Ina barayin suke?(1)

Na dade ina neman inda barayin kasar nan suka shige, musamman ganin ganin cewa ba wani abu ne ya addabi kasar ba, face shegiyar sata da wasu daga cikin al’ummar kasar ke faman yi, amma su kare ba wanda ya san inda suke ko kuma yadda suka yi da dukiyar jama’a da suka sace. Ina […]

Ina barayin suke?(1)
Ina barayin suke?(1)

Na dade ina neman inda barayin kasar nan suka shige, musamman ganin ganin cewa ba wani abu ne ya addabi kasar ba, face shegiyar sata da wasu daga cikin al’ummar kasar ke faman yi, amma su kare ba wanda ya san inda suke ko kuma yadda suka yi da dukiyar jama’a da suka sace. Ina neman sanin inda wadannan barayi suka shige, ba don wani abu ba sai don in har ba a iya kame su, a hukunta ba, to na san mazauninsu da yadda in na gan su zan gane su, in kyamace su, in kauce musu, in kuma nemi Allah Ya yi doguwar katanga tsakanina da su. Sai dai ba wani abin ta da hankali irin ko-in-kula- da ake yi wa wannan matsala ta sata da barna a cikin kasar nan, ta yadda sai a kasa gane wane ne barawon, wane ne ke neman kama barawon, wa kuma ke bin sawun barawon da wanda ke neman kama mabi sawun barawon ko mai neman kamawar. Abin sai ka ga tamkar yanar gizo da kuda ya fada ciki ne, duk yadda yake so ya fita, sai kara daure kansa yake a ciki.
To amma da alama mun fara samun haske, wasu daga cikinmu sun fara bayyana mana ko su wane ne barayin kasar nan, sun kuma bayyana mana inda za mu je mu gan su ko mu neme su in da gaske muke yi. daya daga cikin jiga-jigan siyasa da mulkin kasar ne, wato Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a zamanin Jamhuriyya ta biyu, a karkashin Jam’iyyar PRP ta Malam Aminu Kano, shi ne ni a nawa tunanin ya fasa kwai game da barayin kasar nan, wadanda suke neman sai sun durkusar da ita.
Alhaji Balarabe Musa ya bayyana haka ne kamar yadda rahoton jarida ya zo da shi a lokacin da wasu masu kishin kasa suka kai masa ziyara a liyafar fatar alheri a lokacin da ya cika shekara 77 da haihuwa. A nan ya ce, ‘matsalar da muke ciki a kasar nan ita ce, shugabanninmu a cikin kasar bARAYI ne kurum.’ Ya kara da cewa ‘idan har abin da na fada akwai tababa, bari na sake tuna mana, duk wani wanda ya samu dama ya zama Kansila ko Mamba na Majalisar Jiha ko Sanata ko Gwamna ko Shugaban kasa to ba talakawa ya yi wa aiki ba, kansa ya bauta wa, shi ya sa nan da nan za a ga ya fi kowa kudi daga yankin da ya fito. Kansila a yawancin wurare ya fi kowa arziki a mazabarsa. Shugaban kasa da ya bar mulki, shi za ka ga ya fi kowa wandaka da dukiya a cikin kasar, koda kuwa kafin ya hau karaga, mahaifinsa ba kowan kowa ba ne.”
Da yake kwatanta shugabannin da da na yanzu, Alhaji Balarabe Musa ya ce ai bai dace a auna ko kwatanta ba. Ya yi tambayar da a nuna masa dukiyar da su Azikiwe ko Awolowo ko Sardauna ko Aminu Kano suka bari bayan sun sauka daga mulki, babu! Domin su ba sata suka shiga siyasa ko hawan mulki su yi ba, sun bauta wa jama’a da kasarsu ne bisa amana da yarda.
Amma shugabannin yanzu, tun tashin farko, ba su da tunanin al’umma ko kasa a ransu, abin da suka fi damuwa shi ne, su kwashe dukiyar al’umma su kai cikin bankunan cikin gida da kasashen waje su kimshe, su bar jama’a cikin kunci da talauci da damuwa.
Wannan fitar kutsu da Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya yi game da bayyana wadanda suka takaita kasar nan da yadda suka takaita ta din da kuma ko su wane ne su, shi ne abin farin cikina. Duk da cewa lokacin da ya yi wancan zance a shekarar da ta wuce ba wanda ya maida hankalin kan batun, wasu ma cewa suka yi tsufa ne kurum ke damun Balarabe Musa. To amma abin da ya faru bayan hawan Buhari da irin badakalar da ke wanzuwa ta binciken sata da barayi, da kuma abubuwan da suka fito fili yanzu, ina jin in mun kira Balarabe Musa ‘waliyi’ ba mu yi kure ba!
Ba wani abu ya fi burge ni ba sai ganin cewa bayanin na Balarabe Musa ya kara tabbatar mana da cewa mun san barayin, mun san mazauninsu, mun kuma san irin barnar da suka yi wa kasar, abin da kila muka kasa yi shi ne mu fada a ji, cewa kifi na ganin mai jar koma, har sai da gwamnatin Buhari ta fara bankado abubuwa da kyau.
A wancan lokaci na yi tambaya ne dangane da muhimmancin wannan bayani da Balarabe Musa ya yi, domin kuwa ai mun san da wannan lalatar da ke faruwa! Sai babban sakon na jawabin Balarabe Musa, ba wai kawai ga tsiraicin da ya yi wa shugabanninmu na siyasa ba ne, a’a, nuna mana hanyar da za mu gane wasu barayin ban da wadannan da muka sani da kuma yadda za mu yi maganin su.
Mu bi sahun da Balarabe Musa ya dora mu, mu ga ko za mu iya zakulo wadannan barayi da ya ayyana, duk da yake Gwamnatin Buhari ta fara tono asirin na wannan zamani da lokaci. Shin daga lokacin da su Sardauna suka wuce mun kara samun shugabanni ko sai barayi?
Ina gidaje da kamfanonin Janar Gowon bayan ya sauka daga mulki? Ina fankama-fankaman fadoji da motocin alfarma da marigayi Janar Murtala Ramat ya bar wa magada?
Ina unguwannin da Alhaji Shehu Shagari ya saye a Legas ko Abuja ko manya-manyan kamfanonin da yake takama da su a halin yanzu, bayan ya bar shugabancin Najeriya?
Ina dankama-dankaman filaye da asusun banki makare da kudaden kasashen waje da Janar Buhari ya boye lokacin yana mulki da yanzu yake facaka a rayuwarsa?
Na san mun san amsar wadannan tambayoyi da kanmu! kila amsar da ba za mu iya bayarwa ba ita ce, sauran shugabannin fa, su ma waliyai ne kamar na baya?
Mu tambayi kanmu, wane aiki wasu daga cikin shugabannin da suka mulke mu tun daga Kansila zuwa Kwamishina ko dan Majalisa ko Sanata ko Minista ko Shugaban kasa suka yi da suka ware kansu a saman duwatsu ko suka saye wata unguwa suna zaune cikin aljannar duniya?
Mu tambayi kanmu, me ya sa Ministan shekara daya yake karewa da zaman miloniya na har abada?
Me ya sa kullum ake ta fafutikar neman mukamai, hagu da dama, ka san ba don aiki ba ne, sai dai don a cika aljihu, a shiga kece raini! Me ya idan an nada mutum a kujerar Kwamishina ko Minista ko Mai ba da Shawara za ka ga gidan da yake zaune ya cika makil da taron al’umma, tuwo da miya ba sa katsewa a cikin gida ko barga, domin akwai abin ciyar da mutane?
Me ya sa ake cika motoci daga kauyuka ana zuwa yi wa wanda aka dora kan mukamin murna?
Murnar me? Cewa nake gudun mulki ya kamata a yi, ba tarbarsa da addu’ar ya ki haram, ya ki halal ba?
Me ya sa ranar da aka bayyana a gidan rediyo ko talabijin an cire wane daga mukami, ba ka jin komai a cikin gida sai kuka da lahaula walakuwwati, kamar an yi mutuwa?
Ba wani abu ke jawo haka ba, sai don SATA aka je yi, ita ake yi, rashin damar yin ta ne ke sa kuka da kokawa! To amma wadannan da muka lissafa su ne kadai barayin da muka sani?
 Za mu ci gaba