Ina fata Buhari zai amince da sakamakon zabe idan ya fadi a 2019- Sule Lamido
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce yana fata Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai amince da sakamakon zaben 2019, idan ‘yan Najeriya suka kayar da APC kamar yadda Goodluck Jonathan ya yi a zaben 2015. Sule Lamido ya yi wannan bayyanin ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron tattaunawa […]

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce yana fata Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai amince da sakamakon zaben 2019, idan ‘yan Najeriya suka kayar da APC kamar yadda Goodluck Jonathan ya yi a zaben 2015.
Sule Lamido ya yi wannan bayyanin ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron tattaunawa mai taken: Kalubalen zabe da Najeriya a kan zaben 2019, wanda kamfanin Jaridar Daily Trust ne ta shirya a Abuja domin tattaunawa kan zaben 2019.