Illolin shan lemukan kara ‘kuzari’
Bambanci daya ne kawai; ruwan barasa na rage kuzari ya sa maye, su kuma lemukan kara kuzari sukan yi su sa hauka.
Kowa ya san abubuwa na caccanzawa da zamani; To yanzu ma zamani ya zo wanda ya sa ana ta yada tallar lemuka da sunan lemukan kara kuzari wato ‘energy drinks.’
Wadannan lemuka da nake magana a kansu ba giya ba ne kai-tsaye lemuka ne masu sa naci, sun ma fi lemukan da muka sani irin su Coka-Cola da Pepsi sa naci, kuma suna da kamanceceniya da ruwan giya ta hanyoyi da dama, musamman ta bangaren lafiya ta hanyoyin saka sabo da nacin sha (mutum idan ya sha sau daya sai ya ji begen karawa), da lalata sassan jiki irin su hanta da koda da nane-bango wato pancreas da rikita sinadaran da ke aiki a kwakwalwa.
- Gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijirar Najeriya a Nijar
- An zabi ‘yar Najeriya cikin ’yan jaridar duniya da za su samu horo na musamman
Haka nan a kasashen da aka ci gaba, duk da cewa daga nan tabarar ta faro, ba sa sayar wa kowa sai wanda ya mallaki hankalinsa, wato daga shekara 18 abin da ya yi sama, kamar dai yadda ake yi wa barasa (giya).
Bambanci kusan guda daya aka lura da shi tsakanin wannan lemo da ruwan barasa. Wannan kuwa shi ne cewa ruwan barasa na rage kuzari ya sa maye, su kuma lemukan kara kuzari sukan yi su sa hauka.
To a yanzu a al’ummarmu an fara samun mutane masu tu’ammali da wadannan lemukan shaye-shaye wadanda abin ya zame wa alakakai.
Domin suna so su daina sun kasa, yawan shan kuma na ci-gaba da illata wadancan sassan jiki a sannu a sannu ba su sani ba.
Muna tsoron cewa tunda sababbin-shiga ne lemukan, kada nan gaba bayan ’yan shekaru kamar biyar zuwa 10 mu zo muna jin labarin yawan bacin wadannan sassan jiki da ke da alaka da su.
Don haka wannan shafi a yau zai yi kira ga hukumomi da daidaikunmu domin a lura a dakile wannan barna da ba za ta iya haifar mana da mai ido ba.
Alhakin Hukumar Kiyaye Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) ce, ta tsaya kyam ta duba irin dacewar wadannan lemuka a cikin al’umma da sinadaran da ake sa musu.
Ga su nan kamfanoni birjik har da na cikin gida ga su nan kowa lemon kara kuzari yake hadawa yake turowa cikin al’umma domin samun kudi, tunda an riga an sa musu sinadaran ‘in-ka-ci-sai-ka-kara’ wato masu sa naci irin su sinadarin caffeine mai dimbin yawa a ciki.
Ban da wannan sinadari akwai wasu sinadarai masu illa sosai.
Kai a kasashen waje ma har da hodar Iblis an taba gani a irin wadannan lemuka, amma dai nan kasar ba mu ji labarin haka ba.
Kowa kuma ya san irin nacin da hodar Iblis ke sa wa ya ninka na caffeine.
Idan za a ba da misali da irin wannan hoda, a shekarun baya an taba kama wata mata da ke yin wani cincin a Abuja da take sa wa hodar Iblis, har yaran unguwar suka zama idan ba su ci cincin dinta ba, ba sa jin dadi, daga bisani dubun matar ya cika aka garkame ta.
Ga daidaikunmu kuma, yana da kyau mu yi la’akari da wannan bayani mu yi kaffa-kaffa da lemukan kara kuzari, domin a yanzu ga su nan ko’ina.
Idan ma muka ga yaranmu na shan su a tsawatar a kwabe su, domin idan aka riga aka bari suka ratsa kwakwalwarsu, mai iya raba su da shi sai Allah.
Dokta Auwal Bala I-mel: [email protected] Sakon Tes: 08029013880