“In dai Buhari zai sake tsayawa takara zan ajiye mukamina”

Ministan Harkokin Mata, Hajiya Jummai Alhasan ta ce  za ta ajiye mukaminta muddin Shugaba Buhari zai sake tsayawa takara tare da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakara a zabe mai zuwa. Hajiya Jummai ta yi furucin ne a wata ganawa da ta yi da gidan rediyon BBC a yau inda ta ce ba za ta yi […]

“In dai Buhari zai sake tsayawa takara zan ajiye mukamina”

Ministan Harkokin Mata, Hajiya Jummai Alhasan ta ce  za ta ajiye mukaminta muddin Shugaba Buhari zai sake tsayawa takara tare da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakara a zabe mai zuwa.
Hajiya Jummai ta yi furucin ne a wata ganawa da ta yi da gidan rediyon BBC a yau inda ta ce ba za ta yi wa uban dakinta Atiku butulci ba.
“Idan har Baba ya ce zai tsayawa zabe wallahi tallahi zan je gabansa na durkusa na ce na gode da damar da ya bani na yi aiki a karkashinka a matsayin minista amma zan ce masa Atiku uban dakina ne a siyasa”.
Ta bayyana cewa babu yadda za a yi ta ci gaba da zama a cikin gwamnatin Buhari mudddin Atiku ya nuna sha’awarsa na yin takara.
Ta bayyana cewa ita ba maci amana ce ba ce saboda haka ba za ta taba cin amanar Atiku Abubakar ba.
Ta dora alhakin yada bidiyonta a kafafen sada zumunta a kan makiyanta da suke son Buhari ya kore ta.
Ta ce makiyanta za su ji kunya saboda tana da yakinin Buhari ba zai kore ta ba tunda ba ta aikita wani laifi ba.
“Ai Baba Buhari ba irinsu ba ne mutum ne mai mutunci wanda ya san ya kamata saboda haka ba na zaton zai kore ni tunda ba wani laifi na yi ba”. Inji ta.
Ta bayyana cewa ko da Buhari ya kore ta ba za ta damu ba tunda ba ta taba zaton zai ba ta mukamin minista ba.