Ina amfanin badi ba rai?
Furuce-furucen siyasa da Sanata A’isha Jummai Alhassan, Munistar Ma’aikatar Al’amuran Mata ta yi a makon jiya sun firfitar da wasu abubuwa guda biyu, wadanda ‘yan siyasar Najeriya suka dade suna waswasi game da su, wadanda kuma za su iya kara dumama yanayin siyasar kasar nan, wanda a halin yanzu ana iya cewa a daskare yake. […]
Furuce-furucen siyasa da Sanata A’isha Jummai Alhassan, Munistar Ma’aikatar Al’amuran Mata ta yi a makon jiya sun firfitar da wasu abubuwa guda biyu, wadanda ‘yan siyasar Najeriya suka dade suna waswasi game da su, wadanda kuma za su iya kara dumama yanayin siyasar kasar nan, wanda a halin yanzu ana iya cewa a daskare yake.
Da farko dai ta yi ishara da cewa Ubangidanta Atiku Abubakar, Wazirin Adamawa na son yin takarar Shugabancin kasar nan a shekara ta 2019, sa’annan kuma shi da kansa bai musanta haka ba, hasali ma yaba mata ya yi game da kokarinta na fadakar da jama’a game da kulafucinsa na sake tsayawa takara. Abu na biyu kuma da ta nuna shi ne wai ba dukkan ministoci ne ke goyon bayan Shugaba Buhari ba ko da ma zai fito takarar shugabancin kasa a 2019.
Wadannan kalamun sun buga wa ‘yan siyasa kaimi, ko kuma a ce an tayar da dodon siyasa ne firgigi daga dogon barcin da yake sharbawa, ba a kuma san irin harigidon da zai haifar ba a fagen siyasa da kuma jarumin da zai kame shi, ya sake daure shi.
Akwai ‘yan siyasa da yawa da za su iya rantsewa cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai taba furta cewa shi ba zai sake tsayawa takarar shugabanci ba a karo na biyu, kuma idan har ta dauro zai sake tsayawar, to bisa ga dukkan alamu shi da Wazirin Adamawa za su sake fafatawa ke nan a zaben fitar da dan takarar jam’iyyar APC, idan ma har a karkashinta ne Atiku zai fito.
To amma sai dai duk da haka nan lokacin bayyana ra’ayi game da takara ko akasin haka bai yi ba, domin wannan al’amari ne na siyasa, kuma sai bayan an tuntubi dukkan masu ruwa da tsaki a jam’iyya da kuma wajenta kafin masu sha’awar takara su sanya zaren dambacewa. A tsarin dimokuradiyyar Amurka wacce muke koyo, jam’iyyar da ke da gwamnati kan ba shugaba ko gwamnan da ke bisa mulki damar sake tsayawa idan har yana sha’awar yin haka ba tare da wata hamayya daga ‘ya’yan jam’iyya ba. Amma a nan Najeriya ba haka abin ke kasancewa ba. Idan Shugaba ko gwamna na son sake takara sai ya fuskanci wakilan jam’iyya da ake kira delegates a babban taron da za a yi don fitar da dan takara tare da dukkan wadanda ke kalubalantarsa, idan kuma har an amince masa ya tsaya ba hamayya to sai an jefa masa kuri’a daga mafiya rinjaye game da haka. Ashe ke nan a tsaya ma ana batun Shugaba ko gwamna da ke bisa karaga ba zai sake takara ba don wasu su samu ‘yancin fitowa bai taso ba, wanda duk ke da sha’awar fitowa neman a tsayar da shi takarar shugabancin kasa ko na gwamnan jiha na iya gwada sa’arsa muddin ya ji cewa kashinsa ya yi kwari.
Haka nan kuma hankoron da wasu ke yi don lallashi ko kuma janyo ra’ayin wani shugaba ko gwamnan da ke bisa karagar mulki don ya sake yin takara aikin Baban-Giwa ne suke yi, domin kuwa soja fa malamin kansa ne a wajen yaki, kuma wanda duk ya yi da kyau ya sani, wanda kuma bai yi da kyau ba ya sani. Jama’a na nan jiransa domin su yi masa hisabi, su kuma nuna masa a kwaryar cinsa a ranar farko. An dai ce mai daki shi ya san inda yake yoyo, kuma dabara takan rage wa mai shiga rijiya ce, ba wanda zai ce masa ga yadda zai yi. Batun tsayawa takarar zabe na jam’iyya ne, ita ce ta fi sanin wanda zai biya mata bukata, ta kuma fi kowa fahimtar mai-kaman-zuwa, wanda za ta ji dadin aike ko’ina.
To a yanzu haka kawunan manya-manya da jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar APC a rarrabe suke, bakunansu kuma an ce ba su zo daya ba game da sake tsayar da Shugaba Buhari a 2019. Shi kuma mulkin nan fa ba gado ba ne ko mallakar wanda ke rike da ragama balle ya ce ga wanda zai gaje shi, ko kuma sai wanda ya ga dama zai danka wa ragamar ya ci gaba da ja.
Saboda hakan maimakon ‘yan siyasa da magoya bayansu su tsaya suna ta bankaura game da zaben 2019 da wanda zai tsaya da wanda suke gani ba zai tsaya ba, kamata ya yi su dukufa wajen yin gyararraki na musamman game da yanayin da jam’iyyunsu ke ciki. Ta haka ne za su samu damar dinke barakar da ta yi kamari a cikinta, musamman a wasu jihohin da hakan ke barazanar rusa jam’iyyar.
To ai an yi ittafakin cewa ba wani abu ne ba kuwa ya haddasa yamutsi a cikin jam’iyyar APC da rassanta na jihohi illa rashin kyakkywan shugabanci a cikin jam’iyyar, wanda ke sa bangonta na tsattsagewa har kadangarun na kurkurdawa. Wannan ne ya sa Wazirin Adamawa nuna rashin gamsuwarsa game da halin da jam’iyyar ke ciki wanda ya nuna cewa an bar gwamnatinta kara-zube, tamkar marainiyar da ba ta da iyayen goyo, jama’a kuma na cikin wani halin ni-‘ya-su. ‘Ya’yan jam’iyya da yawa sun damu ainiun game da abin da suke kira rashin kallon alkiblar da gwamnati ke yi, kamar yadda Atiku ke damuwa, game da rashin kiran taro akai-akai don tunkarar mtsalolin da za su dinga tasowa ana magancewa akan kari. Hakan kuwa ba karamin koma-baya ba ne ga jam’iyyar siyasa, musasmman ma wacce ke jan ragamar kasar da kuma wasu jihohin cikinta fiye da ashirin.
Abin da ya fi kamata yanzu ‘ya’yan jam’iyyar APC, manya da kananana su mayar da hankali a kai shi ne farfado da martabar jam’iyyarsu ba wai batun wane ne zai yi takara wane ne kuma ba zai yi ba. Idan har aka bari irin wannan al’amari na kawazucin mulki ya zarme a zukatan ‘ya’yanta to zai iya kai wa ga yi mata lahanin da zai sa a ga bayanta. Idan kuma haka ya faru an kashe saniyar da ake tatsa ke nan, kuma ina amfanin badi ba rai ke nan tun da dai babu jam’iyyar da za a yi takara a karkashinta?