Illolin zina da luwadi da madigo (3)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai.  Tsira da Amincin Allah su tabbata ga mafificin Manzanni, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), tare da alayensa da sahabbansa. Bayan haka, mun kwana a karshen illa ta 5 daga cikin illolin luwadi, yau ga ci gaba daga illa ta: 6. Luwadi yana haifar da munanan cututtuka, […]

Illolin zina da luwadi da madigo (3)
Illolin zina da luwadi da madigo (3)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai.  Tsira da Amincin Allah su tabbata ga mafificin Manzanni, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), tare da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, mun kwana a karshen illa ta 5 daga cikin illolin luwadi, yau ga ci gaba daga illa ta:

6. Luwadi yana haifar da munanan cututtuka, irin su rashin rike bayan gida da kuraje da sanya zuciya ta yi baki wuluk da bacewar basira da kyakkyawan tunani  da rashin kunya da sauransu.

7. Luwadi yana kawo kaskanci da wulakanci da tozarta, a duniya da Lahira.

8. Saduwa da mace ta dubura mummunan abu ne, wanda Ibnul kayyim – Allah Ya yi masa rahama – yake cewa, “Ba a taba halatta saduwa da mace ta dubura a harshen wani Annabi da Allah Ya aiko ba.”

9. Mai luwadi bai kai darajar dabbobi ba, saboda dabba ma ba ta haka.

10. Mai luwadi – in bai tuba ba – ba ya rabuwa da duniya lafiya, ko dai Allah Ya tozarta shi, kowa ya san aikinsa, ya wayi gari ba ya da mutunci a idon duniya gaba daya, ko kuma Allah Ya jefa masa wata mummunar cuta da zai rika fatar ya mutu kowa ya huta, saboda muninta. Allah Ya kiyashe mu.

Madigo da hukuncinsa:

Madigo shi ne mace ta biya bukatarta da mace, ta hanyar rungumar juna da hada gaba da sauransu.

Madigo haramun ne a addinin Musulunci. Malamai sun sanya shi daga cikin manya-manyan zunubai. Sai dai shari’a ba ta ayyana wani hukunci zaunanne da za a yi wa masu madigo ba. Alkali ne zai duba me ya dace ya yi musu na hukunci, bulala ko dauri ko kora ko tozartawa, ko kuma a hada musu duka. Duk dai hukuncin da alkali ya yanke na razanarwa da tsoratarwa ya yi.  (Duba Almausu’atul Fikihiyyatul Kuwaitiyya da Almugniy na Ibnu kudama).

Illolin madigo:

Madigo, kamar sauran abubuwan da suka gabata ne (yana da illa) wajen haifar da cututtuka da bala’i da masifa ga mai yin sa. Ga kadan daga cikinsu:

1. Madigo fita ne daga dabi’ar da Allah Ya halicci mace a kanta, ta jin dadi da da namiji ba mace ’yar uwarta ba.

2. Cikin Madigo akwai rashin kunya da fitsara, alhali Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Kunya alheri ce gaba dayanta.” A wata ruwaya: “Kunya ba ta kawo komai sai alheri.” Buhari ne ya rawaito.

3. Madigo yakan haifar da cututtukan zamani. Wani bincike da aka gabatar, ya tabbatar da za a iya daukar cutar kanjamau ta hanyar madigo, idan aka yi da wadda take dauke da ita, kamar yadda za a iya samun ciki ta hanyar madigo, idan mace ta yi da wadda ba ta dade da saduwa da namiji ba. Haka likitoci sun tabbatar da madigo yana iya jawo rashin haihuwa.

4. Ana iya rasa budurci ta hanyar madigo, wanda hakan ba karamin tozarta ba ce ga budurwa ta rasa budurcinta kafin ta yi aure.

5. Mai madigo takan rayu cikin kuncin zuciya da kunarta, saboda Allah zai debe mata natsuwa a tare da ita, Ya maye gurbinta da kunci da damuwa. Wata budurwa ’yar shekara ashirin tana ba da labarin irin yadda ta samu kanta cikin damuwa da bala’i bayan rabuwarta da abokiyar madigonta. Tana cewa: “Na kasance budurwa ’yar shekara ashirin, ina son wata kawata sosai tsawon wasu shekaru masu yawa, har dai muka fara madigo a tsakaninmu. Ta shiga raina matuka, na zamo duk abin da take so shi nake yi, har ma ya zamana wani lokaci ana samun sabani a tsakanina da ita idan na ga wani ko wata suna kaunarta, saboda yadda nake kishinta. Wata rana sai wannan kawar tawa ta yi aure, abubuwa suka canja, ta ce dole ne mu rabu. Haka muka rabu, ni kuma na shiga wani hali na jin zafi da radadi a jikina da zuciyata! Ciwon kai, ciwon idanu, ciwon jiki, na je wajen likitoci amma ban samu wata waraka ba, wayyo! Ni yanzu yaya zan yi, ga shi na tuba, amma fa ina so in koma wajenta, yaya zan yi? Wannan kadan ke nan daga illar madigo.

6. Madigo yakan hana ’ya mace zaman aure, domin duk wadda ta saba da shi, zai yi wahala ta rabu da shi, wanda wannan zai sa ta kasa wadatuwa da mijinta, sai ta rika fita tana yi, har idan Allah Ya tona asirinta, mijinta ya sake ta, saki na wulakanci, ko kuma ta nemi saki da kanta ta je ta ci gaba da madigonta. Don haka: “Maganin yaya za a yi, (shi ne) kada a fara.”

7. Mai madigo ba ta karewa da duniya lafiya, ko dai tozarta a duniya, ko kuma haduwa da mummunar cuta da bala’in da ba a warkewa, sai dai kabari!

8. Madigo dabbanci ne! Kai! Dabba ma ta fi ’yar madigo.

9. Cikin madigo akwai cin amanar Allah Mahalicci, saboda an aikata abin da Ya hana, haka kuma akwai cin amanar iyaye ko miji.

10. Haduwa da azabar Allah a Lahira, idan ba a tuba ba.

Wannan kadan ke nan daga cikin illolin da madigo yake haifar wa masu yin sa. Allah Madaukakin Sarki Ya kare mu.

Hanyoyin kare kai daga zina da luwadi da madigo:

Saboda hikimar Ubangiji da rahamarSa, duk abin da Ya haramta wa bayi, to za a bude wata kofar da mutum zai biya bukatarsa ba tare da ya auka wa wancan abin da Allah Ya hana din ba. Wannan abu haka yake a nan ma, domin dai mun ji irin tarin illolin da suke tattare da yin zina da luwadi da madigo, to amma babu yadda namiji ko mace za su rayu ba tare da sun samu inda za su zubar da sha’awarsu idan ta taso ba, saboda haka sai Musulunci ya halatta wadannan abubuwa masu zuwa don kauce wa aukawa cikin zina:

1. Aure:Allah Madaukakin Sarki Ya halatta wa maza su auri mata, inda yake cewa: “Ku auri abin da kuke so na mata, bibbiyu (ko) uku-uku (ko) hurhudu. Idan kuwa kuna tsoron ba za ku iya adalci ba, to ku auri daya, ko kuma abin da damarku ta mallaka. Wannan shi ne abin da zai sa ba za ku karkace ba.” (Nisa’i: 3).

Manzon Allah (Sallallahu  Alaihi Wasallam) kuma yana cewa, “Ya ku taron samari! Duk wanda ya samu iko (ma’ana zai iya rike mace) to ya yi aure, domin shi ne mafi kyan abin da yake sa runtse ido, kuma mafi sa a tsare farji. Duk kuwa wanda bai samu iko ba, to ya yi azumi, domin (shi azumi) kariya ne a gare shi.” Buhari da Muslim.

Wannan aya da Hadisi suna nuna mana halaccin mutum ya yi aure, kuma ya auri matar da yake so, wadda ta kwanta masa a rai, matukar ba ta cikin wadanda Allah Ya haramta masa ya aura. Saboda haka da mazinata da ’yan luwadi da masu madigo za su yi tunani da sun ga yadda Musulunci ya sauwake musu hanya, ta hanyar su yi aure, sai ya zamo duk abin da za su yi halal ne, in ma sun yi niyya Allah Ya ba su lada, kamar yadda Hadisi ya nuna.

Za a iya samun Sheikh Muhammadu Rabi’u Umar Rijiyar Lemo,  Kano ta:

Imel:[email protected]