Ina gaskiyar Jonathan cewa rashin 5 abin yi ke sa mutane shiga siyasa a Najeriya?

A kwanakin baya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ’yan siyasar wannan zamanin suna shiga harkar siyasa ne saboda rashin abin yi. Abin tambaya a nan shi ne, shin gaskiya ya fada ko kuwa akwai gyara cikin batun nasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Kalaman ba su […]

Ina gaskiyar Jonathan cewa rashin 5 abin yi ke sa mutane shiga siyasa a Najeriya?
Ina gaskiyar Jonathan cewa rashin 5 abin yi ke sa mutane shiga siyasa a Najeriya?

A kwanakin baya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ’yan siyasar wannan zamanin suna shiga harkar siyasa ne saboda rashin abin yi. Abin tambaya a nan shi ne, shin gaskiya ya fada ko kuwa akwai gyara cikin batun nasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Kalaman ba su kamata ba – Ustaz Habib

Ustaz Habib Adam: “Da farko dai, bai kamata irin wadannan kalamai su rika fitowa daga bakin mutumin da yake jagorancin miliyoyin jama’a kamar Shugaba Goodluck Jonathan ba. Amma a fahimtar da na yi, shi ne, ’yan siyasa a Najeriya sun kasu gida biyu ne. Na farko su ne masu ilmi da ayyukan yi da ’yan kasuwa da suka tsoma kansu cikin siyasa domin kishin mutanensu da kasa baki daya amma ba domin neman abun duniya ba. Kashi na biyu su ne irin wadanda suka shiga siyasa domin neman abun kansu su kadai tare da wani nufi daban domin su gallaza wa wanda suke kyama.”