Ina farin ciki da godiya da addu’o’in Kanawa —  Abba Gida-Gida 

Addu’o’in Kanawa da ma sauran al’ummar Najeriya sun yi tasiri a wannan nasara da muka samu.

Ina farin ciki da godiya da addu’o’in Kanawa —  Abba Gida-Gida 

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce yana farin ciki maras misali da hukuncin Kotun Koli wanda ya tabbatar da nasararsa a matsayin halastaccen gwamnan Kano.

Gwamnan wanda ake yi wa lakabi da Abba Gida-Gida, ya bayyana hakan ne yayin zantarwa da manema labarai a harabar kotun jim-kaɗan bayan yanke hukuncin.

Abba Kabir ya ce ya gode wa al’ummar Jihar Kano da ma na Najeriya baki ɗaya bisa addu’o’in da suka shafe watanni suna yi masa., wanda a cewarsa addu’o’insu ne suka yi tasiri.

A wannan Juma’ar ce Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Abba, inda ta soke hukuncin Kotun ɗaukakka ƙara da ta ce Abba ba halastaccen ɗan jam’iyyar NNPP ba ne.

Tun da farko a cikin watan Satumba kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf, inda ta ce Nasiru Gawuna na APC ne ya ci zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.

Gwamna Abba Gida-Gida ya garzaya Kotun Kolin ne bayan Kotun Daukaka Kara da Kotun Sauraron Kararrakin Zabe sun ce Nasiru Yusuf Gawuna na APC ne halastaccen gwamnan jihar.

Kotun Kolin ta soke nasarar da kotun sauraren kararrakin zabe da Kotun Daukaka Kara suka bai wa Nasiru Gawuna na APC, tana mai cewa Abba Kabir Yusuf na NNPP ne halastaccen gwamnan jihar.

Kuskuren da kotunan baya suka yi — Kotun Ƙoli 

Jagoran alkalan Kotun Ƙolin, Mai Shari’a John Okoro, ya ce Kotun Daukaka Kara ta yi kuskure da ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraron Kararrakin Zabe, wadda ta ce Abba Gida-Gida bai samu kuri’u mafi rinjaye a zaben watan Maris na 2023 ba.

Bayan bitar muhawarar da lauyoyin ɓangarorin biyu suka yi, Mai shari’a Okoro ya ce: “Na gano cewa hukuncin Kotun Sauraron Kararrakin Zabe na zaftare ƙuri’a 165,616 daga sakamakon Abba Yusuf, ya dogara ne a kan tanade-tanaden kundin Dokar Zaɓe ta 2022”.

Sai dai, alƙalin ya ce sashen kundin bai fayyace tsarin yadda harkoki za su gudana a rumfunan zaɓe ba. Ya kuma yi tambayar, “Ko mene ne tasirin kuri’ar da ba ta da tambarin hukumar zaɓe?”

“Ƙuri’ar da ba ta da tambarin INEC, ba za ta zama lalatacciya ba.”

Mai shari’a John Okoro ya ce sai lallai an tabbatar da hujjar cewa ƙuri’ar, ba ita ce Hukumar Zabe ta aika don gudanar da zaɓen ba.

“Babu wata hujja da ke nuna cewa ƙuri’un da ake magana a kansu, ba su ne aka yi amfani da su a zaɓen ba. Don haka hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke tabbatar da hukuncin Kotun Sauraron Kararrakin Zabe, kamata ya yi a jingine shi,” in ji mai shari’a Okoro.

“A ƙarshe, ƙaramar kotu ta yi kuskuren fashin baƙi kan batun ƙimanta ƙuri’un nata. Wannan daidai yake da karkatar da adalci.

“Don haka abin da ya dace, shi ne a mayar wa Gwamna Yusuf dukkan ƙuri’unsa,” cewar mai shari’a Okoro.