Ina alfahari da masu sana’ar fim – Janar Buhari

A Talatar da ta gabata ce ’yan fim din Hausa a karkashin jagorancin Isma’il Na’Abba Afakallah suka ziyarci Shugaban kasa mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari a Daura. Sun bayyana kai ziyarar da nufin taya Buhari murnar lashe zaben Shugaban kasa da ya yi ne, sannan suka gabatar masa da matsalolin da suka hana masana’antar […]

Ina alfahari da masu sana’ar fim – Janar Buhari
Ina alfahari da masu sana’ar fim – Janar Buhari

A Talatar da ta gabata ce ’yan fim din Hausa a karkashin jagorancin Isma’il Na’Abba Afakallah suka ziyarci Shugaban kasa mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari a Daura.

Sun bayyana kai ziyarar da nufin taya Buhari murnar lashe zaben Shugaban kasa da ya yi ne, sannan suka gabatar masa da matsalolin da suka hana masana’antar fina-finan Hausa ci gaba.
“A matsayinmu na masu shirya fina-finai da kuma mawakan Hausa mun kawo maka wannan ziyarar ce don mu taya ka murna kan wannan gagarumar nasara da ka samu ta lashe zaben Shugaban kasa da ka yi, sannan mu kara tabbatar maka da cewa masana’antarmu na tare da kai dari-bisa-dari, kasancewar da yawanmu sun yi amfani da fuskokinsu da kuma muryoyinsu don yi maka kamfen har ka samu nasara. Allah Ya taya ka riko.” Inji Afakallah.
Ya kuma jinjina wa Buhari saboda jajircewar da ya yi wajen takarar da ya rika fitowa har karo na hudu.
Ya ce: “Jajircewar da ka yi ta zamar mana abar misali cewa, duk lokacin da kake yin abu da gaske ka kuma tsaya a kai, to Allah Zai ba ka nasara, za ka samu rinjaye a kan karya. Hakan ya zama mana haske a matsayinmu na matasa masu tasowa, wato mu tsaya mu rike gaskiya, mu rike amana.”
Ya kuma bukaci Janar Buhari ya magance musu matsalar satar fasaha da ke neman durkusar da masana’antar.
“Daga karshe muna kara tunatar da kai alkawarin da ka dauka na magance mana matsalar satar fasaha a lokacin da kake kamfe a Legas, sannan muna bukatar a tallafa wa masana’antar don ta tsaya da kafafunta har ta hau turbar da za ta iya gogayya da kowace masana’antar fim a duniya.” Inji shi.
Janar Buhari ya bayyana matukar jin dadinsa da ziyarar da ’yan fim suka kawo masa, sannan ya tabbatar musu zai dauki matakin da zai habaka masana’antar a duniya.
“Tabbas ina alfahari in ga matasa suna da abin yi ba tare da dogara da gwamnati ba, su daina roko da tumasanci, ko shaye-shaye. Sannan ina yaba muku bisa gudunmuwar da kuka bayar wajen wayar da kan matasa manufofina, don haka zan tsaya wajen ganin masana’antar ta daidai, musamman ma wajen yaki da satar fasaha da ke zama barazana gare ku da kuma tattalin arzikin Najeriya gaba daya.” Inji Buhari.
A cikin ’yan fim din da suka halarci bikin akwai Isma’il Na’Abba Afakallah da Hamisu Lamido Iyantama da Ali Nuhu da Nura Hussain da Dauda Kahutu Rarara da Rabi’u Ibrahim Daushe da Ari Baba da Mustapha Naburaska da Baban Chinedu da Jamila Nagudu da Hadizan Saima da Yahanasu Sani da Hadiza Umar Soja da sauransu.