In za ka gina ramin mugunta… (2)

Bayan ta kanmala abinci ta samu kwano daban ta zuba abincin sannan ta kawo gubar ta zuba a ciki ta ajiye. Daga nan sai ta shiga ban-daki don ta yi wanka. Tana ban-daki sai su Auwalu da Sani suka dawo daga makaranta. Kasancewar Auwalu yana jin yunwa bai tsaya mahaifiyarsa ta zo ba, sai ya […]

In za ka gina ramin mugunta… (2)

Fatima da Jamila, ‘ya’yan Jamilu Abdullahi Qanqara

Bayan ta kanmala abinci ta samu kwano daban ta zuba abincin sannan ta kawo gubar ta zuba a ciki ta ajiye. Daga nan sai ta shiga ban-daki don ta yi wanka. Tana ban-daki sai su Auwalu da Sani suka dawo daga makaranta. Kasancewar Auwalu yana jin yunwa bai tsaya mahaifiyarsa ta zo ba, sai ya shiga kicin da kansa ya dauko abincin nan mai guba ya fara ci tun daga cikin kicin.

Fitowarsa daga kicin din ya yi daidai da lokacin da mahaifiyarsa ta fito daga ban-daki dubawar da za ta yi sai ta ga kwanon abincin nan da ta sanya wa guba a hannun danta. Nan da nan ta yi saurin kwacewa sai dai kafin ta ce komai tuni Auwalu ya fadi a kasa yana birgima yana fadin “Wayyo cikina!”

Nan da nan Delu ta rude ba abin da take yi sai kuka, domin ta san gubar da ta zuba a cikin abincin da dan nata ya ci ne ta fara aiki a jikinsa. Hankalinta ya yi matukar tashi ta dauko ruwa tana ba dan nata amma ya ki karba sai ihu yake yi.

Sani kuma cikin kuka ya fita da gudu don kiran mahaifinsu a gona. Sai dai kafin mahaifinsu ya zo tuni Auwalu ya ce ga garinku nan.

Kowa a gidan ya ji mutuwar Auwalu musamman ma Sani da suka shaku ya yi kuka da bakin cikin rashin dan uwansa. Ita kuwa Delu ta fi kowa shiga damuwa domin ta yi ta zargin kanta tare da nadamar abin da ta aikata.

Darasin labarin:

Babu kyau shirya wa wani mugunta don watakila ba shi kadai abin zai shafa ba har da kai.