IMF ta nemi Najeriya ta janye tallafin wutar lantarki

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya bukaci gwamnatin Najeriya ta dakatar da bayar da tallafin wutar lantarki. Rahoton IMF ya kuma bukaci kasar ta daina bayar da tallafin na man fetur gaba daya a farkon shekarar 22. Mun dora daga inda Ali Kwara ya tsaya —Halifansa Dalibar da aka yi wa sharrin safarar kwayoyi zuwa […]

IMF ta nemi Najeriya ta janye tallafin wutar lantarki

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya bukaci gwamnatin Najeriya ta dakatar da bayar da tallafin wutar lantarki.

Rahoton IMF ya kuma bukaci kasar ta daina bayar da tallafin na man fetur gaba daya a farkon shekarar 22.

Bayan binciken da jami’anta suka gudanar a Najeriya, IMF ta ce janye tallafin wutar lantarki da man fetur, abu ne da ya kamata a ba shi muhimmanci matuka a tsare-tsaren kudin kasar.

IMF ya kuma yi kira da a yi gyare-gyare ga tsarin kasuwanci, canji kudi da shugabanci a Najeriya domin magance tafiyar hawainiyar gwamanti wajen samar da ci gaban kasar.

Ya kuma bukaci ta bullo da tsare-tsare da za su magance mummunar tasirin janye tallafin a kan talakawa da rage ciyo bashi.