In-yi-gwanjon-wala-wala

Tun a cikin watannin da suka arce, wato daga Farin-biri zuwa Marisa, Sallau Lado ke ta caccakar Madam In-gwangwaje-in-wala kan yadda ta yi wasa-rai-rai aka tatuke lalitar kasar Haurobiya, inda aka jidi damin Hauro har tiren taliya tirela kofar hanci da zagaye. Irin wannan azargagiyar zargi bai kamata a wancakalar da ita ba, domin wanda […]

In-yi-gwanjon-wala-wala

Tun a cikin watannin da suka arce, wato daga Farin-biri zuwa Marisa, Sallau Lado ke ta caccakar Madam In-gwangwaje-in-wala kan yadda ta yi wasa-rai-rai aka tatuke lalitar kasar Haurobiya, inda aka jidi damin Hauro har tiren taliya tirela kofar hanci da zagaye. Irin wannan azargagiyar zargi bai kamata a wancakalar da ita ba, domin wanda ya bijiro da ita tsohon Gwamna Babban Asusun Haurobiya ne, kuma jami’in koyar da watsattsake da buda agagen littattafai a fannin tsimi da tanadin dukiya ne.

Kafin Farfesa Sallau Lado ya fito da tabargazar mahukunta Haurobiya, musamman ganin yadda Madam ta rike musu kaho suka mayar da lalitar kasa nagge da karsanar tatsa, sai da Masanin Sisi-da-Sisi ya koka kan yadda Mace da zane da mukarrabanta suka wafce dalar Hauron Amurkawa har gashin balama tsayuwa bisa kafa daya da manuniyar kasa, har yanzu shiru ake ji Malam ya ci shirwa.
Masanin Sisi-da-sisi dai Allah Ya tarfa wa garinsa nono, domin takun sakar da suka yi da samarin jaba da ’yan mata gafiya, ta sanya aka raba shi da mukaminsa, amma sai ga shi ya dare bisa karagar Babban Mutum Mai rawani na birnin Dabo. Maimartaba ya yada kwallon mangoro, ya rabu da shawagin kudaje.
Miyagun Haurobiyawa sai wadaka da watandar dukiyar kasar suke yi, don haka ma suke ta fafutikar ganin ko ta halin kaka sai sun kawo wa zabi-sonka cikas, don haka a kullum sai sun kulla wa Farfesa Ja-gaban Zabi-sonka sharri, alhali su suka nada shi.
Madam In-gwangwaje-in-wala da Mace da-zane har sun fara cin durwansu babu babbaka, sai aka fara yi musu tonon silili. Don haka da wuya manufarsu ta yin gwanjon kasar nan ta cimmawa, musamman ma ganin yadda Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ke tangal-tangal.
Tsarin tattali na nufin tarairayar dukiya, ta hanayar bude kofofin samu da toshe kafafen asara, bisa turbar nazarin tsimi da tanadi. Irin wannnan fahimta ta yalawata arziki a tsakanin al’umma, don warware wa al’umma talalar talauci, ta saba wa kwarewar Madam In-gwangwaje-in-wala, inda ta himmatu wajen tsuwurwurta ayyukan lukudi da lakume Hauro, ta yadda za a ci gaba da jefa Haurobiyawa cikin haure-haure da hauragiyar rayuwa.
Sanin Haurobiyawa ne cewa, Madam In-gwangwaje-in-wala ke juya akalar damin dukiyar kasar nan, maimakon ta fito da tsare-tsaren da za su inganta walwalar al’umma, sai ta karke da wala-wala, inda ta kassara darajar Hauro, ta haifar da karancin man tunkuza,uwa-uba aka kasa biyan ladar kwadagon masu aikatau a kan kari.
Haurobiyawa, kada a dauka ina jefa azargagiyar zargi a kan Madam In-gwangwaje-in-wala, a’a ko kusa, abin da kawai nike ta kokarin nusar da ku shi ne, cewa, a ‘Tsarin tsimi da ta’adi, ga lukudi, ga lakume kudi da ake aiwatar wa al’umma, ana yi ne don Jona-tantin mulkin mulaka’u da Gudun-loko a fadin kasa. Manufar wannan tsari ita ce a tabbatasr da cewa talakawan Haurobiya sun dawwama a cikin sasarin talalar talauci, har sai sun yi dan wuya kamar rakumi-rakumi zololo.
kungiyar Saraf-na-sadaf tam aka Madam In-gwan-gwaje-in-wala a gaban kuliya, don ta yi bayani yadda aka wawushe lalitar kasa. Sun kuma dogara ne kacokan kan batutuwan da Farfesa Sallau Lado ya bijiro da su a cikin watannin da suka arce.
Irin ta’asara da mulkin mulaka’un mai danboto da sanda jirge ya tafa a kwanon tasa, ya isa a ce Haurobiyawa sun wancakalar da ita, tun ma kafin a kada kuri’u. Hakika mun kosa, muna bukatar sauyi. Duk wanda ya ki tabukawa wajen wancakalar da miyagu, to suna iya yin gwanjon kasr nan, su kwashe dan abin da ya rage musu, su arce kasashen ketare. Duk wanda ya yi kwazo ko da jiga-jigan mai dan boto sun cutar da shi, to akwai yiwuwar Mai-duka, Mai kowa, Mai komai ya yi masa irin ta Babban Mutum Mai rawani na birnin Dabo. Kowa yasan yadda Masanin Sisi-da-sisi ya fafata da miyagu. Don haka kada mu rankwafa wajen kawar da Mai dan boto da sanda jirge, domin mun gaji da jirgin Haramta Bobo da kwambon bokoko, al’amarin da ya mayar da kasa ta zama babu tsaro sai tsoro.
‘Idan kusu na da sata, ai an ce daddawa ma doyi take yi,’ wannan dai na nuni da cewa Haurobiyawa ne suka yi sakaci da sakarci, har kowane macuci ya samu kafar cin musu mutunci.
Idan har ba ku ari faden Malam Mantau ba, kun san cewa Sisiliya ta sulale da sulalla; Atuke ya tatuke Asusun Malam Habibu, wanda a halin yanzu aka mayar da shi Mabudin dutse; ga Araruma ta rarumi nata, Santala kwaiduwa ta kashe kason gyaran farfajiyar saukar tsuntsayen sama; ga Audu-tela, wanda ya yi dumu-dumu wajen wawushe sudin man tunkuzar Haurobiyawa. Wannan rukuni na samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya, su ne manyan ’yan wala-wala da Madam Ingwangwaje-in-wala ta rike musu kahon nagge da karsana su yi ta nannagar ruwan nonon dukiyar al’umma. Talakawa sun ga tasku a tsarin Damo-da-kura-da-diyya da dama-dama-da-kurda-kurdar wasan Samson siya-siya da kwakwalen al’umma. Ga shi nan dai dara ta ci gida, Messi Banga-banga Tukururu ya jefa ta-mola a gidansu. shi kuwa Dumu-dumu Muzu-muzu da zuwansa wai zai sauya salon wasa, amma sai ya karke da dagula al’amura. Yanzu duk wata gazawa ta jam’iyya mai dan boto da sanda jirge kokari kawai suke yi su dora alhakin mugun aikin da suka tsuwurwurta a kan jam’iyya mai maganin ciwon kurungu. ‘Tarwada ta hango ka masunci mai jar fatsa da koma.’
Sanin kowa ne an dade ana tafka ta’asa, amma Shugaba Mai Gudu a loko da Jona tantin mulki ya zama rakumi da akala, sai abin da tsohon Kilaki ya ce ya aiwatar shi za a yi, don haka shi Jagoran mutanen yankin Hauren Danja ne, ba na kasa ba. Don haka duk mai hankali a cikin kwanyarsa, dole ne ya nuna kyama ga tsarin da ake tafiyar da Haurobiya a kai. Kuma ai Baudadden Joji ya bijiro musu da batu na ingarman karfen karafa, inda ya ce shi arce zai yi darar Jam’iyya mai maganin zogi da radadin ciwon kurungu ta kama ragamar mulki. Su kuwa masu Malun-malun tuni mabiya suka fasko jirginsu. kaka-kara-kaka-kaka?
Ni dai tuni na yi gwanjon ’yan wala-wala, don Haurobiyawa su samu wal-wala. Su kuwa masu neman salala, sais u nemi sulalla, tun kafin su ji a salansa, don an daina sulalewa da sulalla, sai dai sila wadda tafi salsala da salala. Kuma an daina ganin galala ballantana a dinka galila.