Ina dan shekara 14 na fara rubuta littattafai – Aliyu Dada

Bari mu fara da jin tarihinka a takaice? Cikakken sunana shi ne Aliyu Musa Dada, ni dan asalin garin Chinade ne da ke karamar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi. An haife ni ranar 3 ga Yunin, shekarar 2000 a garin Misau da ke Jihar Bauchi. Na fara karatu a shekarar 2003, a makarantar Nurul Islam […]

Ina dan shekara 14 na fara rubuta littattafai – Aliyu Dada

Bari mu fara da jin tarihinka a takaice?

Cikakken sunana shi ne Aliyu Musa Dada, ni dan asalin garin Chinade ne da ke karamar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi. An haife ni ranar 3 ga Yunin, shekarar 2000 a garin Misau da ke Jihar Bauchi. Na fara karatu a shekarar 2003, a makarantar Nurul Islam Nursery & Primary School Rigasa Kaduna, inda na samu shaidar kammala karatun firamare a shekarar 2011, daga nan sai na koma Gobernment Day Secondary School (Main) Rigasa JNR, inda na samu shaidar kammala karamar sakandare a shekarar 2014. Daga nan sai na koma Odford Science Academy Rigasa, Kaduna, inda na ci gaba da babbar sakandare zuwa aji biyu daga nan kuma sai na koma Khalifah Comprehensibe School Rigasa, Kaduna, inda na samu shaidar kammala babbar sakandare a shekarar 2017. Na rubuta jarrabawar share fagen shiga jami’a (JAMB) a shekarar 2017, inda na samu maki 185. Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) ta ba ni gurbin karatu domin karanta kwas din Geology & Mining (Ilimin Sirrin kasa da Nazarin Hako Ma’adinai) amma rashin kudin rajista ya hana ni tafiya. Yanzu haka na sake sayen JAMB kuma ina neman gurbin karatu a Jami’ar Abubakar Tafawa balewa (ATBU)  da ke Bauchi, inda nake neman gurbin karatu a fannin likitanci.

Yaya aka yi ka fara rubuce-rubuce ganin cewa kana da karancin shekaru?

Abokina ne ya fara ba ni shawara a kan in yi amfani da ilimina wurin yin rubuce-rubuce. Kamar da wasa sai na fara rubutu a kan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero, inda na rubuta takaitaccen tarihinsa da kuma kadan daga cikin ayyukansa, inda a wancan lokacin na sanya wa rubutun sunan: “About His Edcellency.” Daga baya kuma sai na kara tsawaita bincike inda na kara wasu abubuwa, wato na samar da sabon babi mai taken “Democratic Credentials.” Haka kuma na sake bayyana wasu abubuwan da suka shafi zabensa na gaba, wato “Why He Deserbe Re-Election” sannan kuma na canja sunan littafin, inda na mai da shi “The Amiable.” Yanzu haka dai na wallafa littattafai guda uku a kasa, ga su kamar haka: “The Amiable” wanda na yi game da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero, sai kuma “The Man With Great Stride – Rochas Okorocha” wanda na rubuta game da mai girma Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, sai kuma “The Genial” wanda sadaukarwa ce ga Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi, M. A. Abubakar. Guda biyu daga cikinsu na buga bugun gwaji amma daya daga ciki ban buga ba, ganin yadda su kansu wadanda na yi nasu na rasa yadda zan yi na yi su san cewa ma na rubutu a game da su. Yanzu haka akwai wasu littattafan da nake kan rubutawa, kamar “Education In Northern Nigeria” da “Sardauna The Altruistic” amma saboda rashin samun nasara da kuma hali na sha’anin rayuwa, shi ya sa duk na dakata zuwa wani lokaci.

Yaushe ka fara rubuce-rubuce?

Na fara rubuce-rubuce a wani lokacin a cikin shekarar 2014, lokacin ina da shekara 14 da haihuwa, sannan ina ajin karshe na karamar sakandare wato (JSS3), kimanin shekara hudu ke nan baya.

Wane bangaren rubutu ka fi sha’awa?

Na fi sha’awar rubutun zube.

Me ya sa ka wallafa littafai a kan gwamnoni?

Na wallafa wadannan littafai ne domin kawai ina son yadda suke gudanar da mulki. Gaskiya yadda suke tafiyar da mulkinsu yana burge ni. Wannan ne kawai ya sa na rubuta littattafai a kansu.

Mene ne burinka a rayuwa?

Burina bai wuce a ce yau na samu nasara ba, kuma a ce na zama zakaran gwajin dafi ta fannin rubutu, sannan a ce yau ga shi a cikin littafan da na wallafa za a yi bikin kaddamar da su, domin masu azancin magana na cewa burin maje Hajji Sallah. Kuma ina so duniya ta san cewa kananan yara irina ma suna da fasahar rubutu. Kuma ina so in zama zakaran gwajin dafi a tsakanin yara masu tasowa, domin in zama abin kwatance a wajen iyaye, kuma abin koyi ga yara. Sannan ina so nan gaba in zama mai taimakon matasa masu hazaka, wadanda iyayensu ba su da karfi.

Ta fannin karatu kuma, burina in zamo likita domin taimaka wa addinina da kuma talakawa marasa galihu.

Wadanne matsaloli kake fuskanta?

Sanin kowa ne cewa ba za ka taba samun wani ci gaba ba ko kuma nasara face sai ka samu wasu matsaloli. Ni dai matsalar da nake fuskanta ita ce har yau na gaza samun wani da zai zamo mini bango domin in dafa in mike kuma tunda na fara rubuce-rubuce har yau ban taba kaiwa ga gaci ba. Wadanda na yi dominsu ba su sani ba, hasali ma ba wanda ya san ina yi domin akwai mutanen da idan na je na same su a kan maganar sai dai su yi ta ba ni kudi da bai taka kara ya karya ba har na gaji na daina zuwa wajensu.

Mene ne kiranka ga gwamnati da sauran masu ruwa-da-tsaki a harkar adabi?

Lallai harkar adabi, harka ce da gwamnati da masu ruwa da tsaki ya kamata su ba muhimmanci sosai, kuma su tallafa wajen inganta ta, domin harkar tana taimakawa sosai wajen wayar da kan al’umma, ilimantar da su, fadakar da su, da sauransu. Kuma akwai saurin isar da sako. Sannan ina kira ga gwamnati da masu ruwa-da-tsaki su fito da tsarin yadda yara irina, za su fito su baje kolin fasaharsu kuma a dama da su a cikin harkar adabi. Domin akwai ire-irena da yawa amma masu tallafa mana ne matsalar, domin sun yi karanci.