Ina da burin taimakon mutanen karkara

Hassana Arkila mace ce wadda ta yi gwagwarmayar rayuwa, a wajen neman ilimi da harkokin kasuwanci, kuma ta yi kafada da kafada da maza a kasuwannin kauye. Sannan ana damawa da ita a harkokin siyasa. Wakilin Aminiya ya tattauna da ita, inda ta bayyana tarihinta da kalubalen rayuwa da ta fuskanta, har ta kai inda […]

Ina da burin taimakon mutanen karkara

Hassana Arkila mace ce wadda ta yi gwagwarmayar rayuwa, a wajen neman ilimi da harkokin kasuwanci, kuma ta yi kafada da kafada da maza a kasuwannin kauye. Sannan ana damawa da ita a harkokin siyasa. Wakilin Aminiya ya tattauna da ita, inda ta bayyana tarihinta da kalubalen rayuwa da ta fuskanta, har ta kai inda take a yau.

Daga Rabilu Abubakar a Gombe

Uwargida Hassana Arkila, Mace ce wacce ta yi fadi tashin rayuwa, har ta tsaya da kafafunta ,  duk da cewa ta iya ta samu dama ta yi karatun Boko mai zurfi,  amma ba ta taba yin aikin gwamnati ba,  saboda irin rufin asirin da ta samu a sana’ar tuyar waina da karago da koko da kosai. Sana’ar da ta faro tunda kuruciyarta har ta girma tana wannan sana’ ar kuma da ita ce ta rika biya wa kanta kudin makaranta, har tayi babbar difuloma (HND), kafin tayi aure, inda daga bisani ta koma sana’ar sayar da kayan gwanjo, wadda a yanzu haka ita ce shugabar mata masu sayar da kayan gwanjo na Jihar Gombe. Duk wannan fadi tashi da ta yi da jarin Naira dubu uku ta fara, amma yanzu tana da jarin da ya fi na Naira miliyan daya.

Tarihina
Sunana Hassana Arkila, ni haifaffiyar garin Bogoro  ce da ke Jihar Bauchi ‘yar kabilar Sayawa (Basaya ce) sai dai maigidana kuma dan kabilar (Baboyi) ne daga Boi.  A nan garin Bogoro aka haifini cikin shekarar 1973, kimanin shekaru 40 da suka wuce; a nan nayi kuruciyata har na girma iyayena suka sani a makarantar Firamare ta Dashem Yelwan BOI dake Bogoro, a tsakanin shekarar 1981 zuwa 1986 da na gama sai na tafi Sakandaren ’yan mata ta gwamnati GGSS Tafawa Balewa a tsakanin shekarun 1987 zuwa 1992, da na kammala na samu takardar shaidar kammala karatun Sakandare ta SSCE, sai na tafi Makarantar Share fagen Shiga Jami’a ta BACAS Bauchi a shekarar 1993 zuwa 1994, inda na yi jarabawar IJMB, bayan na gama sai na tafi kwalejin kimiya da fasaha ta Bauchi, wato Federal Polytechnic Bauchi a tsakanin shekarun 1995 zuwa 1997, inda na samu takardar shaidar karatun difuloma a fannin aikin Akawu. Sai kuma a tsakanin shekara ta 2001 zuwa 2003 na sake komawa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Gwmanatin Tarayya da ke Bauchi, inda na samu babbar difuloma  (wato HND) a wannan fanni na Akawu. Na yi hidimar kasa na shekara daya a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2004.

Aiki
Ni ban taba yin aikin gwamnati ba, cikin sana’a na tashi kuma karama gami da fatauci. Domin na fara sana’ar tuyar kosai tun ina yarinya karama, har na zama Budurwa  da jarina ya fara yawa ne shine na fara hadawa da fataucin wake da  su mangyada da kayan gwanjo ina sayowa ina sayarwa, ina samun riba, da wannan sana’a ta tuya na rika dauke wa iyayena dawainiyar kudin makaranta  saboda ina samun abin hannuna, har na kammala karatuna na yi aure, da na yi aure ne na daina sana’ar tuya saboda sha’anin aure. Wannan sana’a ta yi matukar rufa mini asiri daidai gwargwado, domin kamar  yadda na gaya maka na fara ne da kudi Naira dubu uku, amma yanzu na mallaki jarin da ya fi na Naira miliyan daya. Don a lokacin idan na tashi tuyar kosai a rana ina yin kosan mudu ashirin zuwa ashirin da biyar.

kalubalen rayuwa
A gaskiya na fuskanci kalubale sosai a rayuwa saboda tun ina karama na fara fatauci, wanda har kasuwanin kauyuka nake zuwa tun ina karamar nan har na kai cikakkiyar Budurwa. Domin a wancan lokaci wasu gani suke yi kamar  maza za su rika yaudarata ta hanyar banza, amma ni kuwa da yake nasan irin tarbiyar da na samu a gida, ko tunanin hakan ma bai zuwa mini a rai. A wani lokaci ga matsalar abun hawa na komawa gida daga kasuwar kauye kar ka manta fa a Rugar Fulani na tashi ni din nan da kake kallo, har nayi aure ban daina yawon fataucin sayen wake ba, domin a kasuwar garin Yelwan Shendam an taba sace min babban dana da kyar na same shi, amma bai sa na karaya da neman kudi ba.

Nasarar Sana’a
Alhadulilahi nagode wa Allah domin ya rufa min asiri ta wannan sana’a saboda a zamanin nan idan mace ba ta da sana’a takan iya fadawa wani hali na sharrin shaidan, watakila shaidan ya rika yi wa mace hudubar banza, har ta fada wani hali na Allah wadai, amma idan mace ta rike sana’a komai kankantar ta za ta taimaki kanta da ‘yan uwa har ma da sauran jama’a don ni da wannan sana’a da nake yi na kafa yara, wanda su ma yanzu sun zaman manyan kansu. Don haka kar mace ta raina sana’ar komai kankantarta tana da rufin asiri sosai.

Yawan iyali    
Allah na gode ma yanzu haka ina da ‘ya’ ya guda  shida, uku maza, uku mata kuma duk suna Makarantar Boko.
Shakuwata da iyalaina
Na shaku matuka da iyalai na har ma da maigidana. Domin duk ranar da na wayi gari na ga ‘ya’yana ko maigidana waninsu yana ciwo ranar ba na iya zuwa ko’ina har sai na tabbata sun samu sauki.

Burina a rayuwa.
Ina so a sani  a sahun uwa ta gari mai kishin koya wa ‘ya’yanta tarbiya ta gari, sannan kuma ina da buri in zama Shugabar karamar Hukumar Bogoro, a Jihar Bauchi, har ma in wuce nan don in samu hanyar taima wa al’ummar kauyuka .

Siyasa
Ni ina da sha’awar Siyasa tun ina karama. Lokacin da na fara fatauci mutane suke yi mini kirari irin na ‘yan siyasa wai sai na yi da zarar wanda ya sanni ya ganni sai ya fara cewa sai na yi, shi yasa tun daga wancan lokaci nake jin sha’awar siyasa a raina. Domin ina da kyakkyawar aniyar taimaka wa al’ummar karkara. Wannan aniya tawa ita tasa nake da sha’awar zama shugabar karamar hukuma, musammam karamar hukumar mu ta Bogoro, domin a lokacin zaben Malam Isa Yuguda na hada kai da wata kanwarsa da shugabar mata ta jam’iyyar PDP na yi masa aiki, har ya ci zabe a shekarar 2007. Shi Malam Isa Yuguda abokin wana ne, haka shi ma Barista Dogara ina daga cikin matan da suka yi masa aiki ya ci zabensa na dan majalisar tarayya daga Bogoro.
kungiyoyi da kasashen da ta ziyarta
Ina cikin kungiyoyi masu yawa, kadan daga cikinsu, ni ce Shugabar mata ta kungiyar Nigerian Arise reshen Jihar Bauchi, kuma jagorar kungiyar Mata ta samar da zaman lafiya mai suna Bogoro women for peace Association, ni ce kuma shugabar mata ‘yan kasuwa masu sayar da gwanjo ta Gombe. Sannan ni Mamba ce a Cocin mu na COCIN. Ban taba zuwa wata kasa ba a duniya sai dai  Cotonou, wato Jamhuriyar Benin, can ma kuma kasuwanci ya kai ni.

Shawara ga iyaye
A matsayina na ‘ya mace ina mai kira da babbar murya ga iyaye Maza da Mata da su sa  ‘ya’yansu mata a makarantun  Boko da na addini don su samu ilimin zamani da zai taimakesu, wajen zamanta kewa da kuma iya tarbiyartar da ‘ya’yansu kamar yadda ya dace.  Rashin ilimi ga ‘ya mace akwai ciwo don an ce idan aka ilmantar da Mace kamar an ilimantar da al’umma ne, amma idan da namiji ne mutum daya aka ilmantar. Sannan kuma su ‘ya’ya mata sun fi maza tausayin iyaye, haka kuma ba na goyon bayan dora wa ‘ya mace talla, domin a inda muke a kasuwa da zarar ka ga yarinya ’yar talla ta wuce za ka ga cewa idonunta a bude suke. Ina kuma kira ga iyaye da kada su ki sa ‘ya’yansu a makaranta, su yi auren wuri hakan bai dace ba, domin idan aka bai wa mace dama za ta hada kafada da kafada da namiji a kowanne irin mataki na aikin gwamnati a kasar nan. Kuma auren wuri yana iya haifar wa yarinya ciwon yoyon fitsari,  inda daga karshe mijin sai ka ga ya saketa ya auro wata.

Sannan ni Mamba ce a Cocin mu na COCIN. Ban taba zuwa wata kasa ba a duniya sai dai  Cotonou, wato Jamhuriyar Benin, can ma kuma kasuwanci ya kai ni.

Shawara ga iyaye
A matsayina na ‘ya mace ina mai kira da babbar murya ga iyaye Maza da Mata da su sa  ‘ya’yansu mata a makarantun  Boko da na addini don su samu ilimin zamani da zai taimakesu, wajen zamanta kewa da kuma iya tarbiyartar da ‘ya’yansu kamar yadda ya dace.  Rashin ilimi ga ‘ya mace akwai ciwo don an ce idan aka ilmantar da Mace kamar an ilimantar da al’umma ne, amma idan da namiji ne mutum daya aka ilmantar. Sannan kuma su ‘ya’ya mata sun fi maza tausayin iyaye, haka kuma ba na goyon bayan dora wa ‘ya mace talla, domin a inda muke a kasuwa da zarar ka ga yarinya ’yar talla ta wuce za ka ga cewa idonunta a bude suke.
Ina kuma kira ga iyaye da kada su ki sa ‘ya’yansu a makaranta, su yi auren wuri hakan bai dace ba, domin idan aka bai wa mace dama za ta hada kafada da kafada da namiji a kowanne irin mataki na aikin gwamnati a kasar nan. Kuma auren wuri yana iya haifar wa yarinya ciwon yoyon fitsari,  inda daga karshe mijin sai ka ga ya saketa ya auro wata.