Ina da nasaba da Najeriya —Gimbiya Meghan
Gimbiya Meghan Markle da Yarima Harry sun ziyarci wasu kasashen Afirka a bana.
Sirikar Sarki Charles III, Meghan Markle ta ce wani bincike da ta gudanar ya tabbatar mata da cewa tana da nasaba da Najeriya ta wajen kakanni.
Uwar gidan Yarima Harry a wata hira ta musamman da ta yi da Spotify, ta ce binciken kwayoyin halitta da aka mata shekaru da suka gabata, an tabbatar mata da cewa tana da jinin Najeriya a jikinta da kusan kashi 43 cikin 100.
- NDLEA ta cafke dillalan miyagun kwayoyi 192 a Ebonyi
- Sarki Charles III ya tabbatar Rishi Sunak a matsayin Firaministan Birtaniya
Sai dai ko da aka tambaye ta daga wacce kabila take a Najeriyar, ta ce bata da masaniya a kai, amma za ta fara bincikawa nan ba da jimawa ba.
A baya-bayan nan ne dai Gimbiya Meghan ta bayyana cewa tana da jini biyu a jikinta, amma ba ta yi cikakken bayan kan asalin nata ba.
A shekarar 2015 ne Mujallar ELLE ta wallafa labarin Gimbiya Meghan game da asalinta na ruwa biyu.
A watan Satumba na 2019, Gimbiyar ta yi jawabi ga asalinta na launin fata a karon farko tun lokacin da ta auri Duke na Sussex.
A cewar RFI, ma’auratan sun ziyarci wasu kasashen Afirka a wannan shekarar.