Ina da yakinin Najeriya za ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya -Jose Mourinho 1
A ci gaba da gasar damben da ake yi a gidan wasan dambe na kasuwar Alaba Rago, an yi dambe tsakanin Shamsu da Duna inda Shamsu ya kashe Duna ba tare da wani bata lokaci ba.Damben wanda ya ja hankalin ’yan kallo saboda kwarewar da ’yan damben suka nuna ya so ya ba marar da […]
A ci gaba da gasar damben da ake yi a gidan wasan dambe na kasuwar Alaba Rago, an yi dambe tsakanin Shamsu da Duna inda Shamsu ya kashe Duna ba tare da wani bata lokaci ba.
Damben wanda ya ja hankalin ’yan kallo saboda kwarewar da ’yan damben suka nuna ya so ya ba marar da kunya. Domin da farko kamar ba za a yi kisa ba saboda jaruntar da ’yan damben suka nuna na shanye duk wani bugu da suke yi wa junansu. Amma daga bisani bayan sun yi gumi baki daya, jininsu ya dauki zafi sai salon damben ya canza inda kowanne ya rika kokarin kashe abokin hamaiyarsa. Da farko Duna ne ke kaiwa Shamsu hari na mugunta amma daga bisani sai Shamsu ya canja salo inda ya rika kaiwa Duna bugu ta ko’ina. Suna cikin kaiwa juna bugu sai Shamsu ya yi kwance-kwance ya naushi Duna a wuya, kan kace kwabo Duna ya fadi kasa warwas. Nan take ’yan kallo suka rika ihu musamman ma wadanda suke goyon bayan Shamsu, suna sowa suna murna gwaninsu ya yi kisa. Ba tare da wani bata lokaci ba alkalin wasa ya bai wa Shamsu nasara a kan Duna babu wata jayayya. Shamsu ya rika zagaya fili wurin ’yan kallo suna yi masa kyauta iri-iri suna kuma kara masa kwarin gwiwa. Shi kuwa Duna ya rika binsa a baya yana karbar nasa rabon daga wurin ’yan kallo don sawa bakin salati.
’Yan kallo da dama da Aminiya ta zanta da su sun nuna farin cikinsu kan yadda damben ya kaya. Kuma sun yaba wa kwamitin shirya gasar saboda matakan da ya dauka na bada tsaro a filin wasan. Shugaban kwamitin shirya gasar, Alhaji Aminu Kucere ya yaba wa ’yan damben saboda halin dattaku da suka nuna yayin damben. Sannan kuma ya yi alkawarin ci gaba da daukar matakan da suka dace na ganin ba a samu wata matasala ba har zuwa karshen gasar.