Illolin yin talla ga ’yan mata  (2)

Nawa aka kasa mata? Nawa ta kawo? Yaushe ta dawo? Wadansu za a ga suna tallar nono ko gyada ko fura ko mangwaro ko goro. Idan ka dauki jarin wata bai wuce Naira 500 ba, kuma sai ta kai kudin gida, ba tare da ta sayar da hajar ba! Sannan a wasu unguwanni akan ja […]

Illolin yin talla ga ’yan mata  (2)

Illolin yin talla ga ’yan mata  (1)

Nawa aka kasa mata? Nawa ta kawo? Yaushe ta dawo? Wadansu za a ga suna tallar nono ko gyada ko fura ko mangwaro ko goro. Idan ka dauki jarin wata bai wuce Naira 500 ba, kuma sai ta kai kudin gida, ba tare da ta sayar da hajar ba! Sannan a wasu unguwanni akan ja irin wadannan ’yan mata zuwa gidajen maza, a yi musu fyade, ko a rika yi musu ciniki a inda ake gine-gine, inda kowane magini sai ya zagaya. Ko ka gan su a gidajen burodi ko tasha ko kasuwa suna bi rumfa-rumfa ko shaguna suna kai abinci!

Sannan a wasu lokuta akan yi abota da su a gidaje masu alfarma, ta  yadda za a yi wa wata madigo sannan a ba ta kudin kayanta, jin dadin haka sai ta rika zuwa yau da gobe abu ya zama jiki, daga nan sai ta kai bala’in kauyensu, inda abin da ake gani a birni ke bulla a kauye. A nan za a ci gaba da tsegumi, tsugunne ba ta kare ba.

Ina malamai, shin idan an yi karatun, an yi aiki da shi? Kuma a nan wane mataki gwamnati ta dauka wajen ganin  kowace yarinya ta yi karatu har zuwa akalla matakin sakandare?

A nan ma sai mutum ya rasa mene ne aikin kungiyoyin mata da masu rajin kare hakkokin bil-Adama da suke kau da kai kan irin wadannnan munanan dabi’u.

An san uba na da damar aurar da ’yarsa, amma ai ’yan uwa da malamai musamman makwabta na iya ba da shawarar a bari har sai ta yi kwari, musamman gudun cuttutuka kamar ciwon yoyon fitsari, ga masifa talauci da kyashi, domin wata tsananin talaucin kan sa ta fita daga kamanninta ta yadda ba wanda zai neme ta, har ta mutu a zawarci.

Sai an sa ido kan yadda mata, musamman dalibai ko mata ’ya’yan talakawa ko wadanda talauci ya daidaita suke tafiyar da rayuwarsu, domin bayanai sun tabbatar da cewa akan yi amfani da damar wajen keta mutuncinsu idan suna neman wasu bukatu a wajen maza a makarantu ko a kungiyance, balle masu zuwa gidajen aikatau a birane ko masu tsallakawa kasashen ketare don ci-rani.

Mafita tana ga gwamnati da malamai. Dole gwamnati ta tsaurara dokoki, musamman kan zamantakewa ta yadda za a rika ba da ingantaccen ilimi kyauta kuma a wajabta ga ’ya mace har zuwa sakandare. A ba masu hazaka sukolashif don zurfafa karatu a cikin gida da waje. Sannan malamai su shiga gaba wajen ba iyaye shawara da kan yadda za a tarbiyyantar da yara da neman aure da yadda zaman auren zai yi armashi.

Buhari Daure, [email protected] Modoji, Katsina.