Ina da yakinin Enyimba za ta kare kofin Firimiyar da ta ci a bara – Koci Aminu
Mataimakin kocin kulob din Enyimba da ke garin Aba a Jihar Abiya, Aminu Musa ya bayyana cewa yana da yakinin cewa kulob din zai iya sake lashe gasar Firimiya ta Najeriya a bana duk da cewa kulob din nasu ya samu kansa cikin tsomomuwa ta rashin nasara a wasanni da yake bugawa.Halin da Enyimba ta […]
Mataimakin kocin kulob din Enyimba da ke garin Aba a Jihar Abiya, Aminu Musa ya bayyana cewa yana da yakinin cewa kulob din zai iya sake lashe gasar Firimiya ta Najeriya a bana duk da cewa kulob din nasu ya samu kansa cikin tsomomuwa ta rashin nasara a wasanni da yake bugawa.
Halin da Enyimba ta samu kanta a gasar ta bana abin damuwa ne inda take matsayi na 19, bayan ta samu nasara a wasa 3, ta yi rashin nasara a 4 cikin wasa 7 da ta buga a gasar ta bana.
Kulob din wanda a halin yanzu ya zura kwallo 6 a raga, sannan aka zura masa kwallo 7 a raga ya samu kansa cikin wannan hali ne bayan an yi hasashen wasan da yake bugawa a Gasar Zakarun Afirka ne ya janyo masa rashin tabuka abin a zo a gani a gasar Firimiya, sai dai a lokacin da Koci Aminu yake tattaunawa da Aminiya ya bayyana cewa kulob dinsu zai ba marada kunya, zai kuma sake lashe gasar kofin firimiya da ya suka ci a bara.
“Halin da muka tsinki kanmu a ciki abin damuwa ne, na ji wadansu suna cewa Gasar Zakarun Afirka da muke bugawa ne ya hana mu taka muhimmiyar rawa a gasar firimiya ta Najeriya, to ina so in sanar da su ba haka ba ne, kulob dinmu yana cikin koshin lafiya, kada a manta muna da kwanten wasanni 5, don haka za mu dawo cin wasanni kamar yadda aka saba gani muna yi.
“Ina da yakinin mu ne za mu sake lashe kofin gasar ta bana, kasancewar ni na san irin shirin da muka yi yanzu, kuma kowa ya sani kyakkyawan shiri, yana haifar da kyakkyawan sakamako.” Inji shi.
Tsohon kocin kulob din Giwa FC da ke Jos ya kuma gargadi ’yan wasansa da su mayar da hankali a wasan da za su buga da kulob din Abia Warriors a ranar Lahadi.