Imanin Musulmi ba zai cika ba sai ya karɓi kowacce ƙaddara — Sarki Sanusi II

Dole ne mu yi imani cewa duk abin da muka samu ƙaddarawar Allah ce.

Imanin Musulmi ba zai cika ba sai ya karɓi kowacce ƙaddara — Sarki Sanusi II

Sarki Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa kowane musulmi imaninsa yana cika ne idan ya rungumi kowace irin ƙaddara da ta same shi.

Sarkin ya faɗi haka ne a cikin huɗubar sallar Juma’a da ya gabatar a Babban Masallacin Kano da ke Birnin Dabo.

Huɗubar Sarkin ta mayar da hankali ne kan ƙaddara mai kyau ko mara kyau.

A cewarsa, “duk wanda ya yarda cewa Allah ne kaɗai Yake bayarwa, saboda haka dole ne a yarda da duk wani hukunci da Allah Ya tabbatar. Kuma babu mai ikon neman dalili daga wurin Allah a kan kowane irin hukunci naSa.

“Mun sani cewa imanin kowane musulmi ba ya cika har sai ya rungumi kowacce ƙaddara da Allah Ya rubuta a kansa.

“Saboda haka ya zama wajibi mutum ya kasance mai godiya ga Allah kan kowacce ƙaddara mai kyau ko saɓanin haka.

“Dole ne mu yi imani cewa duk abin da muka samu ƙaddarawar Allah ce kuma duk abin da ya suɓuce mana daga wurinSa ne.

“A yanzu muna dosar watan Zhul Hijja wanda saboda falalarsa yana da muhimmanci mu dage da addu’o’i a cikin waɗannan kwanaki.”

“Watan babbar sallah na ƙara tunkarowa wanda kuma yana da matuƙar muhimmanci, ya kamata mu mayar da hankali wajen addu’o’i a kwanakin,” in ji Sarki Sanusi.

Huɗubar Sarki Sanusi II na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da dambarwa kan kujerar sarautar Kano tsakaninsa da Sarki Aminu Ado Bayero wanda Gwamnatin Kano ta tuɓewa rawani.