In dai za a yi zabe na gaskiya muna dab da raka Buhari fadar Shugaban kasa – Mamman Nasir
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC reshen Jihar Katsina Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir ya ce in dai za a bari a gudanar da zabe a kuma bar hukumar zabe ta yi aikin ta yadda ya dace to in Allah Ya yarda za su raka Janar Muhammadu Buhari ya karbo takardar shaidar ya ci zaben Shugaban kasa tare […]
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC reshen Jihar Katsina Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir ya ce in dai za a bari a gudanar da zabe a kuma bar hukumar zabe ta yi aikin ta yadda ya dace to in Allah Ya yarda za su raka Janar Muhammadu Buhari ya karbo takardar shaidar ya ci zaben Shugaban kasa tare da raka shi fadar Shugaban kasa a Abuja.
Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gusau fadar Jihar Zamfara, inda ya ce duk inda aka kada kuri’a, to kashi casa’in na APC ne.
Ya kara da cewa bayan an kammala zaben za su raka tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan zuwa kauyensu Otuake da ke Jihar Bayelsa a matsayin wanda ya fadi zabe. “Mu a Katsina ba mu da PDP, kuma ba a kiran Katsina jiha ta PDP, domin a jihar APC ke da sanatoci uku da ’yan majalisa 14 daga cikin 15 take da ’yan majalisar jiha da can an zabo hudu, yanzu wasu cikin PDP sun dawo APC, kuma maganar da ake duk wani mai hikima da mutunci da hankali da jama’a da kima yana nan cikin Jam’iyyar APC,” inji shi. Ya ce wadanda aka baro a PDP daga masu munafurtarta sai makwadaita masu jiran abin da za su samu.
Ya yi kira ga ’yan Jam’iyyar APC a Jihar Katsina su yi hakuri da abin da ake musu, kuma su daina yin fastoci da allunan sanarwa na Jam’iyyar APC, kowane dan jam’iyya ya tada itace ko falwaya a cikin gidansa ya dora mata tsintsiya a sama, “mu ga wane ne zai shiga cikin gidanka ya cire ta don yana adawa da APC,” inji shi.