Ina da karfin gwiwar sake lashe zaben Filato – Gwamna Lalong

Gwamnan Jihar Filato kuma dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC, Simon Lalong ya bayyana cewa yana da karfin gwiwar cewa zai sake lashe zabe a karo na biyu. Gwamna Lalong ya kuma bukaci al’ummar jihar su fito don kada kuri’arsu. Lalong ya yi wannan bayani bayan ya kada kuri’arsa tare da matarsa Regina da kuma […]

Ina da karfin gwiwar sake lashe zaben Filato – Gwamna Lalong

Gwamnan Jihar Filato kuma dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC, Simon Lalong ya bayyana cewa yana da karfin gwiwar cewa zai sake lashe zabe a karo na biyu.

Gwamna Lalong ya kuma bukaci al’ummar jihar su fito don kada kuri’arsu.

Lalong ya yi wannan bayani bayan ya kada kuri’arsa tare da matarsa Regina da kuma ‘yarsa Stephanie a unguwar Ajikamai da ke Karamar Hukumar Shendam a yau Asabar.
Lalong ya kuma yaba kan yadda zabe yake gudana cikin lumana a jihar.

Ya ce, “Dangane da rahotannin da nake samu na samu tabbacin cewa zabuka na tafiya cikin lumana a kananan hukumomin jihar nan, jama’a sun fito da wuri kuma suna gudanar da zabe cikin lumana.”

Gwamna Lalong ya kuma yaba wa Hukumar zabe INEC kan yadda ta kai kayayyakin zabe mazabu da wuri a jihar.
Lalong ya kuma yi alkawarin idan har aka zabe shi a karo na biyu, to zai dora daga inda ya tsaya na ayyukan ci gaba.