Ina alfanun tafiye-tafiyen Shugaba Buhari kasashen waje?

Hulda ta difilomasiyya tsakanin kasa da kasa abu ne mai muhimmancin gaske, ganin cewa babu wata kasa a duniya da za ta iya rayuwa ita kadai ba tare da kulla alaka da wata ko wasu kasashe ba a fannoni daban-daban na samar da ci gaba a cikin gidanta. Najeriya, kasa mafi yawan al’umma a Nahiyar […]

Ina alfanun tafiye-tafiyen Shugaba Buhari kasashen waje?
Ina alfanun tafiye-tafiyen Shugaba Buhari kasashen waje?

Hulda ta difilomasiyya tsakanin kasa da kasa abu ne mai muhimmancin gaske, ganin cewa babu wata kasa a duniya da za ta iya rayuwa ita kadai ba tare da kulla alaka da wata ko wasu kasashe ba a fannoni daban-daban na samar da ci gaba a cikin gidanta.

Najeriya, kasa mafi yawan al’umma a Nahiyar Afirka, wacce ake yi wa kirari da Giwar Afirka, dole ne ta tabbatar da cewa ta ci gaba da rike matsayinta na mai karfin fada-a-ji a siyarsa Afirka da hulda da kasashen duniya masu karfin tattalin arziki za su yi da kasashen na Afirka.

Hakki ne da ya rataya a kan Shugaban Kasa kamar na Najeriya ya tabbatar da kasarsa ta ci gajiyar tallafi ta kowacce fuska da kasashen masu karfin tattalin arzikin ke bai wa kasashe ’yan ‘Rabbana Ka wadata mu.’

Wajen tabbatar da kasa ta ci gajiyar irin wadannan tallafi, wasu lokuta yakan wajaba Shugaban Kasar ya tashi takanas domin kai ziyara ketare, walau halartar taron da ke tattauna hanyoyin shawo kan wasu matsaloli, ko kuma ganawa da shugabannin kasashe domin mika kokon bara.

Tun hawansa mulkin Najeriya a shekarar 2015, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ke shan suka daga ’yan adawa da wadansu ’yan Najeriya dangane da yawan tafiye-tafiyen da yake yi zuwa kasashen ketare.

Watannin kadan da hawansa mulki, Shugaba Buhari ya yi fama da rashin lafiya da ta kai shi kasar Birtaniya jinya, ba ya ga ziyarar kasashen duniya da ya rika yi a wa’adinsa na farko, babu dan Adam da ya wuce Ubangiji Ya dora masa jinya kamar yadda Shugaba Buhari ya yi fama da ita.

Galibin ziyarar da Buhari ya rika zuwa kasashen ketare a tsawon wa’adinsa na farko za a iya cewa ba su haifar da komai ba in ana maganar magance matsalolin da suka yi wa Najeriya dabaibayi. Har zuwa yanzu babu wata matsala da shugabannin kasar ke ikirarin cewa sun magance su sakamakon neman mafita ko dauki daga tafiye-tafiye da suke yi.

Har yanzu Najeriya na fama da matsalar cin hanci da rashin tsaro da tabarbarewar ilimi da lalacewar fannin kiwon lafiya da kuma na matsin tattalin arziki. Wadanda su ne ake ta wakar cewa ana yin wadannan tafiye-tafiye ne domin magance su.

A yanzu haka, balaguro da Shugaban Kasa Buhari ya yi zuwa ketare sun doshi 50, inda a kowacce tafiya ake fita da tarin mukarrabai da kashe makudan kudade wadanda ya kyautu a ce an yi amfani da su wajen samar da muhimman ayyukan more rayuwa.

Ya kamata a ce ba kowane taro Shugaban Kasa zai debi ayari ya tafi ba, akwai bukatar Shugaban ya rika duba muhimmancin taro wanda ya kamata a ce ya zamo wajibi ya halarta. Wasu tarurrukan za su iya samun wakilcin mataimakinsa, wanda Shugaban Kasar ya yi amanna cewa mutum ne mai kwazo da kwarewa wajen aiki.

Ministoci za su iya wakiltar Shugaban Kasa a wasu da yawa cikin tarurrukan da Shugaban ke halarta domin rage kashe kudaden gwamnati. Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa za a rage irin makudan kudaden tafiye-tafiye da ma’aikatan gwamnati ke yi abin da kuma ya saba da irin yawan  kudade da aka ware a kasafin kudin badi domin tafiya zuwa ketare domin tanadi da aka yi na kudaden ya haura wanda aka ware a bana. Hakan na nuni da cewa gwamnatin ta daura aniyar kashe kudade wajen tafiye-tafiye zuwa ketare.

Babu yadda Shugaban Kasa zai tafi ketare neman masu sanya hannun jari su shigo Najeriya, yayin da ’yan kasuwa na cikin gida su kansu neman tudun dafawa suke yi wajen bunkasa harkokinsu. Ya kamata a samar da kyakkyawan yanayi na kasuwanci a cikin gida da zai sanya masu sanya jari na waje su yi tururuwar shigowa Najeriya, maimakon dibar tarin ayari wajen halartar tarurrukan bunkasa tattalin arziki a kasashen waje.

Akwai bukatar Shugaban Kasa Muhammdu Buhari ya dubi yanayin tattalin arzikin Najeriya wajen tafiye-tafiyensa ketare. Kuma ya maida hankalinsa wajen gabatar da wasu muhimman ayyuka a cikin gida da ke neman kula ta musamman daga gare shi.

Umar Ahmad Abubakar,(08039175742)