da karatu daga firamare har zuwa aji uku na karamar sakandare, inda ya ce kamar haka:
“Inda ake ganin cewa tunani da wayewa na al’adu da basira suna da muhimmanci wajen harshe ga dan Adam, wanda yake nuni da cewa irin haka ana samun sa ne kawai a harshen uwa, wanda yake shi ne harshen farko da yaro ya koya ya kuma taso a ciki. Wannan kan ba yaro damar bayyana fahimtarsa da basirar da yake dauke da ita da kuma bayanin sanin da yake da shi a cikin duniya. Haka kan sanya yaro kwarewa kuma tunaninsa ya zamo yana dacewa da al’adunsa.”
Ya kara da cewa amfani da harshen uwa a shekarun farko a makaranta na kara kaifin bunkasar kwarewar yaro. Masana sun yarda cewa koyar da yaro a hankali da harshen uwa zuwa wani harshe na biyu, misali, harshen Ingilishi ya fi saurin a ce tashi daya a juye a fara da Ingilishi nan take daga shiga makaranta.
Ba tare da dogon bayani ba za a fahimci cewa tsarin harshe na kasa da tsarin ilimi na kasa sun yi rawar gani wajen bayar da dama a koyar da yaro a matakin ilimi a shekarar farko da harshen uwa, domin saukin ganewa.
Ingilishi da Harshen Uwa a gidajenmu:
Nnaji (2001) a bayaninsa, cewa ya yi abubuwan da suke faruwa a makarantu game da wannan matsala ta koyar da yara a makarantun firamare da Ingilishi fiye da harshen uwa ya zama ruwan dare ba a Arewacin Najeriya ba ne, kawai duk a kasar ce baki daya, sauran harsunan ma su ma haka suke, domin idan aka duba, ya ma wuce inda ake zato. Duk wadannan abubuwa na faruwa a gidajenmu, mu ’yan Najeriya baki daya saboda akasari iyaye su da kansu Ingilishi suke yi a gidajensu, sai su ki yin harshen da suka gada, wai su ’ya’yansu dole su rika magana da Ingilishi, yin haka shi ne burgewa da nuna ci gaba a rayuwa.
Bugu da kari har ya kai cewa ’yan aikin gidansu su ma komai kauyancinsu su sai dai da Ingilishi za su yi magana a gidan, ba sa so sam-sam a yi magana da harshen uwa. Wannan hali na haifar da koma baya ga bunkasa harshen uwa da kuma hana yara su san asalinsu, wanda ya sa su kansu ’ya’yan ba sa ganin martabar harsunan.
Kishin kai ko kishin kasa?
Bargery (1993) ya ba da ma’anar kishin kai da cewa mutum ya tsare ko ya kula da kansa ko kuma kulawa da abin da yake kauna. A Kamusun Hausa (2006) kuwa, an ba da ma’anar kishin kasa ne da tsayawa da nuna kwazo kan harshe ko kasar mutum. Akilu Aliyu (1976) a Fasaha Akiliya, cikin wakarsa mai suna ‘Hausa Mai Ban Haushi’ a wasu baitoci da yawa ya ja kunnen jama’a da nuna cewa mutane su yi kishin harshensu, shi ne nasu, kamar haka:
Tsuntsu kamata yai da shi ya yi kuka,
Ya irin na kaka nasa can mai nisa.
Ku san Bature ba shi kin Turanci,
In ya game da kininsa ko a makasa.
Faufau, ba ka ga, ba ka ji mai yare ba,
Ya nuna ki ga kininsa, sai mu Hausa.
In har akwai biyu masu jin Turanci,
Kuma ga na ukku cikarsu duk ’yan Hausa.
In kai na ukkun ba ka jin Turanci,
Biyu din na tare da kai sukan kiya Hausa.
Tafiya fa tai tafiya, mu lura mu juyo,
An kada mu, mui kokarin shan fansa.
A halin da ake ciki a yau a manyan makarantunmu, za ka samu da dama daga cikin dalibai masu nazarin Hausa, ba sa ma son abokansu su san cewa Hausa suke karantawa. Haka nan a garuruwansu, ba duka iyaye da ’yan uwa ke farin ciki ba, idan aka ce ga wani nasu na karatun Hausa.
Ingilishi da Harshen Uwa a makaranta:
Mba (2010:44) ya ce, da gaske ne kwarai kuma a bayyane yake, mafi yawan makarantunmu a Najeriya, musamman makarantu masu zaman kansu, mawuyacin abu ne ka ga sun amince ko ka ga suna magana da harshen uwa wajen koyar da yara, koda kuwa yara ’yan ajin raino ne. Wannan na faruwa ne saboda irin muhimmanci da aka ba harshen Ingilishi a kasar nan. Don haka sai ka ga cewa shugaba mai makarantar na bayar da umarni ga malaman da su rika amfani da harshen Ingilishi kawai wurin koyar da yaran, wai domin su nuna cewa sun fi sauran makarantu kwarewa da kwazo. Sai ka ga cewa suna nuna wa iyayen yaran cewa ai sun iya koyarwa, domin ga shi nan sun sa yaransu iya harshen Ingilishi, musamman a lokutan bikin yaye dalibai da bikin cikar shekara. A wannan lokaci wakoki da wasanni da labarai da gasa tsakanin dalibai duk da Ingilishi za a yi su, wai shi ne burgewa.
Ajujuwan kuwa doka ne ga duk dalibin da ya yi magana da wani harshe da ba na Ingilishi ba, za a hukunta shi.
Ingilishi da Harshen Uwa tsakanin manya masu ilimi:
Hakika haka zancen yake, a cewar Rizbi (2009), idan aka duba da kyau za a ga kamar yadda yake faruwa a makarantu ko a waje cikin garuruwa da unguwanni ma harshen Ingilishi ya mamaye harshen uwa a tsakanin manya, iyaye masu ilimin zamani. Akwai alamun cewa harshen Ingilishi ya samu wannan tagomashi sosai ga ’yan Najeriya, a duk tarurruka da za ka ga an shirya, walau Hausawa ne ko Ibo ko Yarabawa, sai ka ga ana saka Ingilishi cikin bayanan ana gamade ko kuma ana rabi-da-rabi, wato a yi magana da harshen uwa can kuma sai a koma a sako Ingilishi. Abin nufi a nan shi ne, wai yin haka zai sa a ce mutum ya burge, kada a yi masa kallon bai waye ba ko kada a dauke shi bai san komai ba. Amma kuma irin wannan hali, mafi yawa yana faruwa ne ga wadanda ba su girma a cikin gida ba, sai kasashen waje da kuma irin wadanda iyayensu ba sa koya musu harshen nasu saboda ba kishin harshen uwa.
Illar fifita Harshen Ingilishi:
Wannan abu na nuni da rashin tsaro ga harshen uwa, idan ba a kiyaye ba; haka kuma idan ba a amfani da harshen uwa a gidajen sosai ga yara, masu harshen ba su dama su rika yi a wuraren tarurrukansu ba. Haka dai kuma idan mutane ba su alfahari da harsunan uwa, zai zamo hadari da ban tsoro nan gaba, wanda zai sa fargaba da koma baya ga harshen uwa. In dai aka bari haka na faruwa, to lallai ba shakka wadannan harsuna na uwa na Najeriya za su rasa matsayinsu da al’adunsu na gado. Har wa yau, a haka da muke ciki, wadansu Hausawan ko Ibo ko Yarabawan, ba sa iya karatu da rubutu da harshensu na uwa, sai kame-kame (Okafor, 2010:501).
Shawarwari:
Don tabbatar da kula da kiyaye wannan harsunan uwa da muke da su, dole ne mu mike mu yi yunkurin da ya dace wajen kare muradun harsunan kamar haka: 1-Dole ne masu ruwa-da-tsaki da masu makarantu masu zaman kansu a kasa su maida hankali kan tsarin ilimi na kasa. 2-Gwamnatin Tarayya ta rika kula da irin wadannan dokoki da take kafawa, ta hanyar bibiya da kafa kwamitocin da za su rika tsawatar wa makarantu don cimma wannan buri. 3-Ya kamata a mike a dage wajen yin kamfe a wurare kamar su ofisoshin ma’aikatun gwamnati da kasuwanni da makarantu, domin jawo hankalin mutane kan amfani da harsunan, cewa a koyaushe cikin al’amuransu na yau da kullum. 4-Iyaye kuma ya zama wajibi a gare su da su rika amfani da harshen uwa a gidajensu, suna koyar da ’ya’yansu don su taso da harshen asalinsu, su san tarihinsu cikakke.
Kammalawa:
Ganin irin fifikon da aka ba harshen Ingilishi fiye da harsunan Najeriya wanda su ’yan Najeriya suka bayar da wannan dama da kansu, kuskure ne sosai, domin ba wani harshe da ya fi wani.
Wannan tunatarwa ce ga dukan mai kishin Hausa da ya tuna a baya can, Turawa su suka jagoranci yin rubuce-rubuce cikin harshen Hausa da har gobe ana alfahari da su kuma wadannan rubuce-rubuce sun jawo wa Turawan suna da daukaka. Amma yanzu ga shi Hausawan sun yi sake kuma a wannan zamanin idan har ba ka ‘busa kahonka ba, to babu mai busa maka.’
Musa Abdullahi, Malami ne a Sashen Koyar da Harsuna da Al’adu na Jami’ar Tarayya da ke Gusau, Jihar Zamfara.