Ina fatan Ronaldo ya ci gaba da zama a United —Casemiro

Na zaku na buga wasa tare da shi.

Ina fatan Ronaldo ya ci gaba da zama a United —Casemiro

Casemiro

Sabon dan wasan Manchester United Casemiro, yana fatan ganin Cristiano Ronaldo ya ci gaba da taka leda a kungiyar.

Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito Casemiro yana fadin haka ga manema labarai yayin da yake ban-kwana da kungiyar Real Madrid.

Ronaldo da Casemiro na daya daga cikin ’yan wasan da tasu ta zo daya a tsawon shekarun da suka shafe tare suna taka leda a kungiyar Real Madrid mai buga gasar La Liga.

“Na zaku na buga wasa tare da shi[Ronaldo], ban san mai zai faru ba, amma ina matukar burin na ga ya zauna.”

Ana ta dai cece-kucen cewa Ronaldo zai bar Old Trafford gabanin rufe kasuwar musayar ‘yan wasa ta yanzu.

Wannan kuma na faruwa ne kakar wasa daya tak bayan da ya yi kome zuwa United daga Juventus a bara.

Magoya bayan United da dama na ganin zuwan Casemiro na da matukar muhimmanci duba da yadda tagomashin kungiyar yake ci gaba da dusashewa, inda ta sha kaye a wasanninta biyu na farko a gasar Firimiyar Ingila ta bana.

Tasirin Casemiro ga United

Bayan kammala cinikin Casemiro daga Real Madrid kan yuro miliyan 70, masana harkokin wasanni sun fara diga ayar tambaya kan ko Manchester United za ta iya farfadowa daga koma bayan da ta ke fama da shi ko kuwa shi ma dan wasan na Brazil zai narke cikin jerin zakakuran ‘yan wasan da United ta jibge ba tare da nuna bajinta a filin wasa ba.

Cikin shekaru 9 tun bayan Sir Alex Ferguson ya bar Manchester United, kungiyar ta sauya manajoji na din-din-din har guda 6 yayinda ta yi cinikin manyan ‘yan wasa masu matukar tsada sai dai ba tare da ta kai labari ba.

Zuwa yanzu Casemiro mai shekaru 30 ya sa masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni ke ci gaba da tofa albarkacin baki kan cinikin da kuma yiwuwar haskawar dan wasan a kungiyar mai fama da mashasshara.

Wasu na kallon cinikin na Casemiro a matsayin babban kuskure ga United musamman la’akari da yadda ta zuba tsabar kudi wajen kawo Cristiano Ronaldo amma ba tare da ta iya samun gurbi a gasar cin kofin zakarun Turai ta bana ba.

Casemiro wanda zai rika karbar fam dubu 350 kowanne mako shi ne dan wasa na 3 mafi albashi a Manchester United bayan Cristiano Ronaldo da David de Gea.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna