Illolin zina da luwadi da madigo (2)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai.  Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin manzanni, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), tare da alayensa da sahabbansa.   Bayan haka mun kwana a karshen illa ta 4 daga cikin illolin zina, yau ga ci gaba daga: 5. Zina tana kawo kiyayya da gaba a tsakanin […]

Illolin zina da luwadi da madigo (2)
Illolin zina da luwadi da madigo (2)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai.  Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin manzanni, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), tare da alayensa da sahabbansa.  

Bayan haka mun kwana a karshen illa ta 4 daga cikin illolin zina, yau ga ci gaba daga:

5. Zina tana kawo kiyayya da gaba a tsakanin masu yin ta da sauran mutane. Allah Madaukakin Sarki Yana cire kwarjininsu da girma daga idon mutane, saboda haka ne za ka ga karamin yaro yana fada da sa’an kakansa a wurin neman mata, saboda ba ya kaunarsa, ballantana ya girmama shi.

6. Zina tana jawo rashin amincewa da mai yin ta.  Kowa yana yi masa kallon maha’inci, mayaudari.

7. Zina tana haifar da wari daga jikin mai yin ta. Ba wanda yake jin wannan wari sai mutanen kwarai.

8. Zina tana jawo azaba mai tsanani ga mai yin ta – idan bai tuba ba – a duniya da Lahira.  A duniya jefewa ko bulala da bakuntarwa; a Lahira kuwa makomarsa wuta.  Allah Ya kare mu.

9. Zina tana kawo rugujewar gida da daidaicewar iyali, sannan tana kawo lalacewar tarbiyya.

10. A cikin zina akwai tozartar da dangantaka da sanya cin dukiyar mutane ba da hakki ba, domin kuwa duk dan da aka samu ta hanyar zina, abin da zai gada ba hakkinsa ba ne.

11. Cikin zina akwai kamancecceniya da dabbobi, saboda mazinaci ba ya daukar nauyin abin da zai biyo bayan lalatarsa, kamar yadda dabba ba ruwanta da abin da ke biyo bayan saduwarta da ’yar uwarta, na kula da mai ciki da tufatar da ita da rainon abin da aka haifa da yi masa tarbiyya. Ka ga ke nan mazinata rayuwar dabbobi suke yi. Allah Ya kiyaye mu.

12. Zina tana kawo kisan kai a cikin al’umma. Sau da dama fada kan faru tsakanin masu neman mata a wajen yawon banzarsu; wani ya kashe wani, kamar yadda yawancin yaran da ake yarwa, ko ake kashewa ’ya’yan zina ne. Haka yawancin cikin da ake zubarwa cikin zina ne, wanda duk wannan kisan kai ne da Allah ba Zai kyale wanda ya yi shi ba.

13. Zina tana lalata al’umma, ta ruguza rayuwa gaba daya, ta hanyar samar da ’ya’yan da ba su da tarbiyya, ba sa ganin girman kowa.  Kai, suna jin haushin al’umma, lura da hanyar da suka zo, abin da da dama yakan sa su zamo ’yan daba da fashi da sauran miyagun ayyuka, su bata rayuwarsu, su bata rayuwar al’umma.

14. Yawaitar zina alama ce ta tashin Alkiyama, kamar yadda ya zo a Hadisi, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), yayin da ya ce:  “Ya al’ummar Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam), wallahi babu wani da ya fi Allah kishin a ce yau bawanSa ya yi zina, ko kuma baiwarSa ta yi zina. Ya al’ummar Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) da kun san abin da na sani da kun yi dariya kadan da kun yi kuka da yawa.”  Sannan sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya daga hannunsa sama ya ce, “Ya Ubangiji, na isar,” Buhari ne ya rawaito.

15.  Zina tana jawo fushin Allah da azabarSa ga al’umma. Abdullahi dan Mas’ud (Allah Ya yarda da shi) ) ya ce: “Zina ba za ta bayyana a wata alkarya ba, face wannan alama ce da Allah Ya yi izinin halakar da ita.”

’Yan uwa wadannan kadan ke nan daga cikin abin da zina take haifar wa masu yin ta da sauran al’umma. Allah Madaukakin Sarki Ya kare mu. 

Ma’anar luwadi da hukuncinsa:

Luwadi shi ne: Saduwa da namiji ko mace ta dubura. A kan haka luwadi ya kasu kashi biyu: Babban luwadi, wanda shi ne saduwa da namiji ta duburarsa; karamin luwadi shi ne saduwa da mace ta dubura.  

Hukuncin luwadi: 

Luwadi da dukan nau’o’insa guda biyu haramun ne a Musulunci, saboda ba ya cikin hanyoyin da Allah Ya halatta wa bayinSa su biya bukatarsu daga gare su.

Allah Madaukakin Sarki Ya fadi irin azaba da bala’in da Ya saukar a kan wadanda suke luwadi a surori goma a cikin Alkur’ani: Suratul A’araf, daga aya ta 80; Suratu Hud, aya ta 76; Suratul Hijir, aya ta 58; Ambiya’i, aya ta 73; Furkan, aya ta 28; Shu’ara, aya ta 160; Nnamli, aya ta 54; Ankabut, aya ta 28; Saffati, aya ta 133da kamar, aya ta 33. 

A cikin wadannan ayoyi, za mu ga yadda Ubangiji Ya hada wa mutanen Annabi Lud (Alaihis Salam) azaba da bala’i iri-iri, Ya makantar da su, Ya kife gidajensu, Ya jefe su da duwatsu, Ya jefa su cikin wuta.

Haka nan ya tabbata a cikin Hadisin da Imam Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah suka rawaito, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Duk wanda kuka samu yana aikin mutanen Annabi Lud, ku kashe shi, ku kashe wanda ake yi da shi.”

Sahabbai sun hadu a kan hukuncin wanda duk ya yi luwadi shi ne kisa, sai dai sun yi sabanin yadda za a kashe shi:

• Magana ta farko: Za a kone shi da wuta, wannan shi ne fahimtar Sayyidina Abubakar da Aliyu da Ibnu Zubair da sauransu. (Duba Zadul Ma’ad da Adda’u waddawa’u da Sunan Al-kubra na Baihaki da sauransu).

• Magana ta biyu: Za a jefe shi da duwatsu har ya mutu, ya taba aure ko bai taba ba.  Wannan ita ce fahimtar Sayyidina Umar da Abdullahi dan Abbas da sauransu. (Duba Raudatul Muhibbin na Ibnul kayyim).

• Magana ta uku: Za a samu ginin da ya fi kowane tsawo, a jefo shi daga can, sannan a biyo shi da duwatsu. An rawaito wannan magana daga Abubakar da Abdullahi dan Abbas. Sai ya zamo suna da fahimta biyu ke nan a mas’alar.

• Magana ta hudu: Za a jefo masa katanga. An rawaito wannan magana daga Aliyu bin Abu dalib.

• Magana ta biyar: Za a yi masa hukuncin mazinaci, idan yana da aure, ko ya taba yi sai a jefe shi, in kuma saurayi ne a yi masa bulala. Wannan ita ce fahimtar Abdullahi Ibnu Zubair.

Wadannan su ne maganganun sahabbai da almajiransu a kan hukuncin da za a yi wa mai luwadi. Babu ko shakka, idan muka dubi wadannan maganganu, za mu gane cewa yin luwadi ba karamin laifi ba ne a addinin Musulunci.

Illolin luwadi a cikin al’umma:

Ko tantama babu cewa luwadi ya kunshi dimbin illoli da cutuwa ga mai yin sa da kuma al’ummar da yake rayuwa a cikinsu. Ga kadan daga cikinsu:

1. Luwadi yana jawo wa mai yin sa da al’umma gaba daya fushin Allah da azabarSa. Kamar yadda ya faru ga mutanen Annabi Lud (Alaihis Salam).

2. ’Yan luwadi mabarnata ne, azzalumai, mutanen banza, fasikai, haka Allah Ya siffata su a wasu ayoyi a cikin Alkur’ani Mai girma.

3. Cikin luwadi akwai almubazzaranci, saboda mai luwadi yana kashe dukiyarsa cikin abin Allah Ya haramta, duk kuwa mai sanya dukiyarsa cikin haramun almubazzari ne, almubazzari kuwa dan uwan Shaidan ne, kamar yadda Allah Ya fada.

4. Cikin luwadi akwai fita daga tsarin da Allah Ya halicci mutum a kai, saboda Allah bai halicci namiji don ya sadu da da namiji ba. Ya halicci maza da mata ne don su ji dadi da natsuwa da juna, kamar yadda Ya fada.

5. Mai yin luwadi kazami ne, kazanta mai muni, domin ya sanya tsokarsa a cikin dubura wurin kashi da najasa.

Mu kwana nan.

Za a iya samun Sheikh Muhammadu Rabi’u Umar Rijiyar Lemo, ta Imel: [email protected]