Ina barayin suke? (2)
Lallai ba su ne kadai barayin da muke da su ba a cikin kasar nan, muna dai iya cewa su ne hamshakai, su ne, gandama-gandama, su ne kuma masu kawo illa ga kasa da sauran lamurran rayuwa. Daga Kansila zuwa Shugaban kasa, nan ne ake da dabar masu sunkurun ganin bayan talaka da neman sai […]
Lallai ba su ne kadai barayin da muke da su ba a cikin kasar nan, muna dai iya cewa su ne hamshakai, su ne, gandama-gandama, su ne kuma masu kawo illa ga kasa da sauran lamurran rayuwa. Daga Kansila zuwa Shugaban kasa, nan ne ake da dabar masu sunkurun ganin bayan talaka da neman sai sun ga bayan kasar da suke wa ‘hidima.’ Idan da abin a zauna a kididdige tarin dukiyar da wadannan gungun mutane suka sace, suka kimshe, suke wandaka da ita, za mu fahimci cewa ashe ba laifi ba ne idan kashi 70 cikin 100 na al’ummar kasar nan suka kasance cikin tasku da talauci da fatara da shiga cikin kowane irin halin ni’yasu na rayuwa. Kenan ba abin mamaki ba ne da Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya jaddada mana wadannan ‘yan uwan Ali Baban wannan zamani. Amma ba su kadai ba ne, akwai wasu barayin can boye wadanda kila ma sun fi wadannan da Balarabe Musa ya zayyana barna da tayar da hankali. Su wane ne wadannan?
Mu koma ga jawabin da Balarabe Musa ya yi, ya ce ne matsalar kasar nan ta bARAYIN SHUGABANNI ce. Kenan ba dole sai shugabannin siyasa ba, za a iya samun wasu gungun barayin daga cikin shugabannin addini da na tattalin arziki da saye da sayarwa da kasuwanci da na sauran al’umma da suka hada daga Sarakuna da Hakimai da Dagatai da Masu unguwannin. Haka kuma lissafin Balarabe Musa, duk da bai fito karara da alkalumman ba, yana iya hadawa da shugabanni a kasuwa da makarantu da cikin gidajenmu, wato tsakanin iyali. Kenan muna iya cewa barayin suna da yawa! Ta yaya za mu gane irin wadannan shugabanni da irin tasu barnar da suke yi wa kasa da al’umma?
Mu soma da shugabannin addini, ba sai na yi ta mawakin nan Fela ba, da yake cewa ka taba ganin inda Fasto ko Fada ko Liman ko Ladan ko wani rikakken malamin addini da yake talaka? Kila ka ce ai naka malamin ga shi nan kwance cikin talauci da rashi, kila domin shi ba shugaban ba ne na gaskiya, da kila tuni ya yi hannun riga da wahala da tashin-tashina. Amma nawa daga cikin shugabannin addinin da muke da su a cikin kasar nan suka kasance talakawa? Nawa suke yawo da jiragensu na kan su a sararin samaniya? Nawa ke cikin daular aljannar duniya; su ne da jifa-jifai da manya-manyan gidaje da yawon bude idanu a kasashen duniya, a lokacin da suka so, yadda suka so, alhali ko aikin kwarai ko wata sana’ar kirki ba su da ita? Nawa daga cikin shugabannin addinan da muke da su za mu iya kira mutanen talakawa ko masu son talakawa ko da ba mu kira su barayi ba kai tsaye? Nawa? A fa lura, shi wannan shugaban addinin da ke faman bayyana mana inda wuta ko aljanna suke, da sakamakon wadanda suka saba wa Maiduka, wasu ba su ma yarda akwai gobe kiyamar ba, balle wani abu wuta ko aljannar. Idan ka yi maganar aljanna, ga irin wadannan malamai, sai ka ji suna maganar Aso Rock ko fadojin Gwamnonin jihohi ko ofisoshin ministoci ko kwamishinoni ko shagunan hamshakan ‘yan kwangila ko kuma unguwannin Asokoro ko bictoria Island ko makamantan su. Nan ne aljannarsu! Idan kana ji suna maganar wuta, to rashin samun kwangila ce, ita ce wuta a gare su. Wata wutar ita ce rashin wata hanyar da za su diba daga tarin dukiyar al’umma. Duk lokacin da hakarsu ba ta kai ga ruwa ba lokacin ne zafi ke damun su, lokacin ne suke tuna akwai wata aba wai ita wuta, ba wai don sun amince da akwai tan ba a can lahira !
Shin ba mu san da irin wadannan shugabannin addinin ba ne? Shin su kuma me ya raba su da sauran barayin da Balarabe Musa ya zayyana mana? Mu dinga yi wa kanmu kiyamul laili fa!
Ba wadannan kadai ba, shin ina barayin da suke zaune cikin kasuwanci da tattalin arzikin kasar nan, ba su da daki ko falo ko wurin shakatawa sai dukiyar kasa da ta al’umma? Wane ne zai ce da ni yawancin shugabannin da muke da su, masu kamfanoni da masana’antu bilahaddin, su kuma masu ceto ne ba cutarwa ba? Don Allah wane irin kasuwanci ko sana’a wadannan manya, kuma hamshakan masu ‘kudi’ suke yi da suke tara da samun wannan kazamar riba? Wasu daga cikin su, sun ma if gwamnatin kasar tarin dukiya, kuma wai sana’a ce suke yi? Sai mu tambayi kanmu, wace irin sana’a ce wannan da ke sa yara ‘yan shekara 30 zuwa 35 ke da tarin dukiyar da ta fi ta wata gwamnatin jiha? Wace sana’a ce wannan? Wasu za su ce ai kwangila suke yi, amma mu tambayi kanmu shin kwangila aikin yi ce ko wata sana’a ta a zo a gani? Shin me ya bambanta dan kwangila irin wannan zamani namu da barawo? Me ya bambanta satar da shugabanninmu na siyasa ke yi da irin wadda ‘yan kwangila da hadin bakin shugabanninmu ke yi, cewa nake, Ali ne ya ga Ali! Kenan shugabannin sana’o’i da kwangiloli su ma barayin ne!
Haka batun yake a fannin harkar ilmi da kiwon lafiya da sauran al’amurran zamantakewar al’umma. Hedimasta a Firamare barawo ne, Firinsifal a Sakandare, ba shi dama, satar zai yi, balle irin su Rekto da Furobos da Shugabannin jami’i’o, duk dai jama’ar ce ta Gambu! Ke nan duk inda ka samu shugaba, komin kankantar wurin da yake shugabanci sai ka ga dan hali ya bayyana. Shi ya sa a harkar asibiti ba fus. Harkar gina hanyoyi da sa kwalta da gina azuzuwa ba shugabannin kwarai, sai macuta.
Kenan harkar sata a Nijeriya ta riga ta zama ruwan dare, domin kuwa ba ta bar kowane shugaba da tsarin shugabancin da yake yi ba. Ina shugabannin kwadago? Ina shugabannin ‘Yan Yuniyon da masu tura baro da masu faskare da ‘yan-ga-ruwa da shugabannin mata masu adashi da kungiyar malamai tun daga Firamare zuwa Sakandare da Jami’o’i? Ina maigida da gidansa, ina matarsa da ‘ya’ya, ina mai sayar da man gyada da tumatir a kasuwar kauye? Su wadannan ba barayi ba ne?
Za Mu Ci Gaba