Ina fuskantar kalubale a harkar rubuce-rubuce – Kamal Iyantama
Sunansa Kamal. Allah Ya hore masa baiwar rubuce-rubucen kirkirarrun labarai, ga shi gwani wajen iya zane da zayyana, kamar kuma yadda ya kasance mawakin Hausa na zamani. Ta yaya aka yi ya samu mallakar wannan fikira da fasaha? Mene ne burinsa a rayuwa? Wadannan da ma wasu tambayoyin, su ne kunshiyar tattaunawar da ya yi […]
Sunansa Kamal. Allah Ya hore masa baiwar rubuce-rubucen kirkirarrun labarai, ga shi gwani wajen iya zane da zayyana, kamar kuma yadda ya kasance mawakin Hausa na zamani. Ta yaya aka yi ya samu mallakar wannan fikira da fasaha? Mene ne burinsa a rayuwa? Wadannan da ma wasu tambayoyin, su ne kunshiyar tattaunawar da ya yi da Aminiya, kamar haka:
Ko za ka bayyana mana tarihinka a takaice?
Ni dai asalin sunana shi ne Kamal Yunous bin Abdallah, amma an fi sanina da Kamal Y. Iyantama. An haife ni a karamar Huhumar kank’ara Jihar Katsina, shekaru 28 da suka gabata. Iyayena sun taso daga Kano, inda babana ke aikin gwamnati, aka dawo da shi Malumfashi. A nan girma har na yi karatuna, ko kuma in ce nike yi har yanzu.
Maganar iyali kuwa, a halin yanzu dai ba ni da mata balle batun ’ya’ya, sai dai niyya da fatan Allah Ya kawo tagari. Na samu lakabin ‘Iyantama’ ne daga asalin mai sunan, fitaccen dan fim wato Alhaji Hamisu Lamido Iyantama, saboda tarayyarmu da shi da dadewa kuma har yau, kai har gobe muna tare in sha Allah muna zaman mutunci, karamci, ina karuwa da shi tamkar da nike a wurinsa.
Yaushe ne ka fara rubuce-rubuce, musamman rubutun waka, aikin zane-zane da kuma rubutun zube kuma me ya ja hankalinki har ka ga cewa ya kamata ka fara rubutu da sauran aikin fasaha?
To, takamaimai ban iya cewa dai ga lokacin da na fara rubuce-rubuce amma ina tunanin dai tabbas a shakarar 2009 ne, kasancewar ni mai sha’awar rubutu ne daman can. Aikin zane-zanena kuma tun ina makarantar firamare nike yin su har zuwa yau din nan da nike magana da kai. Sannan ita ma rubuta waka a shekarar 2010 ne na fara har zuwa yau ina kan yi ban daina ba.
Abin da ya ja hankalina zuwa ga yin rubuce-rubucena, tun ina karami mahaifiyata ko mahaifina sukan rika karanta mana littattafan Hausa, a ina jin dadi. Bayan na girma ne sai na fahimci ashe ana isar da muhimmin sako ta hanyar rubutu. Abin da ya sa ke nan na dukufa cikin harkar rubutun ke nan.
Ya zuwa yanzu, littattafai nawa ka rubuta, waka nawa ka rubuta kuma guda nawa ne aka buga suka shiga kasuwa?
Ya zuwa yanzu dai na rubuta littattafai akalla guda uku, sai dai babu wanda na buga domin fitarwa kuma ba ni da burin bugawar a gaskiyar. Sai dai bayan raina watakila ’yan baya su dauka su buga da kansu amma kam rubutu kamar yanzu na fara yi ma.
Haka wakoki, na rubuta sai dai idan na ce maka ga adadinsu wallahi na yi karya. Wakokina sun kunshi na aure, siyasa, soyayya, fim, fadakarwa da sauransu dai kuma dukkansu nan da na zayyano sun fita kasuwa, jama’a suna kuma sauraron su.
Shin ka koyi aikin zane a makaranta ne ko kuwa da kanka ka koya?
To hakikanin gaskiya dai ba a makaranta na koyi zane ba. Abin da zan iya sani shi ne, ni dai na tashi kawai na gan ni ina yin zane-zanena. Wannan lamari dai kawai baiwa ce daga Allah Madaukakin Sarki. Shi Ya yi mini ita kuma a kullum bana gajiya da gode masa.
A wane irin yanayi ka fi jin dadin yin rubutu ko tsara waka ko yin zane?
Na fi jin dadin rubutu ko rubuta waka mafi yawa a cikin dare, lokacin babu hayaniyar da za ta dame ni ko kuma idan ina a zaune ni kadai a wurin da babu kowa.
Ko ka taba samun kyauta ko karramawa ta dalilin rubuce-rubucenka?
Eh! Na kuwa taba samu. Don ba ni mantawa, a karshen shekarar 2010, lokacin da Kamfanin Iyantama Multimedia Nig. Ltd. ya shirya wani taro kan zaman lafiya, ci gaban matasa, ina daya daga cikin wadanda aka karrama da kyauta. Na yi farin ciki tun da ban taba tunanin haka ba a rayuwata.
Ko ka gamsu da yadda harkar rubuce-rubuce take a duniyar Hausawa?
To zan iya cewa na gamsu ko don nuna kishin yaren namu na Hausa, sannan kuma gaskiya Hausawa sun dace da sanya rigar rubutu da kuma tafiyar da shi a salo iri-iri don bunkasa ko inganta rubutu tun fil’azal. Sai dai kawai fatan kura-kuren da ake samu a ciki su gushe sannu a hankali, don rubutun ya kara samun tagomashi a cikin Hausawa maza da matan a kere sa’a; ganin yadda yanzu rubutu ke bunkasa da hauhawa a duniya kamar wutar daji.
Ko kana cikin wata kungiyar marubuta? Wace irin gudunmowa irin wadannan kungiyoyi suke bayarwa ga harkar rubuce-rubuce?
Wannan haka yake, ba shakka kuwa a cikin kungiyoyi na marubuta, ni mamba ne a Alkalam Authors Kaduna. Sannan ina a cikin kungiyar nan ta ANA Reshen Jihar Kano. Sai Duniyar Marubuta Reshen Jihar Katsina. Gaskiya a dukkan kungiyoyin nan da na bayyana, baki ba zai iya bayyana irin dimbin gudunmowar da suke bayarwa a tsakanin al’umma ba, don kuwa rubutu na samun babban ci gaba da kaso mai tsoka daga bangarensu. Jama’a da dama shaida ne kan haka.
Wadanne kabubale ka taba fuskanta ko kake kan fuskanta da suke kawo maka cikas a harkar rubuce-rubucenka ko tsara waka ko yin zane?
Hakika dukkan dan Adam in dai yana numfashi a doron duniya, to ba zai rasa gamuwa da kalubale ba, musamman ma irinmu masu harkar rubuce-rubuce da sauransu. Kuma wannan tunda lamari ne na Allah haka Ya rubuto su gare ni don jarabawa ce babba. Ina samun tsangwana daga mutane masu yi mini wani kallo ko zato. Misali, akwai wani littafi da nike kan rubutawa mai suna Illuminati: Haduwata Da Mawakiya Rihanna, sai ya zamana na dan saka dandanonsa a Duniyar Marubuta a Facebook. To da yawan mutane sun zage ni, cewa na zama abin tsoro, wasu na mini kallon ma ni dan kungiyar bautar shaidan ne, tun da ba su fahimci mene ne rubutu ba. Sannan alhamdu lillahi, Allah Ya ba ni baiwar zane salo iri-iri tare da kirkira. Hakan ba ya yi wa wasu dadi, inda nike ganin suna nuna hassadarsu a fili, kai har da barazana ma. Ka ga wannan babban kalubale ne a gare ni. Sannan akwai wata wakata da zan yi bidiyonta mai suna Aljanu Da Mutane, inda zan kwaikwayi Micheal Jackson a wakarsa da matattu ke tashi daga kaburbura da daddare. Sai dai ni an sha bamban da nasa salon, ni ba matattun ke tashi ba, aljanu ne ke tashi a wata irin siffa. To ka ga shi ma wannan ya gamu da kalubale iri-iri.
A matsayinka na marubuci, mene burinka a nan gaba?
Lallai burina a matsayina na marubuci shi ne, dukkan ayyukana na rubutu, su wanzu tare da amfani ga al’umma amma masu zuwa nan gaba, bayan na kau ke nan.
Ko kana da wani kira ko shawara ga ’yan uwanka marubuta da gwamnati da kuma al’umma dangane da harkar rubutu da wallafa?
Ba shakka kirana da zan yi ga gwamnati kai har ma da masu hannu da shuni, kan su dubi girman Allah su dubi darajar Manzo (saw) da su rika yin agaji da tallafa wa irinmu masu baiwa ko fasaha da jari, domin dogaro da kanmu ta yadda har za mu iya daukar masu tasowa irinmu don koya masu sana’ar hannu, su ma su dogara da kansu. Ka ga za a rage talauci da zaman banza da ya addabe mu a k’asa. Wannan shi ne kirana. Ga ni kaina nan, rashin jarin shi ne matsalata da ke ci min tuwo a kwarya. Sannan su ma ko kuma mu ma masu rubutu ko kuma marubuta, mu daina yin rubutu don neman suna da son a sani, mu taimaka mu rika yin rubutu don al’umma wajen wayar da kansu ta hanyoyi kala-kala. Sai ka ga an samu ci gaban rayuwa ganin yadda a yanzu muna cikin wani zamanin da sai dai addu’a.