Ina alfahari da sanaa’ar bugu – Sarkin Mabugan Zazzau
Sana’ar bugu tsohuwar sa’ana ce wadda ta shara a kasar Hausa, kuma har zuwa yanzu ana alfahari da ita. Aminiya ta ziyarci unguwar mabuga da ke bakin kasuwa cikin birnin Zariya domin jin yadda ake gudanar da sana’ar. Sarkin mabugan Zazzau Zubairu Sa’adu ya fayyace mana zare da abawa na wanna tsohuwar sana’a. Ga yadda […]
Sana’ar bugu tsohuwar sa’ana ce wadda ta shara a kasar Hausa, kuma har zuwa yanzu ana alfahari da ita. Aminiya ta ziyarci unguwar mabuga da ke bakin kasuwa cikin birnin Zariya domin jin yadda ake gudanar da sana’ar. Sarkin mabugan Zazzau Zubairu Sa’adu ya fayyace mana zare da abawa na wanna tsohuwar sana’a. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Za mu so mu ji takaitaccen tarihinka?
Zubairu Sa’adu: Da farko sunan Zubairu Sa’adu Sarkin mabugan Zazzau kuma na gaji wannan sana’ar ce daga wajen mahaifina Malam Sa’adu Sarkin mabugan Zazzau bayan rasuwarsa, kuma an haifeni kimanin shekaru 35 da suka wuce kuma tun ina dan shekara bakwai, idan na dawo karatun allo nake zama domin taimakawa wajen wannan sana’a, tun ina kallo har nima na fara gwadawa.
Na taso har Allah Ya sa na gaji sarautar mabuga. Kuma wannan sana’ar ta bugu kamar yadda tarihi ya nuna tafaro ne tun sama da shekaru kamar 200 da wani abu da suka gabata a nan kasar Zazzau, kuma ana yin ta ne tun zamanin da aka fara rini irin na tukwane wanda ake yi da baba, a lokacin duk kwalliyar da ake yi ko gyaran da ake yi na sutura ana yi ma sara.
Kuma a lokacin ne za ka ga idan kai rini na saki, ko kwakwoto, ko girken saki ko hankaka ko wata riga da ake kiranta kore da kuma rawani ‘yar kura da rigar mata da kuma rawani bakin dan kura da kuma girken nufe, ita riga ce tasa ki sai kwonkwata, sai na mata adire wanda akafi sani da kamfala wadannan su ne kalan bugu da ake yi sa kuma kayayyakin da ake nema na farko da mune muke zuwa mu saro itacen da ake amfani da shi.
Aminiya: Wane irin ice kuke amfani da shi?
Zubairu Sa’adu: Mun fi amfani da ice iri uku wato: icen tsamiya da icen madaci da kuma itacen kadanya da su ne muka fi amfani. Kuma mu ne muke sassaka abin mu da kanmu, bayan mun saro itace akwai uwar ma buga wato itacen da ake shunfidawa a kasa, sai kuma dan mabuga shi ne wanda ake rikewa ana bugu da shi to abu nafarko za’akoya maka yanda ake shinfida kayan kafin akai ga fara bugawa. To ka ga wadannan su ne abubuwan da ake nema. Kodayake, akwai ruwa da zaka aje kusa da kai daga nan za’a fara buga kaya wanda za’a mai shini, a mai shuni sai ka ga an buga kaya ya bugu sosai yana kyalli to kowa Aminiya: Bugu hawa nawa ne?
Zubairu Sa’adu: Shi bugunnan hawa-hawa ne. Kuma karfin mutum domin karamin bugu muna cajan naira 200 ne, sannan akwai har wanda muke cajan naira 1500. To ka ji yadda bugun yake kamawa kuma bari na fada maka wani abu da anan Arewa, kasar Hausa babu inda yakai mu kwarewa a wannan sana’ar ta bugu domin daga ko ina daga arewacin kasar nan ana kawo mana aiki saboda iya aikin. Amma saboda rashin tallafi yanzu Jihar Kano sun sha gabanmu. Kuma ita wannan sana’ar tana bukatar natsuwa da kuma fahimtar yadda ake shimfida kaya domin gudun samun akasi na hujewan kaya.
Aminiya: Wace fa’ida ka samu albarkacin wannan sana’ar?
Zubairu Sa’adu: To da farko amfanin da yawa baya da kasancewa na sarki na masu wannan sana’ar na je Makkah kuma na yi aure kuma nasan jama’a kai bama ni ba duk wanda yake tare damu a nan baya rasa amfani ta bangaren rufin asiri da kuma gudanar da al’amuransa na yau da kullum cikin rufin asiri albakacin wannan sana’ar don haka mun gode wa Allah.
Aminiya: Akwai wata matsala da ka taba fuskanta?
Zubairu Sa’adu: Akan sami akasi kamar na lalacewar kaya wani ya ce a biya shi, wani kuma ya ce a gyara masa, sannan kuma a wajen bugun kana iya samun akasi ka buge yatsun hannunka, idan ba sa a aka yi ba duk su kare raye ko ita mabugar ta buge maka goshi. Ko idan ka daga sama ta kufce ta dawo ta buge ka a kai. To duka ana samun irin wannnan.
Aminiya: Kasancewar wannnan itama tsohuwar sana’ace, ko kuna da abokan wasa kamar yadda makera da wanzamai suke abokanan wasa?
Zubairu Sa’adu: kwari kuwa muna da abokanan wasa kamarsu mu mabuga mahauta ne abokanan wasanmu domin su ne bayinmu.