Ina gargaɗin Kwankwaso kan tsoma baki a rikicin masarautar Kano — Ata
Sabon ministan ya ce kalaman Kwankwaso za su iya zama raini ga kotu.
Sabon Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya gargaɗi jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, da ya guji yin magana kan rikicin masarautar Kano.
Ya yi gargaɗin cewa tsoma baki kan lamarin na iya ƙara rura wutar rabuwar kawuna a ƙasar nan.
- Kwalara ta kashe mutum 1 wasu 60 na a asibiti a Filato
- NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa Ake Ɗaukar Masu Ƙwarewar Aiki A Bar Masu Digiri?
Hadimin ministan, Adamu Aminu Fagge, yunƙuri ne na “mulkin mallaka” a yankin Arewa.
Ya ce, “Yanzu Legas ba za ta bari mu zaɓi sarki ba. Legas ta shiga tsakiyar Kano don kafa nasu sarkin.”
A martaninsa, Minista Yusuf Abdullahi Ata ya yi nuni da cewa batun masarautar Kano yana gaban kotu, don haka ya ce furucin Kwankwaso na iya zama raini ga kotu.
Ministan ya roƙi shugabanni da su mayar da hankali kan haɗa kan al’umma da tattaunawa mai amfani maimakon yin maganganun da za su iya dagula al’amura.
Ata, wanda tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano ne, ya jaddada cewa jagoranci na gari yana da muhimmanci a wannan lokaci da Najeriya ke fuskantar ƙalubale daban-daban.
Idan ba a manta ba, tsohon gwamnan Kano, ya yi wasu kalamai masu kaushi tare da gugar zana a Jami’ar Skyline da ke jihar.
Kwankwaso ya zargi wasu jiga-jigan siyasa daga Jihar Legas, hana gwamnatin NNPP a jihar yin rawar gaban hantsi.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da Kwankwaso ya aurar da ’yarsa ga ɗan fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Mangal.
Bikin dai ya samu halartar manyan baƙi ciki har da tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.
Sauran sun haɗa da Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido da sauransu.