‘Ina gani aka yi wa Limamin Gwoza yankan rago’

Babban Limamin garin Gwoza, Liman Bamanga da Hakimin Wakale da ’ya’yansa bakwai na cikin mutum 200 da ’yan Boko Haram suka kashe a harin da suka kai Gwoza a Jihar Borno, a ranar Talatar makon jiya inda garin ya koma karkashin ikonsu.Maharan sun yi wa Liman Bamanga yankan rago ne a kofar gidansa bayan fito […]

‘Ina gani aka yi wa Limamin Gwoza yankan rago’
‘Ina gani aka yi wa Limamin Gwoza yankan rago’

Babban Limamin garin Gwoza, Liman Bamanga da Hakimin Wakale da ’ya’yansa bakwai na cikin mutum 200 da ’yan Boko Haram suka kashe a harin da suka kai Gwoza a Jihar Borno, a ranar Talatar makon jiya inda garin ya koma karkashin ikonsu.
Maharan sun yi wa Liman Bamanga yankan rago ne a kofar gidansa bayan fito da shi daga cikin gidan, kuma sun kone ofishin ’yan sanda da Sakatariyar karamar Hukumar Gwoza da wani bangare na gidan Sarkin Gwoza.
Wani magidancin da aka yi abin a kan idonsa mai suna Malam Umaru Musa, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Maharan sun kashe Liman Bamanga ne bayan sun kone muhimman wurare, saboda liman bai iya gudu zuwa kan dutse ba, sai suka shiga gidansa suka dauko shi suka yanka shi a kofar gidansa, lokacin iyalansa sun gudu. Ni kuma ina kan itaciya na boye bayan da suka bar wurin, na gudu na hau kan dutse, inda muka zauna babu abinci ba ruwa har kwana uku. Liman Bamanga yana da mata uku da ’ya’ya sama da 20, kuma gidansa na gefen gidan Sarki ne kusa da masallaci kuma akwai manyan mutane da tsofaffin da aka kashe, amma Sarkin Gwoza ba mu san inda yake ba, domin an ce ba a kashe shi ba wai ya gudu ne”.
Malama Hauwa Isma’il, wadda take da ’ya’ya hudu, daya daga cikin wadanda suka kubuta daga harin, ta shaida wa wakilinmu cewa, “Wallahi mutanenmu da ’yan uwanmu duk an yanka su yankan rago, kamar maharan sun fita cikin hayyacinsu ne domin kuwa sun shagala da yanka mutane, sukan shiga gidajen mutane su fito da su su yi musu yankan rago, to a haka ne suka shiga gidan Liman suka fito da shi suka yanka shi”.
Shi ma Adamu Usman, wani ma’aikaci a garin Maiduguri cewa ya yi, “Ina da mata biyu da ’ya’ya 15, amma a yanzu ban san inda suke ba, sakamakon abin da ya auku a garin Gwoza, domin ina nan Maiduguri ina aiki, har yanzu ban san halin da suke ciki ba na neme su a waya ban same su ba”.’
Maharan sun kwashe sama da kwana biyar da kwace garin tare da kafa tutarsu, kuma sama da mutum dubu uku ne suka gudu da garin zuwa kan Dutsen Mandara don tsira da rayukansu.
Bayanai sun nuna cewa jami’an tsaro sun gaza isa garin Gwozan don fatattakar maharan, wanda hakan ya harzuka mutanen Gwozan mazauna Maiduguri suka gudanar da zanga-zanga don nuna damuwa kan yadda maharan ke ta  cin karensu ba babbaka a garin Gwozan ba tare da jami’an tsaro sun isa don ceto garin ba.
Kimanin mutanen Gwoza mazauna Maiduguri da suka haura dubu biyu ne suka gudanar da zanga-zangar daga filin Polo zuwa gidan gwamnati, dauke da rubutu a kan kwalaye masu cewa: “Ba ma son irin wannan aikin ta’addanci,” da “Ina gwamnati take ne ake aikata wannan mummunan ta’addanci?” da “Za mu yi kaura zuwa kasar Kamaru idan gwamnati ba ta magance wannan matsala ba.”
Gwamnan Jihar Kashim Shettima ya fada musu cewa duk da sha’anin tsaro ba a hannunsa yake ba, zai yi magana da wadanda abin ya shafa a Abuja ta yadda za a kara yawan jami’an tsaro a garin, kuma ya jajanta musu dangane da lamarin.