…Ina fede saniya fiye da yadda masu ido ke yi – Nazuntu Makaho
Malam Muhammad Zubairu Zuntu, wanda aka fi sani da suna Nazuntu Makaho, mahauci ne mai sana’ar sayar da nama a garin Jos babban birnin jihar Filato. A wannan tattaunawar da ya yi da wakilinmu ya bayyana yadda yake fede saniya ko rago ya cire fita ba tare da ya huda ba,kuma ya fitar da kowane […]

Malam Muhammad Zubairu Zuntu, wanda aka fi sani da suna Nazuntu Makaho, mahauci ne mai sana’ar sayar da nama a garin Jos babban birnin jihar Filato. A wannan tattaunawar da ya yi da wakilinmu ya bayyana yadda yake fede saniya ko rago ya cire fita ba tare da ya huda ba,kuma ya fitar da kowane bangare na naman dabba fiye da yadda masu idanu suke yi. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya. Mene ne tarihin rayuwarka?
Nazuntu. To, ni dai asalina daga garin Zuntu da ke jihar Kaduna nake, mahaifina shi ne Sarkin fawan garin. A yanzu ina da shekaru kamar 55. Ina da mata daya da yara 9. Kuma ita wannan larura ta makanta ta same ni ne kamar shekaru 25 da suka gabata. Na yi kokarin samun magani amma abin ya gagara. Domin a lokacin na yi ta zuwa asibiti, amma matsalar rashin kudi ta sa abin ya gagare ni, saboda ba ni da kudin kuma ba ni da mataimaka. Kuma ni ba mai son na je na tambayi jama’a ne domin su taimaka mini ba.
Aminiya. A wannan lokaci ne ka fara wannan sana’a ta fawa?
Nazuntu. To, kamar yadda na fada tun da farko, wannan sana’a ta fawa sana’ar mahaifina ke nan. Don haka a lokacin da na taso sai mahaifina ya koya mini wannan sana’a. Bayan da na iya sai na rungumi sana’ar. Don duk da ina makaho ko saniya ka nuna mini ka ce na gyara ta, zan iya gyara ta in fede ta, idan ka nuna mini rago ka ce na gyara shi zan iya gyara shi, ta yadda ko mai ido ma ba zai fi ni ba. Domin duk dabbar da na fede ba na huda fatar, kuma nakan fitar da komai a jikin duk dabbar da na gyara, ba tare da samun wata matsala ba, saboda na iya aikin.
Aminiya. Ta yaya kake gudanar da wannan sana’ar?
Nazuntu. A kullum na kan tashi na shiga kasuwa, na je mahauta na duba naman da nake so. Idan na duba na san ridadden naman sa mai kyau, na kan gane duk da ba na gani, kowane irin nama ne. Idan na duba nama naga ba mai kyau ba ne ba na saye, sai na zabi nama na ridaddiyar dabba sannan nake saye. Ko saniya ce a tsaye, idan ka je ka nuna mini ka ce in duba maka ko tana da kyau, idan na zo na taba bayanta na kan iya gane tana da kyau ko ba ta da kyau.
Aminiya. To, ga mutanen da kake sayarwa da nama fa, yaya kuke yi da su wajen sayar masu da naman?
Nazuntu. Mutanen da nake sayar wa da nama, a kullum idan na dauko naman mai saudi nakan gaya musu tsakanina da Allah yadda na saya. Idan sun ga ya yi masu sai su fada mani abin da za su ba ni. Sai na karba na sanya albarka.
Aminiya. Mene ne ya darfafa maka gwiwar ride wannan sana’a duk da cewa kai makaho ne?
Nazuntu. Abin da ya sa na ride wannan sana’a shi ne, na ga cewa ba zan iya bin mutane ina yin bara ba. Don haka na danne zuciyata na rungumi wannan sana’a, ta yadda a kullum nake fitowa da wannan ‘yar jagora tawa mu je kasuwa na sayi nama na je na sayar wa da jama’a, na samu abin da zan ciyar da iyalina, na biya wa yarana kudin makaranta. A yanzu haka ina da yara guda 6 da nake biya wa kudin makaranta.
Aminiya. A dalla ka kan yi cinikin kamar nawa a rana?
Nazuntu. A kullum idan na fito da nama idan Allah Ya kawo ciniki na kanyi kamar naira dubu 20 ko naira dubu 15 ko kuma naira dubu 10 idan babu ciniki. Ina da abokan ciniki da dama a wannan gari
na Jos, wadanda a kullum suke sayen nama a wajena. Wani ma za ka ga saboda sha’awar ganina makaho bai yi niyyar sayen naman ba, sai ya kira ni ya saya.
Aminiya. Ka kai kamar shekaru nawa da fara wannan sana’a?
Nazuntu. Na kai kamar shekaru 40 ina wannan sana’a. Domin tun ina darami na fara wannan sana’a, tun kafin wannan larura ta same ni.
Aminiya. Yaya aka yi ka zo wannan gari na Jos?
Nazuntu.Yadda aka yi na zo wannan gari na Jos shi ne, akwai wata yayata da take aure a wannan gari, da mahaifina ya rasu sai ta dauko ta kawo ni wannan garin.
Aminiya. A darshe mene ne sakonka ga nadasassu?
Nazuntu. To, ina kira ga nadasassu su rida yin dodari suna koyan sana’o’,i maimakon su tsaya suna barace-barace.