Illolin leda ga muhallinmu
Leda kan bazu a gari idan iska ta dauko ta, ta bata gari. Daga cikin manyan illolinta su ne, ba ta narkewa, takan dauki sama da shekara dari ba ta narke ba a cikin karkashin kasa kuma idan ma ta narke, sinadaranta na da illa ga dan Adam. Ita tana illa a ayyukan gona ko […]
Leda kan bazu a gari idan iska ta dauko ta, ta bata gari.
Daga cikin manyan illolinta su ne, ba ta narkewa, takan dauki sama da shekara dari ba ta narke ba a cikin karkashin kasa kuma idan ma ta narke, sinadaranta na da illa ga dan Adam. Ita tana illa a ayyukan gona ko gini. Misali, idan tana karkashin kasa, ba ta bari ruwa ya ratsa kasa, sannan manoma ko makiyaya idan dabbobinsu suka ci, tana halaka su.
Toshewar magudanan ruwa na haddasa ambaliya. Leda, abin da kowa yake gani shi ne, yadda take rufe magudanan ruwa. Misali, a kasar Maleshiya, shekara da shekaru suna fama da matsalar ambaliyar ruwa. Hakan kuma na faruwa ne saboda leda. Don haka sai aka yi taron masana muhalli, bayan da suka fitar da rahoto, aka yi amfani da shi; aka samu sauki da kashi hamsin cikin dari.
Idan leda ta yi yawa a muhalli, ko kyan gani ba ya yi, sannan idan da a ce za ta narke, idan aka yi noma a inda take mutane suka ci abincin, zai yi masu illa.
Tsarin mahukunta: Yadda al’umma ke riko kaya cikin leda ba bakon abu ne ba a fadin duniya. Da yawa mahukunta a kasashenmu na Afirka ba su ba tsarin kula da muhalli muhimmanci saboda idan a ce akwai tsari kamar na kasashen da suka ci gaba, inda za ka ga tsarin kula da shara na musamman ne, to da an samu ci gaba. Su kansu al’umma sai sun zama masu bin doka da oda. Sai ka ga mutum da ake ganin mai ilimi ne amma yana tafe yana zubar da shara, wanda kuma bai yi ilimi ba yana bi ya share – Ai wannan abin kunya ne.
Mafita: Na farko, a fitar da tsare-tsare masu muhimmanci game da muhalli. Mutane da ba su bin doka, a hukunta su, sannan a nema wa al’umma makamanciyar irin wadda ake amfani da ita a kasar Japan, wacce ke dauke da wasu sinadarai da ke da wa’adi, muddin wa’adin ya cika, za ta wargaje ne ta bi iska kawai.
Ana iya sanya haraji mai yawa ga kamfanonin ledar don ta yi tsada, yadda al’umma za su rage amfani da ita. Haka kuma ba za ka jefar da ita ba ko’ina ba, kana iya kara amfani da ita. Kudin da aka samu ta siyar da ita ko ta harajin da aka samu daga gare ta, ana iya amfani da su a alkinta muhalli.
Daga Ibrahim Rabilu Tsafe (07064282182)